Wednesday, January 18, 2012

BANKIN MUSULUNCI YA FARA AIKI A NIGERIA

Sakamakon Hargowar da aka
shiga satin da ya gabata, wato kowa na cikin gwagwarmayar neman 'yanci sakamakon tallafin man fetur da gwamnati ta cire, hankalin
da yawa daga cikinmu bai kai kan wannan ci
gaba da Musulunci da Musulman Nigeria su ka
samu ba.

Bankin Musulunci karkashin Ja'iz International Bank ya fara aiki a wannan kasa tamu, bayan suka da bankin ya rinka sha ta hannun mabiya addinin Kirista. Bankin dai ya fara aiki ne ran
ar 10/01/2012 Ya kuma bude
Ofisoshi biyu a shiyyar Abuja
da kuma Kano.

Kamar yadda tsarin bankin yake kowa da kowa na iya yin ajiya a cikinsa wato ba iya mabiya Addinin Islama ne kadai ke da damar ajiya a ciki. Za'a fara a jiyar farko a bankin da kudi Naira dubu Goma
N10,000:00 zuwa sama. Kuma kamar yadda kowa yadda kowa ya sani banki na tafiya ne kafada da kafada da dokokin Musulunci, saboda haka babu RUWA (Interest) a tsarin ajiyar bankin.

To daga yanzu
dukkan wani Musulmi da yake ajiya a wasu bankunan da suka sabawa dokokin Musulunci kuma yake fakewa da cewa lalura ce to dai yanzu ga karshen lalurar ya zo.

Yan Kasuwa, 'yan siyasa, sarakuna, malamai, dalibai da sauran daidaikun jama'a sai mu tanadi amsar da zamu bawa Allah akan mu'amalantar Riba a sauran
Bankuna.

Kamar yadda bankin yake kukan rashin
yawan masu mu'amala dashi, idan har kaunarmu da Addininmu
da son ci gabansa ba'a iya fatar bakinmu ya tsaya ba, ya kamata masu ajiye
kudadensu ko baso (loan) su
daga bankunan Riba, zuwan
wannan bankin sai muyi kokari mu dakatar da hakan mu koma amfani da namu, saboda hakan ne hanya daya da za
ta daukaka shi da bunkasa shi tare
da saurin yadashi zuwa
bangarorin kasar nan cikin kankanin lokaci.

Malamai da masu fada a ji, Ba sai
ka jira an tuntube ka ba, Lalle mu
hada karfi da Karfe don kara
tallata al'amuran wannan banki da zaburar da
mutane da su bada hadin kai
wajen samarwa bankin abokan
hulda.

Ba zan bari a fara shuka wannan
alkairin ba tare da hannuna ciki ba, da zarar Allah ya hore min abinda zan ajiye
zan fara sanya
ajiyata. To kai/ke fa yaushe zaka/ki fara ajiyar domin daukakuwar wannan banki saboda daukakarsa daukaka ce ta addinin Musulunci.

An rawaito daga Danbuzu Multi-Purpose Medium

Gyarawa da karin bayani
Bashir Ahmad
08032493020, 08050600160

2 comments:

  1. To yanzu kam, ba maganar lalura, duk wanda ya ci gaba da banki mai ruwa sai ya tanadi azabar Allah ranar lahira, kamar yadda Allah ya fada a Al Qur'ani.

    ReplyDelete
  2. Abuda zan fara da akkkkan bankin muslumci innawa allah godiya da yakawomu wannan dama don bijirewa.akan kudin ruwa da sauran bankuna suke bayarwa ga Al'ummar musulmin.Allah yakawo karsen sa kuma muna add'uar allah yasa karshensane

    ReplyDelete