Wednesday, June 20, 2012

Addu'a: Hanyar Kawo Karshen Halin Da Muke Ciki A Kasar Nan


Aminci a gare ku ya ku 'yan uwana Musulmai maza da mata, yara da manya, kasarmu Nijeriya na cikin wani mummunan hali, halin da idan ya ci gaba da faruwa to nan gaba komai na iya faruwa.

Wani abin bakin ciki kuma abin da ya fi tayar min da hankali shi ne tun lokacin da wannan mummunan abu ya fara faruwa a shekarar 2009, 'yan uwanmu Musulmai Hausa/Fulani su abin ya fi ritsawa da su, amma kullum kuma mu ake zagi da zargar cewa mu muke haifar da komai, hakan ta sa kullum ake kara tsanarmu, ana zagi da aibanta addininmu.

To mu dai kowa ya sani ba mu da takobi, ba mu AK47 balle kuma jirgin yaki, amma dai duk da haka addininmu ya sanar da mu muna da makaman yakin da ya fi duk wadannan makamai, saboda haka lokaci yayi da zamu maida hankalinmu kan makamanmu, mu dakko shi mu fara amfani da shi, haka ne kadai zai kawo mana daidaituwar wadannan al'amura.

Wannan makami namu ba boyayye ba ne, a wurinmu hasalima, dukkan mu mun iya fafata yaki da shi, kuma mu samu nasara akan abokan gabarmu, ba tare da mun ji rauni ko kwarzane ba, sai dai kawai mantuwa da koyaushe take hana mu fafata yakin da shi.

ADDU'A ita ce makamin namu, wadda kuma ya kamata a tsakaninmu mu dauki wani adadi daga cikin wadanda Al Qur'ani mai girma ya koya mana har sai mun yi nasara, saboda haka mu kudure a cikin zuciyoyinmu daga yanzu kullum muke karanta "HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL" sau miliyan daya (1,000,000.00) da zummar Allah (SWT) ya taimake mu, ya kawo mana karshen wannan hali na rashin tsaron da muke ciki, sannan Allah ya tona asirin duk wanda suke shirya wannan al'amari, koda kuwa Musulmai ne ko kirista Allah ya wargatsa shirin su.

Idan kowanne daga cikin mu zai karanta adadin 1000 a kullum, to tabbas za mu haura yawan adadin miliyan dari ma. 'Yan uwa mu taimaka mu aikawa sauran 'yan uwanmu maza da mata wannan sako, sannan mu sanarwa yara kanana su ta karantawa. Allah ya taimake mu ya amsa addu'o'inmu.

No comments:

Post a Comment