Monday, January 30, 2012

An Yankewa Al-Mustapha Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

A Najeriya wata kotun daukaka
kara a jihar Legas ta yanke wa
tsohon dogarin marigayi Janar
Sani Abacha, Hamza Al-
Mustapha hukucin kisa ta
hanyar ratayewa sakamakon
kisan uwargidan marigayi MKO
Abiola.

Mai shari'a Mojisola Dada ta ce ya
kamata a rataye Manjo Hamza Al-
Mustapha, sakamakon samunsa
da hannu a shirya kisan
uwargidan shahararren dan
kasuwa kuma dan siyasa
marigayi Moshood Abiola.

Al-Mustapha, shi ne na hannun
damar tsohon shugaban mulkin
soji Janar Sani Abacha, ya shafe
shekaru 13 yana zama a gidan
yari, tun bayan da aka zarge shi
da shirya kisan.

Wannan shari'a ta ja hankalin
jama'a sosai a kasar, musamman
ganin lokacin da aka shafe ana
gudanar da ita - da ma
abubuwan da suka rinka faruwa
a lokacin shari'ar.

Anta samun shaidu masu cin
koro da juna a lokacin shari'ar,
yayin da kungiyoyi daban-
daban suka nuna damuwa kan
yadda aka dade ana gudanar da
ita.

A shekarar 1996 ne aka kashe
Kudirat Abiola sakamakon wani
harbi da wasu mutane suka yi
mata.

Marigayi Moshood Abiola ne ake
kyautata zaton ya lashe zaben
shugabancin kasar da aka
gudanar a shekara ta 1993,
wanda daga bisani gwamnatin
mulkin soji ta Janar Ibrahim
Babangida ta soke.

Kuma babu wani abu da yake
tunawa 'yan kasar wancan zabe
kamar wannan shari'ar.
Sai dai babu tabbas ko wannan
hukunci zai kawo karshen
sa'insar da shari'ar ta haifar.

Wannan hukuncin ya zo a daidai
lokacin da Najeriya ke cikin
mawuyacin hali ta fuskar tsaro
da kuma siyasa, abinda masu
lura da al'amura ke ganin ka iya
kara cakuda al'amura a kasar.

Daga shafin BBC Hausa

No comments:

Post a Comment