Monday, January 9, 2012

BAN MUTU BA - BASHIR AHMAD

A ranar 9/1/2012 wanda aka yiwa lakabi da ranar 'YANCI, miliyoyin al'ummar Nijeriya, suka fita zanga - zangar lumana, domin neman 'yanci da nunawa gwamnati da sauran al'ummar duniya, kin amincewa da janye tallafin man fetur da gwamnatin tayi a farkon shekarar nan.

Ni ma da sauran al'ummar Kano manya da yara mun fita kwammu da kwarkwatarmu. A wannan fita da mukayi mun tafi rukuni guda daga unguwarmu, inda muka hadu da daliban Jami'ar Bayero dake Kano muka tafi tare dasu, munyi tafiyar sama da 10km a kafafuwanmu zuwa dandalin 'yanci (Liberation Square) wanda aka fi sani da Silver Jubilee.

Allah mai iko! A cikin wannan tawaga tamu jami'an tsaro suka harbi dan uwanmu, kuma Allah ya dauki ranshi jin kadan bayan kai shi asibiti. A daidai lokacin da abin ya faru banyi kasa a gwiwa ba na aikawa 'yan uwana da abokaina na shafukan sada zumunta na Facebook da Twitter, wanda cikin dan lokaci kalilan jama'a suka fara aiko min da sakonnin ta'aziyya da kuma addu'ar Allah ya kare mu.

Wannan sako dana aika Facebook da Twitter ba karamin rudani ya jefa wasu daga cikin 'yan uwa da abokaina ba, inda wani daga cikin abokina ya yiwa sakon nawa gurguwar fahimta, inda shi ma ya aikawa abokansa cewa "Bashir Ahmad ya rasu a wurin zanga - zanga" wasu daga cikin wadanda suka ga sakon dana aika, sai suka ce "ai ba shi ne ya rasu ba dan uwansa ne" wasu kuma suka ce "ai bayan an kashe dan uwan nasa shi ma an kashe shi" haka dai akai tayin muhawara akan na mutu ko ban mutu ba.

Abinda ya kara tsorata mafi yawancin abokaina sun kira wayata sun samu wayar a kashe, kuma sun kasa samun wanda zai tabbatar musu da cewa ban rasu ba. Dalilin rashin samu na a waya da ba'ayi ba, haka ya faru ne sakamakon chaji daya kare kuma ina cikin gungun masu zanga - zanga don haka ban samu damar sa chaji ba.

Bayan komawa ta gida da misalin 4:45pm ina kunna wayata sai ga kira daga wasu a cikin abokaina suna tambaya "shin Bashir Ahmad ne akan layi?" bayan tabbatar musu da cewa eh ni ne, sai suka sanar dani halin dake faruwa akan jita - jitar da ake yi akan na rasu, kuma suka bukaci dana koma shafin Facebook da Twitter na sanar da cewa ba ni ne na rasu ba.

Ba tare da bata lokaci ba, na shiga wadannan shafuka na sanarwa da 'yan uwa da abokan arziki ina nan da rai na, ban rasu ba. Nan ma dai abokan nawa suka rinka aiko min da sakonni Allah ya kiyaye kuma Allah ya kara nisan kwana.

A karshe ni mika godiyata ga duk wadanda suka nuna kulawa, damuwa da soyayyarsu a gare ni, musamman wadanda suka kira ni waya ko suka aiko min da sakonni. Nagode! Nagode!! Nagode!!!

No comments:

Post a Comment