Shahararren shafin samar da bayyanai na Wikipedia bangaren Turanci ya tafi yajin aiki na tsawon awanni 24 a yau Laraba domin nuna adawa da sabuwar dokar hana satar bayanai ta Internet da Amurka ke shirin bullo da ita. Su ma shafukan Reddit da kuma na Boing Boing sun ce za su shiga cikin yajin aikin. Shafukan internet din na adawa ne da dokar hana satar bayanai da kare fasaha wacce yanzu haka ake tattaunawa a kanta a Majalisar Dokokin kasar.
Sai dai shafin sada zumunta na Twitter ya ce ba zai shiga cikin yajin aikin ba. Takwaransa kuma shafin Facebook har yanzu bai ce komai ba a wannan al'amarin. Mutumin da ya kafa shafin na Wikipedia, Jimmy Wales, ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC cewa: “Mutanen da ke goyon bayan dokar sun rikide tsakanin masu adawa ko goyon bayan dokar. “Amma wannan bashi ne zancen ba, lamarin shi ne an fadada dokar da yawa, kuma an rubuta ta ta yadda za ta shafi duk wani abu da ka sani, ba ta da wata alaka da hana satar bayanai.
Amma masu goyon bayan dokar sun ce an shirya ta ne domin hana kudade shiga hannun kamfanonin internet na bogi. Akwai wata dokar makamanciyar wannan da ke kan hanyar zuwa majalisar dattawan kasar ta Amurka. A ranar Asabar fadar White House ta fitar da wata sanarwa inda ta nuna goyon baya ga masu adawa da dokar.
Sanarwar ta ce: “A yayin da muka amince cewa satar bayanai babbar matsala ce, ba za mu goyi bayan dokar da za ta rage ‘yancin fadin albarkacin baki ba, kara rashin tabbas ta fuskar tsaro a Internet, da yin zagon kasa a fagen Internet”.
An rawaito daga shafin: BBCHausa.com
No comments:
Post a Comment