Monday, June 18, 2012

Shin Gaskiya Ne Shahararriyar Jarumar Fim Din Nan Nafisat Abdullahi Ta Rasu?


Tambaya: "Shin gaskiya ne shaharriyar jarumar shirin fina-finan Hausan nan Nafisat Abdullahi ta rasu?" Wannan tambaya ko nace jita - jita, ta dade tana zagayawa a tsakanin al'ummar kasar nan musamman masu sha'awar finafinan Hausa. Hakan kuwa ya samo asali ne tun bayan hadarin da Nafisan daya rutsa da ita da abokin sana'arta Adam A. Zango.

Shahararriyar 'yar wasan kwaikwayon, ta kawo karshe wannan jita - jita da bakinta a wata tattaunawa da tayi da wakilin jaridar RARIYA, inda take cewa "Ina nan da raina a daina cewa na mutu".

Domin karanta cikakken labarin sai a nemi jaridar RARIYA ta ranar Juma'an nan wadda ke kasuwa a halin yanzu, kuma za a iya samun jaridar a dukkan wuraren saida jaridu dake sassan kasar nan.

2 comments:

  1. GASKIYA NAJIDA DIN KARANTA WANNAN MUJALLAR HAUSA INA FATAN KUNA LAFIYA

    ReplyDelete
  2. yauwa abunda nake nema kenan naji dadi sosai

    ReplyDelete