Za mu iya daukar darasi daga kasashe irin su Brazil, Indonisiya da Malesiya. Duk da cewa, wadannan kasashe su na samar da mai, arzikin noma ne daya bunkasa su da al’ummarsu bakidaya.
Amurka ta siffanta Brazil a matsayin kasa mafi karfin arzikin noma a duniya. A bangarori da dama Brazil ta na kamanceceniya da Nijeriya. Kowacce ta na da yawan al’umma da fadin kasa. Brazil ta na da yawan mutanen da ya kai miliyan 190, yayin da Nijeriya ke da miliyan 167. Dukkanninsu su na da mai da kuma kasar noma, amma shugabanci ne ya bambanta kasashen biyu.
Llokacin mulkin kama-karya a Brazil an yi sakaci da aikin noma, amma tun lokacin da mulkin dimokuradiyya ya dawo kasar, aikin noma, wanda ya ke bai wa mafi yawa aikin yi sai ya sami bunkasa. Cikakkiyar hikima ita ce dimukradiyya ta bayar da yanayi na sauyi (ban da a Nijeriya), domin komai na dimokurad-iyya ya ta’allaka ne ga mutane. An bai wa noma muhimmanci a Brazil, dalilin da ya sa ya kenan kashi daya bisa uku na masu aikin yi a kasa shi ke ba su aiki.
Sakamakon ba wai ya tsaya ne kawai a kan cewa Brazil ta dogara da kanta ta fuskar ciyar da kai ba ne, a’a, ta na cikin kasashe ne ma mafi fitar da kayan amfanin gona. Brazil ta fi kowacce kasa fitar da rake, kuma ta na daya daga cikin mafi fitar da koko, waken soya da lemo. Kiwo ma ya na da fadi a kasar. Kayan noma su ne kashi 35 cikin 100 na abinda kasar ke fitarwa waje. Brazil ce mafi fitar da jan nama a duniya, rake, kofi, waken soya da kaji.
Arzikin noma na Brazil ya haura na kowacce kasa ne saboda aniyar shugabanninta; sun kafa manyan gidajen gona, yayin da kuma su ka karfafa kananan gonaki, bincike, bude kasuwanci a faifai da kuma amfani da dabarun noma na zamani. Gonakin Brazil su na da girman da ya fi yawancin gonakin Amurka, kuma a na kallon manomansu a mataki na duniya, ba wai cikin kasarsu kadai ba. Babu wani dalili da zai hana yin amfani da salon ’yan Brazil a Nijeriya. Dogaron da a yanzu mu ke yi da kananan manomanmu ba zai kai mu ko’ina ba. Za mu iya aikata abinda ya fi haka. Ba Ina cewa, gwamnatocin jihohi ko ta tarayya su mallaki gidajen mar da gona ba, amma dai su samar da filayen noma domin yin abinda ya ke a can din. Karfin gwiwa ne kadai zai iya samar da hakan. Ya kamata gwamnatoci su sayo iri masu kyau, kuma a samar da matsaya a kasuwannin duniya.
Ya kamata gwamnatin tarayya ta shigo ciki ta hanyar babban bankin Nijeriya, domin samar da rance da kuma noman kansa. Bambancin shi ne, Brazil ta na da filin noma hekta miliyan 76.7, yayin da a ke da fadin kasa na miliyan 170. Don haka ba abin mamaki ba ne don shanun Brazil sun kai miliyan 190, yayin da shanun Nijeriya ba su wuce miliyan 10 zuwa 15 ba. Kai kamar kowane abu ma dai, Nijeriya ba ta da kididdigar yawansu.
Brazil ta na fiye da hekta miliyan 23 da a ke girbe waken soya kadai. Masara ta na da hekta miliyan 12, rake na da miliyan 7, sannan shinkafa na da miliyan 2.5.
Malesiya ma wata abar misali ce. Ta na fiye da hekta miliyan hudu na noman kwakwa. A bara kadai ta sami Dala biliyan biyu a fitar da kwakwa waje. Saboda hazaka da zakakuranci, Indonisiya ta zo ta sha kan Malesiya wajen fitar da kwakwa. Wadannan kasashen fa su na da mai, amma kawai su na da shugabanni na nagri ne fiye da Nijeriya. Akwai lokacin da Nijeriya ce kasa mafi fitar da gyada waje a duniya da manja, roba da koko. Kuma a lokacin mu na cikin kasashen da ke kan gaba wajen fitar da auduga, karo, fata, kashu da sauran kayan amfanin gona.
Ya kamata gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi su fara tseren noman a junansu. Ya kamata gwamnatocin jihohi, musamman ma na Arewa tunda sun fi fadin kasar noma, su samar da akalla hekta 500,000 a kowanne yankin mazabar sanata (jihohi da dama za su iya samar da fiye da hakan), sannan su shigar da matasan da ke barazana ga tsaro cikin tsarin aikin yi a gidajen gona. Ya kamata a dawo tsarin wa’adin filaye da hukumar nan ta NALDA (Nigerian Agricultural Land Development Agency), wacce Janar Babangida ya kafa, amma saboda wawanci gwamnatocin da su ka gaji tasa ta rushe.
Ya kamata shugaban kasa ya fara aiki na hakika kan sha’anin noma, ya daina damun mu da batun biredin rogo haka nan.
No comments:
Post a Comment