Sunday, July 1, 2012

Kukan Kurciya: Tattaunawa Tsakanin Malam Habu Da Malam Jatau Game Da Kudirin Kayyade Haihuwa


Malam Habu! Malam Habu!! Dakta Habu!!! Malam Ha.......

Na'am! Na'am!! Malam Jatau, ina zuwa haka da ranan nan?

Hhmm! kafin na baka amsar tambayarka, anya lafiya kuwa ka zauna kake irin wannan tunani, nayi ta kiranka kusan sau hudu kafin ka amsa?

Malam Jatau kenan, ni fa da kai duk 'yan Nijeriya, kuma zan iya cewa ba zai zama abin tambaya ba, ga duk dan Nijeriyar da ka gani ya dukufa ya bata lokaci mai tsawo yana tunani, saboda a wani lokaci da muke ciki ko kankanin yaron da bai san menene tunani ba, za ka ganshi lokaci lokaci yayi shiru baya cewa da kowa komai, da kuwa za kayi katarin tambayarsa mai yake damunsa? Amsar da za ta fito daga bakinsa zai ce ma "Halin da Nijeriya ke ciki" to ka ga kuwa ni ma idan ka ganni cikin wannan hali bai kamata ka daga hankalinka ba.

Malam Habu kenan gwanin iya sarrafa zance, to kai yanzu menene ya saka wannan dogon tunani game da Nijeriyar?

Hhmm zahiri abubuwa ne marassa adadi suke damuna da hana zuciyata sukuni game da wannan kasa tamu, yau kwana uku kenan ina yin tattaki har gidanka, domin mu zauna mu tattauna akan wannan al'amari daya ta so, amma bana yin sa'ar samun ka, kullum sai mai dakinka ta bayyana min cewa tun sassafe ka tafi gona, kuma ba cika dawowa ba sai daf da Magriba.

Eh haka ne kam, ka san manomi da zarar ruwan damuna ya sauka ba shi da wani lokaci na kashin kansa da ya fi ya je ya ziyarci gonarsa, koda kuwa ba shi da wani muhimmin aiki a gonar. Kuma wani abin mamaki duk bacin ran dake addaba ta da zarar na isa gonata, sai kaji komai ya zama tarihi. Ku ba kun tsaya ba, wai ku 'yan boko sai zuwa Office, da yaki da biro da takardu, kun manta da cewa noman dai shi ne gatanmu. Mu bar dai wannan zance, Malam Habu menene al'amarin da kake son mu tattauna akansa?

Malam Jatau ba komai ya tayar min da hankali ba, sai wata magana da shugaban Jamhuriyar nan, wato shugaba Mai Bakar Malafa ya yi game da maganar kayyade iyali, kuma ka san fa wannan ba karamin laifi ba ne addininmu, kai har ma a addinin nasu, babban laifi ne, aikata wannan kuduri na shugaban.

To ban da abinka Malam ko nace Dakta Habu menene zai daga maka hankali akan hakan, har ka shiga irin wannan tunani?

Ba komai ya daga min hankali ba, sai gaskata maganar Mai Malafar da nayi, saboda kuwa duk abinda ya furta cewar zai yi to fa sai ya yi, ko da kuwa ana muzuru ana shaho, ma'ana idan shi kadai ya yanke hukuncin zai yi abu kaza, ko duk kasar nan za su nuna rashin goyon bayansu, bai dame shi, kai ko jama'ar kasar za su shiga wani hali, an yi irin haka da shi ba sau daya ko sau biyu ba, idan za ka tuna janye tallafin albarkatun man fetur da yayi, ko karin kudin wutar lantarki daya yi, duk 'yan kasa sun nuna kin amincewarsu, majalissun kasa ma duk biyun basu amince ba, kungiyoyin da bana gwamnati ba har zanga - zanga cin amincewa suka yi tayi amma duk a banza, yayi kunnen uwar shegu sai da ya aiwatar da kudirinsa.

Maganarka tana kan hanya domin a baya bayan nan ma, sai daya canja sunan Jami'ar Legas, duk ba tare da yardar kowa ba, to amma idan haka ne ai akwai wani alkawari daya dauka amma ya kasa cika shi.

Wannan wane alkawari ne kuwa, amma dai zai amfani talakawa ko?

Sosai ma kuwa, alkawarin da yayi na kawo karshen kungiyar Boko Haram a watan June, ga shi har mun yi bankwana da watan mun shigo watan July, kai wani abin mamaki ma, kungiyar kamar karfi ta kara a cikin watan June din, maimako a murkushe ta kamar yadda shugaban ya dauki alwashi.

Hahahahaha! Malam Jatau har ka bani wata budurwar dariya, ai daman shi shugaba Mai Malafa a yadda masu bibiyar al'amuran yau da kullum da ya shafi kasar nan suka bayyana shi baya nuna bajintarsa da matsawarsa, a komai sai inda talakawan kasar nan za su shiga wani mawuyacin hali, kuma idan kayi nazari za ka gane wannan batu haka yake babu ja ko kadan.

To a karshe menene matsayinka a game da kudirin kayyade haihuwar da kace yana yunkurin yi?

To daman ai Malam Jatau neman da nake yi ma kenan har kwana uku don naji ra'ayinka da shawararka akan kudirin?

Malam Habu da ma baka wahalar da kanka wurin jigilar nema na ba, domin kuwa ni tuni na dade da daina tofa albarkacin bakina a komai daya danganci kasar nan, saboda kuwa sai mutum ya je ya sanyawa kansa hawan jini ya tafi ba tare da lokacin tafiyar tasa ya yi ba. Kai bari ma na karashe ma maganar tun ruwan farko na baiwa Malam Mati makocina rediyo na kyauta, hankalina kacokan yanzu ya koma kan gonata, fatana Allah ya ba mu damuna mai albarka. Ga ga tafiya ta, sai an jima!

Malam Jatau! Malam Jatau!! Malam Jatau!!! Malam Jatau...... (Zancen zuci) Kai lalle Malam Jatau ya watsar da al'amuran Nijeriya sai ka ce ba shi ne kullum ba shi da zancen daya fi na Nijeriyar ba. Kai anya nima kuwa ba tattarawa zanyi na hakura da bata lokaci akan tunanin gyaruwar NIJERIYAr ba? To idan kuma muka daina yunkurin gyaruwar kasarmu, wasu za su zo daga wata kasar ne su gyara mana kasar tamu sannan su koma kasarsu? Tunda nake karanta tarihin kasashen da suka ci gaba, ban taba karanta tarihin kasar da baki suka zo suka daidaita kasar bayan ta rikice ba, ko suka kawo mata ci gaba a lokacin da take sahun koma baya. Amma dai zanyi tunani akai kafin na yanke hukuncin karshe.

To 'yan uwana Maza da Mata 'yan DANDALI sai mu taru mu taya Malam Habu yin tunaninsa na karshe kafin ya yanke hukunci ci gaba ko daina tunani akan makomar kasarsa anan gaba.

Shin ya kamata ya ci gaba da tunanin gyaruwar Nijeriyar ko ya hakura ya fuskanci harkokin da ke gabansa?

No comments:

Post a Comment