Thursday, January 19, 2012

Jami'an Tsaro Sun Sake Kama Dan Boko Haram Bayan Kubucewa Da Yayi Daga Hannunsu

Kai amma wannan wasan kwaikwayo yayi kyau ga jan hankali gami ban dariya har ma da ban haushi. Ba sai na ja ku da nisa ba, na takaice muku labari dai a yau ne hukumar jami'an tsaro ta kasa ta bada sanarwar sake kama Kabiru Sokoto aka bayyana cewa dan kungiyar Boko Haram ne, kuma ake zarginsa da shirya harin ranar Kirismeti a garin Madalla, dake jihar Niger.

An sake kama Kabiru Sokoto ne a lokacin da yake kokarin tsallake kasar nan a tsakanin iyakar kasar nan da kasar Chadi a jihar Borno, bayan kubucewar da yayi daga hannun jami'an tsaro a ranar Lahadin da ta gabata.

Babban abinda ya fi bada mamaki ko nace abin haushi shi ne bayan kubucewar wannan bawan Allah daga hannun jami'an tsaron shugaban kasa Jonathan Goodluck ya bawa jami'an tsaron umurnin cewa su fito da Kabir Sokoto duk inda yake a fadin kasar nan, cikin kasa da awa ashirin da hudu ko kuma ya dauki tsatstsauran mataki.

Jami'an da suka bada umarnin wannan wasan kwaikwayo sun nuna kwarewa a aikin nasu wanda saura 'yan awanni kalilan umarnin na mai girma Shugaban Kasa ya cika, sai ga sanarwar sake kama Kabiru Sokoto.

"Ba komai yasa na kira wannan labari da wasan kwaikwayo ba sai saboda wasu dalilai nawa wanda kuma nasan kuma idan kuka dubi dalilan nawa da idon basira zaku gane cewa wannan labari shiryayyen wasan kwaikwayo ne da ake son wasa da kwakwalwar jama'ar kasar nan"

Idan mukayi duba da yadda hankalin gwamnati ya tashi akan 'yan kungiyar Boko Haram ba yadda za'ayi ace an kama daya daga cikin 'yayan kungiyar amma jami'an tsaro suyi sakaki har ya kubuce daga hannunsu ba tare da anyi musayar wutar da zatayi sanadiyar asarar rayuka ba.

Baya ga haka idan har ba so ake ayi wasa da hankalinmu ba, babu yadda za'ayi ace shugaban kasa ya bawa jami'an tsaro umarnin kamo wani mai lefi a kayyadadden wani lokaci a kasar nan kuma kafin lokacin ya cika, jami'an tsaron suka cika aikinsu da kyakkyawan sakamako.

Tambaya anan itace idan har muna da irin wadannan jami'an tsaro da za'a basu umarnin kamo mai laifi cikin kasa da kwana daya kuma suka kamo shi, to mai yasa Shugaba Goodluck bai bada umarni a kamo wadanda suka kai harin ranar cikar shekaru 50 da samu 'yancin kan Nigeria ba, duk da kuwa shugaban yayi ikirarin yasa wadanda suka kai harin.

A baya bayan nan an hare hare ciki har da babban ofishin jami'an tsaro na kasa da kuma ofishin majalisar dinkin duniya dake birnin tarayya Abuja. Ga kuma hare - haren kwanan nan irin nasu Maiduguri, Yobe, Adamawa da sauransu, amma duk shugaban bai bada umarnin kamo wadanda suke kai hare - haren ba, duk kuwa da irin wadannan jami'an tsaro masu kamo masu laifi cikin kankanin lokaci da yake da su.

"Na san da wannan 'yan dalilai nawa idan ku ma kuka zurfafa tunani akan hakan za ku gano cewa kawai wasan kwaikwayo aka shiryawa 'yan Nigeria"

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com

4 comments:

  1. Kakana, ai wannan da akwai abinda ya fi wasan kwaikwayo da mun kira wannan batu da shi, saboda kuwa abin yafi karfin duk wani tunani mai karamar kwakwalwa. Fatanmu Allah ya daidaita mana kasarmu.

    ReplyDelete
    Replies
    1. Zahiri Nasir, kayi magana ta fahimta sai maganarka ta karshe ita ce kawai mafuta ga al'ummar kasar nan wato mu dage da addu'a.

      Delete
  2. 24 hours kenan ringim ya zama jack bauer

    ReplyDelete
  3. Lalle wannan yanuna cewa sun maida muta jarirai, wai Allah yakyauta.

    ReplyDelete