Tuesday, September 18, 2012

Mu Kauracewa Amfani Shafin YouTube


Yan uwa ya kamata mu kauracewa amfani da shafin YouTube da rage mu'amala a shafin matambayi baya bata na Google, sakamakon kin cire video wasan kwaikwayon da aka yi isgilanci ga Fiyayyen Halitta Annabin Muhammad (SAW).

Tun bayan fitowar wannan wasan kwaikwayo a shafin na YouTube gwamnatin kasar Amurka ta umarci kamfanin Google da ya mallaki shafin na YouTube da su cire video daga shafinsu, saboda kyale shi cin zarafin mabiya addinin Musulunci ne.

Amma kamfani na Google ya kekasa kasa da cewar yin hakan ya saba dokar kare hakkin loda video na masu amfani da shafin.

Wannan dalilin ya sa wasu kasashen Musulmai suka yanke shawarar kauracewa amfani da YouTube a ranakun 20, 21 da 22 na watan Satumba da muke ciki, don nuna fushin su ga kin cire video da shafin yayi. Wanda kuma akalla Musulmai sama da miliyan 100 suna amfani da shafin a kowace rana.

To ya kamata mu ma mu shiga sahun 'yan uwanmu Musulman duniya, na kauracewa amfani da shafin a wadannan rana ku, koda kuwa akwai muhimmin aiki da za muyi a cikin sa, yin hakan ba karamin asara zai haifarwa kamfanin ba, idan kuma hakan ma suka ki yarda da bukatarmu na cire video, to sai mu dauki matakin daina amfani da shafin na dindindin, wato na har abada.

Aikawa, sauran 'yan uwa wannan sako.

1 comment:

  1. Malam Bashir wannan magana ta cewar a kauracewa wannan shafin bashi bane mafita, mafita ita muma mu cika wannan gida da karatuka da kuma tarihi na shi Manzon Allah wanda a sakamakon wancan videon da aka saka an sami sama da mutane miliyan dari taa suna kokarin sanin wane ne wannan mutumin da aka wulakanta.

    Sannan a sakamakon kirkirar wancan takin da amurka tayi da iraki da kuma karya da ta shirya na cewar musulmai sune suka kai wa tagwayen cibiyar kasuwanci hari, sama da mutane dubu dari biyu da hamsin suka musulunta a sanadiyyar bincike da suka yi akan hakan. Kuma kada ka manta shafin Youtube ba na yahudawa bane haka kuma ba na 'yan kungiyar asiri bane, sai dai idan jiya ko yau shuka tsunduma ciki. Kuma a jiya dana duba naga sama da mutane miliyan bakwai suka kalli wannan video kuma a saka wannan vidon har kashi shida zuwa bakwai a cikin wannan shafi saboda haka akwai yadda ake dukkan wani video ko audio ko hoto da aka saka shi a internet musamman shafuka na kyauta to suna da ka'ida na cewar dukkan abinda ba a sonshi ko kuma zai kawo hargitsi to ayi plagging dinsa shike nuna ba'a son shi. Kuma ma ai duk abinda suka yi inda aka samu wani musulmi yayi sharing din videon ko kuma ya umarta da a kalle shi to ai yafi kowa laifi.

    Allah nake roko da ya shiryar da mu kan tafarki madaidaici, su kuma da suka shirya wannan film din da su da wanda yaji dadi da wanda yayi shiru da wanda ya kalla kuma bai tsine musu ba Allah ya tsine musu gaba daya Allah ya hallarta jininsu ta kowane hanya amin.

    Daga salisu hassan (websmaster)

    ReplyDelete