Monday, June 4, 2012

Ta'aziya Ga Jama'a Lagos Da 'Yan Nijeriya Baki Daya


Inna illahi wa innaa ilaihi raji'un! Inna illahi wa innaa ilaihi raji'un!! Inna illahi wa innaa ilaihi raji'un!!!

A madadin daukakin makaranta da maziyarta wannan Dandali muna mika sakon ta'aziyarmu ga gwamnatin jihar Lagos karkashin jagorancin Gwamna Babatunde Fashola da sauran jama'ar Lagos dangane da bala'in daya same su a jiya na hadarin jirgin saman fasinja na kamfanin DANA da yayi sanadiyar mutuwar sama da mutane dari da hamsin 150. Sannan muna jajentawa wadanda suka samu munanan raunuka da kuma wadanda suka rasa dukiyoyinsu.

Muna kuma mika makamanciyar irin wannan ta'aziya ga gwamnatin kasar nan karkashin jagorancin shugaba Goodluck Ebele Jonathan da sauran al'ummar kasar nan baki daya, saboda kuwa wannan bala'i ya shafi dukkan daukakin jama'ar Nijeriya.

A karshe muna addu'ar ya Allah ya jikan 'yan uwa Musulman da suka riga mu gidan gaskiya sanadiyar wannan hadari su kuma wadanda ba mabiya addinin Musulunci ba za mu iya cewa RIP.

Ya Allah ya baiwa wadanda suka samu raunuka lafiya, ya maidawa wadanda suka rasa dukiyoyinsu da alkhairi. Ya Allah ya kare mana faruwar irin haka anan gaba.

5 comments:

  1. Allah ya jikan Musulmai da suka rasa rayukansu.

    ReplyDelete
  2. Salam. Wannan abu na faduwar jirgi ya girgizani, musamman danaji ya fada cikin unguwa ne a Lagos. Allah jikan wadanda suka rasu, ya kare faruwa haka a gaba.
    Bayan haka, ina yabamaka da irin wannan kokari dakake a wannan dandali, Allah kara basira, yayi mana jagora.

    ReplyDelete
  3. Amin summa amin. Allah ya kare faruwar hakan anan gaba.

    ReplyDelete
  4. Rabiu Shamma nagode, Allah ya bar zumunci, Allah kuma ya kawo mana karshe bala'o'in dake damun mu a kasar nan.

    ReplyDelete
  5. Ministan wannan ma'aikata ta jiragen sama tayi murabus idan ana son samu raguwan hadari a Nigeria.

    ReplyDelete