Wannan Dandali Matattarar Tunani na ce, wato inda nake Bayyana ra'ayina game da al'amura daban - daban dake faruwa a harkokin rayuwarmu ta yau da kullum. Musamman akan siyasar Kasarmu Nigeria, nahiyarmu Africa, wani lokacin ma da duniya baki daya. Allah yayi mana Jagora!
Tuesday, June 26, 2012
Tashin Hankali: Tashin Bama - Bamai A Unguwarmu
Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!!
Tashin hankali ba a sa maka rana, yau kam unguwarmu Goron Dutse Dala/Gwale Kano mun shiga tashin hankalin da ba mu taba samun kanmu a ciki ba, abin da muke jin labari a da a kasashen duniya da suke fama da yaki, sai gashi ana tafe ana tafe ya zo kasarmu a yankinmu na Arewa, to sai kuma ga shi a yau ya zo mana har gida, daman masu iya magana na cewa idan gemun dan uwanka ya kama ta wuta sai kayi kokarin sanyawa naka ruwa, tabbas wannan magana haka take a yammacin yau sai da aka shafe sama da awa daya rabi ana rugugin wata da tashin bama - bamai a unguwar tamu, wanda wasu 'yan bindiga suka fara daga bisani kuma sai ga jami'an tsaro da tankokin yaki suma suka fara nasu lugudan wutar, wanda hakan ya sanya hankalinmu ya yi bala'in tashi domin ji muke yi kamar a cikin dakunanmu da tunda aka fara tashin hankalin muka shiga muka kukkule, muna jiran yadda Allah zai yi damu.
Haka za gaji karar tashin bam kamar dakin da kake ciki zai ruguzo a kanka, kafin wani dan lokaci tuni titi da layukan unguwarmu sun zama kamar ba a taba halittar bil'adama ba. Sai dai wani abin haushi da na rasa yadda zan yi sai kawai da dakko radio na kunna domin ko zan ji halin da muke ci, saboda kuwa a lokacin da za a yi min tambayar cewa Bashir a wane hali kake a yanzu? Wallahi amsar da zan bada ita ce Allah a'alamu, saboda kuwa ba zan iya cewa ga halin da nake ba. Amma maimakon na ji gidajen radion dake cikin fadin kwaryar jihar Kano sun sako wani abu daya danganci halin tashin hankalin da muke ciki, sai na ji akasin haka, kowace tasha na murdo sai kawai na ji ana ta shan kida, kamar ma ba su san mai ke faruwa a jihar ba, abin ya bani haushi na kashe radion na dakko wayata na budo shafin Facebook nan na dan ji sanyi a zuciyata, domin kuwa sai naga kowa ba a abinda yake rubutawa sai batun halin da muke ciki, ga kuma 'yan uwa sai addu'a suke ta taya mu, duk da dai na kasa cewa komai a Facebook din amma na dade ina ta kallon abubuwan da jama'a ke bayyanawa game da mu, gami da saurin cewa "amin" idan naga wani ya taya mu da addu'a akan halin da muke ciki.
To dai a halin yanzu komai ya lafa, babu karar harbe - harbe kamar da zu, sai dai dan kadan da za ka dan ji nan da can, sai dai sanarwa da muka samu cewa da zarar munyi sallar Isha'i to kowa ya koma cikin gida ya kwanta, domin kuwa tuni an jibge manyan tankokin yaki da tarun jami'an tsaro a wasu sassa na unguwar tamu. Ni kuwa daman da yake wannan shi ne karon farko da na taba samun kai na a cikin irin wannan hali tun da aka fara abin na shiga gida, sallar Magriba ba a cikin gidan nayi, ba don tsoron mutuwa ba sai don tunanin wahala, saboda kuwa mutuwa dai daya ce kuma na san zan mutu koda ina so ko ba na so, da lokacin ya yi zan koma ga Mahaliccina Allah.
A karshe ba abin da zance sai godiya ga 'yan uwa da suka taya mu da addu'a, musamman wadanda suka yi ta kirana a waya suna tambayar lafiyata, Allah ya saka da alheri, ya kuma bar zumunci.
Ya Allah ka kawo mana karshen wannan tashin hankali a kasarmu. Ka bayyana dukkan masu hannu a ciki, koda kuwa suke rike da madafan ikon kasar nan. Na gode!
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment