Friday, January 6, 2012

TASIRIN SHAFUKAN YANAR GIZO A SIYASAR WANNAN DUNIYA

Shafukan Yanar Gizo musamman shafukan sada zumunta da yin abokanta (Social Networks) irinsu Facebook, Twitter, Yahoo Messanger, Gtalk, Live Messanger, MySpace da sauransu, ba karamin sauyi suka kawo ba, a siyasar duniya a wannan karni 21 da muke ciki.

Wadannan shafukan sun kawo sauki ga siyasar da kuma 'yan siyasar, ta irin wadannan shafuka 'yan siyasa ke samun damar aikawa da sakonninsu zuwa ga al'umma domin neman goyan bayan su cikin kankanin lokaci, kuma sakonnin su samu isa inda aka aika su ba tare da jin kiri ko tsaye - tsaye ba.

Haka zalika bayan aika sakonnin neman goyan baya da 'yan siyasa ke yi kai tsaye ga al'umma, suna samun martanin sakonnin da suka aika, na amincewa ko akasin hakan, ta haka ne 'yan siyasa masu dabara ke yiwa abokannan hamayyarsu fin cin kauuu.

Anan zan dauki shafin sada zumunta na Facebook nayi misali dashi saboda kasancewarsa shafin da 'yan siyasar duniya suka fi amfani dashi wurin aika sakonnin nasu. Saboda shafin ne suke ganin ya fi hada mutane daban - daban na sassan duniya da dunkule su wuri daya. Kamar yadda Mark Zuckerberg wanda ya kirkiro shafin ya dauki alwashin tattara al'ummar duniya da dunkule su wuri guda, wanda kuma zamu iya cewa lalle ya dauki hanya, idan mukayi la'akari da yadda mutane daga kowane bangare na duniya ke kulla abota da sada zumunta a shafin, kamar suna tare da juna.

A wannan misali da zan kawo zan dauki wasu manya - manyan 'yan siyasar duniya na bada misalin dasu. Akwai Shugaba Barrack Obama na kasar America, yayi amfani da shafin Facebook wurin tallata kansa da irin manufofinsa ga al'ummar America da sauran al'ummar duniya baki daya, yayi hakan a lokacin yakin neman zabensa don zama shugaban na America, haka saboda ganin alfanun yin hakan, a wannan yakin neman zarcewa da yake muradin yi a wannan shekara 2012, ya dauki shafin na Facebook a matsayin rukukin farko, sahun gaba wurin yakin neman zaben nasa, ta nan yake aikawa magoya bayansa da masu adawa dashi abinda zai yi musu idan suka sake amincewa dashi ya koma kan kujerarsa.

Haka shugaba David Cameron na kasar England, yayi a lokacin nasa yakin neman zaben har yakai ga yin nasara.

Kamar yadda wannan shafi na Facebook yayi silar darewar wasu shugabanni gadajen mulki, ta wani bangare kuma shafin yayi silar tumbuke wasu shugabanni daga kan gadajen mulkinsu, kamar Shugabannin wasu daga cikin kasashen arewacin Africa (Egypt, Tunisia, Libya) wannan shafi ba karamin gudunmawa ya bada ba, wurin saukar da wadannan shugabannin kasashe, saboda kuwa ta shafin ne jagororin da suka jagoranci tumbuke shugabannin suka rinka aikawa da sakonni ga matasan kasashen, da kuma sanar da al'ummar duniya halin da suke ciki da kuma irin nasarorin da suke samu.

To muma nan Nigeria ba'a bar manya - manyan 'yan siyasarmu a baya ba, shi kansa mai gayya mai aikin wato shugaba Jonathan Goodluck yayi amfani da irin wannan dabara, haka babban abokin hamayyarsa General Muhammad Buhari. Da sauran wadanda sukayi takarar zama shugaban kasa a 2011 kamar Nuhu Ribadu da Malam Ibrahim Shekarau.

Kamar yadda bahaushe yace tun sassafe ake kama fara, tun yanzu wasu daga cikin masu muradin mulkar kasar nan a zaben 2015, ko nace magoya bayansu sun fara bayyana aniyarsu a shafin na Facebook. Kadan daga cikin sun hada da Senator Ahmad Sani Yariman Bakura (Yarima Vision 2015), Malam Ibrahim Shekarau (Tsangayar Masoya Sardaunan Kano), Atiku Abubakar (Atiku Abubakar 2015) sai Muhammad Namadi Sambo (Sambo 2015)

Haka ma wasu magoya bayan Gen. Buhari na da nasu shafin (Buhariyya & Gen. Muhammad Buhari Suppoters' Group) da sauran ire - iren wadannan shafuka a dandalin na Facebook.

A karshe ina fatan matasan Nigeria za muyi amfani da wannan dama wurin tantance aya a cikin tsakuwa, wato lokacin zabe mai zuwa mu tattara manufar kowane dan takara mu auna ta a sikelin tunani wanda yayi rinjaye muyi masa ruwan kuri'unmu, sannan Mu kasa, mu tsare, mu raka, mu jiraci sakamako, ba don komai ba sai don ceto kasarmu daga lalurar mutuwa dake kokarin kama ta.

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020, 08050600160

No comments:

Post a Comment