Wednesday, January 25, 2012

Boko Haram Na Kashe Jami'an Tsaro - Jami'an Tsaro Na Kashe Farar Hula

A daren ranar Talata al'ummar unguwar Tsamiyar Boka dake yankin Hotoro a cikin birnin Kano suka samu kansu cikin wani mawuyacin hali wanda jami'an tsaro suka rinka harbe - harbe a kokarinsu na farautar 'yan Boko Haram, wanda jami'an tsaron ke zargin unguwar a matsayin mafakar 'yan Boko Haram din.

A wannan zargi da jami'an tsaro ke yi wa mutanen unguwar yasa suka je gidan wani bawan Allah mai suna Uzairu Abdullahi suka bude masa wuta suka kashe shi tare da matarshi 'yar shekara 18 mai dauke da juna biyu. Wata majiyar ma ta bayyana cewa har da mahaifiyarsa marigayin a cikin gidan lokacin da jami'an tsaro suka budewa gidan wuta, kuma ita ma nan take Allah ya yi mata rasu.

Uzairu Abdullahi matashi ne dan kasuwa, wanda yake sai da shaddodi da atamfofi a kasuwar Kwari cikin birnin Kano, kuma al'ummar unguwar da yake zaune sunyi masa shaida akan mutumin kirki ne, kuma suka tabbatar da cewa ba dan kungiyar Boko Haram ba ne, sannan yana zaune a unguwar sama da shekara bakwai. Wasu daga cikin mazauna unguwar ta Tsamiyar Boka sun bayyana cewa jami'an tsaron sun harbe Uzairu da iyalansa ne akan zargin dan Boko Haram ne saboda kawai yana da dogon gemu kuma yana dage wandonsa.

SANAYYA TA DA UZAIRU ABDULLAHI

Na san Uzairu tun ina karamin yaro sama da shekaru goma da suka gabata, na san gidansu na san mahaifansa da sauran 'yan uwansa, a yadda na fahimci dabi'o'insa ko kadan ba suyi kama da na 'yan kungiyar Boko Haram ba. Kai ko ma dai ace shi din dan Boko Haram ne, ai kamata yayi a ce lokacin da jami'an tsaro suke zargin dan Boko Haram ne, kama shi ya kamata suyi su gudanar da bincike akansa domin tabbatar da zargin da suke yi masa, idan sun tabbatar da hakan sai su mika shi kotu don yi masa hukuncin daya dace dashi. Saboda hakan ne kadai zai kawo mana karshen wannan bala'i da muke ciki.

Ya Allah ka kawo mana dauki, ka sanya mana garkuwa a tsakaninmu da makiyanmu, Ka kawo mana zaman lafiya a jiharmu da kasarmu baki daya.

No comments:

Post a Comment