Monday, January 30, 2012

Shin Kotu Ta Yiwa Hamza Al-Mustapha Hukuncin Adalci?


Kotu ta yankewa Major Hamza Al-Mustapha hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan shafe sama da shekaru 13 a gidan yari. Alkaliyar Kotun Mrs Dada ta bayyana cewa an yankewa Al-Mustapha hukuncin ne saboda da sa hannunsa aka kashe Hajiya Kudirat Abiola matar MKO Abiola. Al-Mustapha yaje kotun ne sanye da fararen kaya wanda bayan yake hukuncin ya fito yana murmushi gami da dagawa mutane hannu. Wannan dalili yasa wasu daga cikin magoya bayansa kuka, wasu kuma na Kabbara.

Major Al-Mustapha ya bayyanawa manema labarai cewa a matsayin na Musulmi bayyi mamakin hakan ba, kuma dukkan wani munafiki karshensa bazai yi kyau. Lauyan da yake kare Al-Mustaphan ya bayyana cewa zasu daukaka kara kuma suna sa ran samun hukuncin adalci a kotun gaba.

TAMBAYOYI: Shin wannan hukunci da kotu ta yakewa Al-Mustapha akwai adalci a ciki? Shin duk shekarun daya shafe a gidan yari basu isa hukunci ba? Shin duk mutanen da Ojukwu ya kasha mai yasa ba'a yanke masa hukuncin kisa ba? Shin ina labarin mutanen da Al-Mustaphan ya lissafo a kwanakin baya wanda da sa hannunsu aka kashe MKO Abiola? Shin wane mataki manyan Arewa suka dauka don ganin ba'a yiwa dansu hukuncin zalinci ba?

Ya ALLAH ga bawanka Hamza Al-Mustapha kar ka bari ayi masa hukunci na zalinci.

5 comments:

  1. Bama goyan baya wannan hukunci da kotu ta yankewa Al Mustapha, wannan ba komai ba ne sai sharrin PDP da azzaluman shugabanni. Ya Allah ga Al Mustapha. Auwal Ismail

    ReplyDelete
  2. Hamza Al-Mustapha Allah ya saka maka, Allah ya tonawa duk wanda yasaka acikin wanna hali asiri, Allah ya tsine musu, Allah ya nuna musu karshen su tun a duniya

    ReplyDelete
  3. hakika wannan ya nuna mana cewa anyi amfani da wata damane domin a rage manya masu kishin arewa amma allah gaka ga duk wanda yake ganin zai zalunci bawanka kuma allah ka kubutar da al mustapha ko suna so ko basa so.

    ReplyDelete
  4. lallai allah ysan abunda kuke nufi yan PDP mu amayin yan arewa game da Al mustaph,sai dai mu ce allah yakawo masa karshen wannan abu da yan PDP suke nufi akan sa.bayan haka allah ya tuna asirin dukkan wanda yasa akan ajeshi har tsawon wannan shekaru aru aru. batare da wani kwakwarn dalili ba.

    ReplyDelete
  5. Wannan ba adalci bane sai dai mu roki Allah ya kwatar mana hakkin mu daga hannun azalumai

    ReplyDelete