Friday, June 1, 2012

Gwamnatin Nijeriya Ta Kara Farashin Wutan Lantarki - Amma Ta Ce Karin Ba Zai Shafi Talakawa Ba



Gwamnatin Nijeriya karkashin jagorancin Goodluck Jonathan ta kara maimaitawa 'yan Nijeriya ranar 1 ga January (Ranar da aka janye tallafin mai) saboda kuwa a yau 1 ga June, muka tashi da karin farashin kudin wutar lantarki, kamar yadda gwamnatin ta alkawarta tun a baya. Duk da hukumar da ke kula da wutar lantarkin ta bayyana cewa karin farashin ba zai shafi talakawa ba, sai dai manyan masana'antu. Amma masa fannin tattalin arziki sun bayyana cewa karin farashin ba wanda zai fi sha fa sama da talakawa, saboda idan an yiwa kamfani karin farashin wuta, shi kuma kamfanin akan talakawa za su fanshe.

Shin anya kuwa za'a samu wutar lantarki isashiya a kasar nan? Na yi wannan tambaya ne saboda yadda a cikin satin nan na ci karo da hoton tsohuwar wata jarida a shafukan internet, wannan hoto ya tabbatar min da cewa lalle an dade ana yiwa 'yan kasar alkawarin kawo karshen nai na zama a cikin duhu. Bayanai da suka bayyana a cikin hoton tsohuwar jaridar sun nuna cewa a lokacin shugaba Shehu Shagari ne ke jagorantar kasar nan, kuma gwamnatin nasa ta dau alkawarin daga 1986 ba bu sauran sake zama cikin duhu a kasar nan baki daya.

Amma abin mamaki daga wancan lokacin zuwa yanzu kusan shekaru 30 kenan, amma har yanzu wutar bata samu yadda ake bukata ba, hasalima, kullum lantarkin sai kara tabarbarewa take yi tana ja da baya, kuma kowane shugaba ya zo maganar kenan, ga makudan kudaden talakawa da ake fitarwa lantarkin tana lakusewa.

To mu dai kullum addu'armu Allah ya kawowa kasar nan mafita ta alkhairi, Allah ya bawa kasar nan jagorori na gari.

3 comments:

  1. Hhhmm! Allah sarki talakan Nigeria, kai wai yaushe zamu ci gaba ne? Nayi matukar mamaki lokacin da aiki ya kai ni kasar South Africa, sai na ashe su tuni sun ma manta da labarin dauke wutar lantanki. Allah ya bamu shugabanni tsayayyu.

    ReplyDelete
  2. totally nice blog! Bashir zanso mu sharing ideas ( i am a journalist too) Allah ya taimaki najeriya da arewa

    ReplyDelete