Sunday, January 15, 2012

Sako Zuwa Ga Dakarun Gwagwarmayar Neman 'Yanci

Ya ku 'yan Nigeria! Gwamnati tayi imanin cewa bamu da juriya kuma bamu da kokarin rike yunwa da kishirwa, kwanaki kalilan zamuyi cikin wannan hali na yajin aiki da zanga - zanga zamu gajiya ma'aikata su koma bakin aikinsu, dalibai su koma makarantunsu, 'yan kasuwa su kuma kasuwanni, ba tare da munyi nasara sun dawo da farashin man fetur yadda yake ba. Don Allah kar mu yarda mu bada kai bori ya sau, mu dage mu jajirce har sai munyi nasara. ALUTA CONTINUA!

Al'ummar kasashen Libya, Tunusia, Egypt, Syria da sauran kasashen larabawa, ba gwagwarmayar kwanaki uku kawai sukayi ba suka samu nasara, sai da suka jajirce ba dare ba rana, suka bar gidajensu, 'yayayensu har ma da matayensu. Sun rurrufe kasuwanninsu, dalibai sun hakura da zuwa makarantu, sun manta da kowane irin jin dadi ko yin wasanni, sun bar gadajensu sun koma kwana a fili a cikin tantuna, har sai da duniya taji muryoyinsu, a karshe kuma sukayi nasara. Fatan zamu dauki darasi daga wadannan al'ummomi wanda a zahiri kowa yasan sun fi mu jin dadin rayuwa, sun fi mu samun shugabanni nagari da sauran abubuwan more rayuwa.

Duk wani dan Nigeria daya haura shekaru 35 bai taba jin dadin shugabanni ba, kowane shugaba yazo yana shinfida mulkin kama kara har wa'adinsu ya kare. Lokaci yayi da ya kamata mu tashi domin 'yancinmu, mu tashi tsaye don kawo karshen wannan bakin mulkin na zalinci da ake yi mana. Zamu sha wahala kafin muyi nasara, amma da munyi nasara wahalar ta wuce 'yayanmu da jikokinmu zasu gode mana nan gaba akan jajircewar da mukayi domin kyautatuwar rayuwarsu.

Ba abin alfahari bane a gare mu muyi hijira daga kasarmu ta gado Nigeria zuwa wasu kasashe da suka ci gaba don yi kyakkyawar rayuwa acan har mutuwa tayi ahalinta. Ina kira ga dukkanin mu, karmu gajiya kuma kar muyi tunanin gajiyawa, kar mu karaya kuma kar muyi tunanin karaya, mu ci gaba da goyawa kungiyar 'yan Kwadago baya, tunaninsu a kullum talaka ya samu 'yanci ya fara jin dadin rayuwa da amfanar arzikin kasarsa kamar kowa, ba iya wasu 'yan tsiraru daga su sai 'yayansu ba.

Idan mukayi hakuri muka ci gaba da wannan yajin aiki da zanga - zangar neman 'yanci ba iya mu muke abin yake shafa ba, hatta gwamnatin Nigeria da 'yan kanzaginta abin yana shafarsu. A satin daya gabata Sanusi Lamido Sanusi shugaban bankin kasa na CBN ya bayyana irin biliyoyin kudin da gwamnati take yin asara a kullum tunda aka fara wannan yajin aiki.

Samun goyan bayan hukumar hako man fetur ta PENGASSAN ba karamar nasara bace a wannan gwagwarmaya, sanin kowane babu wani abu da muke fitarwa don samun kudin shiga a kasar nan sama da man fetur, da zarar PENGASSAN sun tafi yajin aiki to aikin gama ya gama, barawo zai rasa inda zaije ya saci kudi. Sun saba da yin baccin har da munshari akan dukiyar kasarmu. A karshe tunanin da suke yi mana na cewa yunwar 'yan kwanaki zata sa mu koma bakin aikinmu da wuraren sana'armu, to reshe zai juye da mujiya. Zasu zo suna rokon kowa ya dawo aikinsa, sun dawo da man fetur din yadda muke so N65. Mu kuma anan zamu sanar da abubuwan da ke cikin zociyoyinmu na irin bakin mulkin zalincin da suke shinfida mana, idan zasu gyara mu dawo bakin aiyukanmu, idan kuma ba zasu gyara ba to su sauka su bamu mulkinmu, muma zamu iya tafiyar da kasarmu yadda muke bukata.

Na bada damar kwafar wannan rubutu don aikawa sauran 'yan uwa jagororin gwagwarmayar neman 'yanci.

Bashir Ahmad
bashahmad29@yahoo.com
08032493020, 08050600160

No comments:

Post a Comment