Saturday, June 16, 2012

Ta Tabba Faruk Lawan Ya Karbi Cin Hanci: Wane Hukunci Ya Cancanci A Yanke Masa?


Wannan takaddama tayi daidai da abinda bahaushe ke cewa "Mai Dokar Bacci Ya Buge Da Gyangyadi" ba komai yasa na bude wannan maganar ba, sai game da takaddamar da ke kai kawo a kasar nan ta Hon. Faruk Lawan shugaban kwamitin bankado badakalar tallafin man fetur, wanda ya tsaya tsayin daka, ya kuma jajirce ba tare da jin kunya ko nuna tsoro ba, yayin tafiyar da aikin da aka dora masa a kwamitin nasa, ya gudanar da aikin nasa ba tare da nuna abokan taka ba, duk irin barazanar da shi da sauran 'yan kwamitin nasa suka sha, hakan bai hana su gudanar da ingantaccen bincike ba akan duk wani dake da hannu a cikin badakalar ta tallafin man fetur din ba. Kai na dai takaice jawabina duk wannan kwanci tashin da Faruku da sauran abokanan aikinsa suka sha a karshe sai da suka bayyana sunan duk wani da suka samu da hannun cikin badakalar, ba tare da ware 'yan lele ko abokanai ba. Wannan sakamakon bincike da kwamitin suka bayyana ba karamin burge 'yan Nijeriya suka yi ba, kuma ya karawa jama'ar kasar nan kwarin gwiwa, da jinjina a gare su domin ba wanda ya taba tunanin cewa za a samu gwarzaye marasa tsoron da za su iya jagoranta wannan jan aiki har su kai ga nasara.

Sai dai kuma bayan wasu 'yan satuttuka da bayyanar sakamakon duk kafin a kai ga hukunta wadanda aka gano da laifuka, sai ga reshe na neman juyewa da mujiya, domin kuwa sai ga sanarwar zargin jagoran kwamitin kamo masu laifi ana zarginsa da laifi makamancin irin wanda ya jagoranci bankadowa. A takaice shi ma dai a karshe an bankado ta sa badakalar da ake zarginsa da karbar cin hancin zunzurutun kudi har dalar Amurka $6000,000, da wani kamfanin hada hadar man fetur wanda ba a tantance sunansa ba ya ba shi, kuma a karshe zargin ya tabbata gaskiya sakamakon wasu shaidu da aka gabatar ciki har da faifai hoto mai motsi wato Video, wanda har hakan ya jawo sauke jagoran bankado masu badakala ya bayyana da bakinsa cewa ya karbi na goron, amma domin ya zame masa wukar gindi wurin gurfanar da wadanda suka yi masa tayin na goron a gaban hukumar yaki da cin hanci da yiwa dukiyar kasa zagon kasa wato EFCC. Daga karshe dai wannan tabargaza da jagoran ya tafka ta jawo sauke shi daga dukkan wasu mukamai da yake jagoranta a majalisar ta wakilai.

Baya ga haka, su kuma jami'an hukumar 'yan sanda suka garzayo don gudanar da aikinsu akan Faruku, wato dai tuni suka yi awon gaba da shi don ci gaba da binciken kwakwaf, har su gano gaskiyar lamarin.

To abin tambaya anan shi ne, shin idan masu binciken kwakwaf sun sake gano Faruku da laifi dumu dumu, wane irin hukunci ya cancanci a yanke masa don ya zama darasi ga masu irin halayyarsa?

Na san ni da sauran masu karatu ba za a rasa tarun amsoshin wannan tambaya a cikin kwakwalenmu ba, to amma kafin azo kan amsa tambayar ina labarin baragurbin da kwamitin da Faruku ya jagoranci bankado almundahanar da suka tafka akan tallafin man fetur? Shin su tunda an tabbatar da laifukansu an yanke musu hukuncin da yayi daidai da laifinsu? Idan ba a yanke ba har yanzu, to shin mai ake jira?

A karshe zan bawa hukumomin shari'a da abin ya shafa shawarar ya kamata suyi amfani da maganar da Janar Muhammad Buhari ya fada akan masu hannun a badakalar tallafin man fetur din, inda yake cewa "Da ni ne shugaban kasa, da zan yankewa duk masu hannun a cikin badakalar hukuncin kisa, ko hukuncin dauri a gidan yari" tabbas Janar ya fadi gaskiya kuma bana tunani akwai wani hukunci da za a yanke musu da ya fi hakan dacewa. Kuma da tun farko ana daukar irin hukuncin akan duk wani da aka samu da hannun dumu dumu akan cin hanci da karbar rashawa, da tuni sai an share gumi wurin binciko mutum daya da za a samu da irin makamancin laifi, saboda kuwa duk kasashen da suka yi kaurin suna wurin cin hancin irin hukunci ake amfani da shi ake kawo karshe mummunan aikin.

No comments:

Post a Comment