Tuesday, June 5, 2012

Tsakanin Buhari Da PDP Wa Ke So Tarwatsa Nijeriya? I



Ga duk wanda ya san Janar Muhammadu Buhari zai iya fassara shi a matsayin mutum mai tsattsauran ra’ayi akan abinda ya yarda da shi. Wanda ba ya shakkar bayyana ra’ayinsa ga kowa a kowa ne lokaci, kazalika kuma a ko ina.

Tsayayyen da ya ke fafutukar kawar da mulkin danniya da kama-karya. Kaifin dayan da ba ya fargabar shelantawa duniya manufarsa ta hukunta duk wani barawon shugaban da ya kwashi dukiyar talaka. Wanda a halin yanzu miliyoyin talakawan Nijeriya su ke son sa ba domin giwa ta fadi a sha gara ba, face sai domin kyautata masa zato da su ke yi cewa, shine kwalelen da zai tsallakar da su daga kududdufin karangiyar bakar wahala da su ka tsinci kansu sakamakon rashin nagartaccen shugabanci.

Janar Buhari ya kasance mai alfahari tare da bugun kirjin cewa, ya zama shugaban kasa, ya zama ministan man fetur, ya zama gwamnan tsohuwar Maiduguri kana kuma ya rike shugaban hukumar rarar mai ta kasa, amma kuma bai taba satar ko kwabo ba. Ya kan kuma jaddada cewa, a shirye ya ke ya amsa takardar gayyata daga kowa ne domin kare kansa akan shi ba barawo ba ne. Sau da dama a Nijeriya idan aka samu mutum mai bayyana kansa a matsayin mai gaskiya, sai tafiya ta yi tafiya sai a tsince shi ya hada kai da wadanda a baya ya ke kira a matsayin azzalumai kuma barayi domin karbar nasa kason.

Amma wani abin mamaki da ya kara daukaka kimar Janar Buhari shi ne yadda har yanzu ya ki aminta ya je ya sayar da ‘yancin talakawan da su ke son sa, domin a cika masa asusunsa. Shi ne wanda masu kashi a gindi su ke fargabar ya samu dama domin sun tabbatar ba zai raga musu ba. Janar Buhari ne talakawa ke tsananta son sa ba tare da ya na da kudin da zai kyautar a gare su ba. Sabanin sauran ‘yan siyasa da sun kwashi dukiyar kasa su ke kuma rabar wa ga talaka a yayin da su ka so a sake zabensu.

Janar Muhammadu Buhari ne ake ta kulle-kulle tare da makarkashiyar ko ta wanne hali a samo laifin da za a jingina masa domin a tozarta shi. Ko a yayin da hasalallun talakawa su ka yi tinzurin yi wa PDP korar-kare a wasu jihohin Arewa, sakamakon zargin tafka magudi da aka yi, wanda hakan ya janyo yamutsin da aka yi asarar rayuka da kuma dukiyoyi. An nemi a jingina wannan tarzoma ga Janar Muhammadu Buhari.

Kalamansa na ‘kowa ya kafa ya tsare ya kuma raka kuri’arsa’ a yayin gudanar da zabe, na daya daga cikin abinda ‘yan barandan siyasa da kuma sojojin baka su ka karbo kwangila domin lika masa a matsayin makamashin da ya assasa wutar wancan rikici. Kana kuma an zarge shi da yin amfani da karin maganar ‘jiki magayi’ a matsayin sababin rashin zaman lafiya da ya zama alakakai a wasu jihohin Arewa.

Akwai karashen wannan jawabi a kashi na II a kasa.

3 comments:

  1. Amsa a bayyane take mal. Bashir, PDP ce, sai dai Allah ya yi mana maganinta.

    ReplyDelete
  2. Mall Bashir Allah ya saka. Allah kuma ya kawo mana karshen duk wani azzalumi a kasanna

    ReplyDelete
  3. Ai masu iya magana daga cikn larabawa ma na cewa, “azzulmu la yadumu wa'in dala dammara“ ma'ana; shi zalunci baya dorewa koda an dauki lokaci mai tsawo ana yi sai ta rushe. Kuma ga shi Allah ya nuna mana haka. Mal. Ina maka fatan alkhairi.

    ReplyDelete