Monday, September 3, 2012

Babbar Magana: Tsakanin Shugaba Goodluck Da Fastor Tunde Bakare


Bari mu waiwayi tarihi na baya-bayan nan. La’alla a matsayinsa na fasto, dan siyasa, mai wa’azi, mutumin Allah, lauya ko mai kwato hakkin ’yan kasa – wanda dukkansu shi ne – Fasto Tunde Bakare a koyaushe ya kasance mai akida kuma maras wargi...

A matsayinsa na lauya ya yi aiki a karkashin Gani Fawehinmi. A 1999, a lokacin da kusan kowa ke zumudin takarar Olusegun Obasanjo, Bakare ya fito gaba-gadi ya ayyana cewa ba a dauko mai ceton al’umma ba. Ya yi ikirarin cewa, a hakikani ma dai Obasanjo zai sake yamutsa matsalolin Nijeriya ne. Tuni a ka tabbatar da gaskiyar batunsa a aikace. Ba ma haka kadai ba, Obasanjo ya zama annoba ta yadda ya dasa harsashin gurbataccen shugabancin da duk ya biyo bayansa.

A lokacin da Shugaba Umaru Musa Yar’Adua ya gaza saboda jinya, kwakwalwarsa ta daskare kuma ’yan ma’abban gwamnatinsa su ke amfani da rashin lafiyar wajen hana mataimakin shugaban kasa na lokacin, Goodluck Jonathan, ya gaje shi, Fasto Bakare ya jagoranci kungiyar Save Nigeria Group (SNG) wacce ta tilastawa ’yan siyasar aikata abinda ya dace. A yanzu Shugaba Jonathan ya shaku da sabbin abokansa har ya mance da kokarin Fasto Bakare a mawuyacin lokaci. Dukkanmu, har shi Tunde Bakare, mun dage a kan sai an aiwatar da sashe na 144 na kundin tsarin mulkin kasa ne, wanda zai bai wa mataimakin shugaban kasa Jonathan darewa karagar mulki kai tsaye ba wai a matsayin mai rikon kwarya ba, saboda hakan ne daidai. Ni na ga wautar majalisar dattawa ma da su ka yi amfani da wani abu wai shi ‘matakin tilashi’ su ka ayyana mataimakin shugaban a matsayin shugaba na rikon kwarya alhali sashe na 144 a fayyace ya ke kan abinda ya dace kasar ta aikata a irin wancan hali.

Fasto Bakare ya kausasa harshe ga masu rike da madafun iko kamar yadda littafin Bible ya wa’azantar. Ba wai kawai rashin tsoro ne da faston ba, ya na ma da kwakwalwar yin kyakkyawan hasashe.

’Yan kwanaki kadan da su ka gabata, jami’an tsaro na farin kaya, SSS, su ka gayyaci faston bisa lafazansa. Akwai shakkun cewa idan SSS za su iya gayyatar Bakare ba tare da izinin shugaban kasar ba. Wannan cin zarafi ne ga ’yancin fadar albarkacin baki kuma hakan bai dace da dimukradiyya ba a ko’ina cikin duniya. Irin wadannan ne abubuwan da su ke faruwa a Nijeriya lokaci zuwa lokaci wadanda ke nuni da cewa babu dimukradiyya a Nijeriya sabanin abinda a ke ikirari. An gayyaci Fasto Bakare ne saboda ya ce makomar Jonathan ita ce talauta Nijeriya bisa la’akari da irin almundahanar da a ke tafkawa a kasar tun ma kafin 2015. Abinda Bakare ya fadi kenan. Har yanzu babu wanda ya shaida mi ni cewa an gano bindigu ko bama-bamai a gidansa ko mujami’arsa da za a iya yin kokwanton cewa ya na shirin kifar da gwamnatin Jonathan ne ko kuma a matsayin wata shaida da ke nuna cewa shi dan ta’adda ne.

To, amma mene ne laifin kalaman na Fasto Bakare, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar CPC a zaben 2011? Idan don ya ce makomar Jonathan ita ce talauta Nijeriya, to me ye laifi a wannan? Shin ba abinda Jonathan ke aikatawa din ba kenan? Idan har Jonathan zai iya barnata Naira tiriliyan 2.6 ga masu kawo mai na karya, alhali sauran shugabannin kasar na baya su na kashe kasa da biliyan 300, ta yaya ma wani zai ga laifin lafazan Bakare? Ko kuwa shugaban ya na so ya mari ’yan Nijeriya ne ya kuma hana su kuka? Gaskiyar magana ita ce, idan har shugaban kasa zai kashe tiriliyan 2.6 a shekarar zabe maimakon biliyan 245 na tallafin mai, shin ba zai zama abu mai sauki ga dan kasa ya ce Jonathan ya na neman tsiyata kasarsa ba? Kai Bakare ma ya yi sassauci da yawa ga shugaban kasar. Lamarin ya fi haka la’acewa. Idan da a ce dimukradiyya na aikinta yadda ya dace, ai da tuni an tsige shi bisa aikata wannan danyen aiki na barnata tiriliyan 2.6 ba bisa ka’ida ba.

Faston ya kuma nusar da cewa, a matakin da cin hanci ya ke a kasar da Jonathan ke jagoranta, babu fa’ida a yi magana ma kan 2015. Fasto Bakare ya furta abinda kowa ke furtawa ne. Ya yiwa shugaban alfarma ne ma da ya sanar da shi abinda kowa ya fadi – ciki kuwa har da wadanda ke ikirarin su na tare da shi – amma su ke fadi a bayan idanunsa. Ni Ina mamakin yadda babu wanda ya taba bude baki ya gaya ma sa gaba da gaba. Tiriliyan din Nairori da a ka sace a karkashin kulawar Jonathan za su iya sanyawa kasar ta durkushe idan ba a hana ba.

Sace kudin tallafin mai, fashin kudin ’yan fansho, wawure gangar mai akalla 400,000 kullum ba bisa ka’ida ba, cefanar da rijiyoyin mai 245 da sauransu da sauransu ba abubuwa ne da sa mu su idanu ba. Eh, Nijeriya ta yi suna wajen tafka almundahana a idanun duniya, amma ba irin wannan rashin hankalin da mu ke gani a gwamnatin Jonathan ba. Wannan ne hakikanin abinda ya hana komai aiki a kasar. Lokacin da Jonathan ya yi alkawarin kawo sauyi, ba mu san irin sauyin da ya ke magana a kai ba. Hatta Naira biliyan 300 da Yar’Adua ya saki kafin ya kwanta jinya don gyara yankin Neja Delta, har yau ba a san inda su ka kwana ba. Rabin kudin PTF ta kashe a kasar bakidaya a ka ga bambanci.

Kuma ma don karin abin haushi shi ne Shugaba Jonathan ya umarci matsiyancin gwamnan can Henry Seriake Dickson na jihar Bayelsa ya nada matarsa mukamin babbar sakatare. Hakan ya biyo bayan bai wa bokansa, Tompolo, kwangilar tsaron tashar sauke kayan da a ka yi jigalar su a jirgi ne fa. Watarana lokaci zai zo wanda a bainar jama’a za a shaidawa ’yan Nijeriya hakikanin dangantakar Jonathan, babban kwamandan askarawan Nijeriya, da dan bindiga (tsoho ko mai yi), wanda ayyukansa su ka halaka sojoji da dama a kasar. ’Yan Nijeriya da dama har ma da ’yan kasashen waje sun shiga rudani kan ainihin dangantakarsu. Hakika lamari ne mai cike da dimuwa.

Ya kamata Shugaba Jonathan ya san cewa, ’yancin fadar albarkacin baki ya na daya daga cikin alfarmar dimukradiyya. Kamar yadda ’yancin wallafawa da yin abota su ke, haka nan fadin albarkacin baki ba za a turbude shi a dimukradiyya ba. Tauye hakkin fadin albarkacin baki ya zama al’ada a gwamnatin Jonathan. Shugaban ya na so ne ya rika aikata duk abinda ya ga dama ba tare da a na sanya ma sa shingaye ba. Ya na son kashe Naira tiriliyan 2.6 a shekarar zabe duk da majalisar dokoki ta kasafta Naira biliyan 245 ne kacal, amma ba ya so Fasto Bakare ya ce kanzil! A bara an tsare Nasir el-Rufai, daya daga cikin ’yan adawa na siyasa, a filin saukar jiragen sama, saboda rubutun da ya yi a kan shugaban kasar, kuma a 2011, gabanin zabe, jami’an SSS sun gayyaci Bola Tinubu saboda ya ce, ’yan Nijeriya su daina sauraron bugaggen mai kamun kifi, wato ya na nufin Jonathan. Martani ne fa ga Jonathan din bisa kiran ’yan jam’iyyar ACN da ya yi da ‘’yan iska’ a lokacin da ya ce “Kudu maso Yamma ta wuce a bar wa ’yan iska ita”. Tabbas al’ummar yankin Kudu maso Yamma sun mayar da martani ta hanyar kin zaben jam’iyyar Jonathan da Obasanjo a bakidayan yankinsu, kuma a nan an gane su wa su ka mayar ’yan iskan.

Abu ne mai wahala ga duk wanda ke kaunar Nijeriya ya iya tsuke baki ya na kallon yadda a ke tafiyar da kasar a halin yanzu. Fasto Bakare ya taimakawa shugaban kasar ne kawai don ya fahimci yadda ’yan Nijeriya ke ji a ransu game da shi. Fasto Bakare ya kuma ce, juyin-juya hali lallai zai afku a Nijeriya, saboda salon yadda a ke tafiyar kasar, musamman kan irin yadda a ke barnatar da arzikin kasar.
Shugaban ya nuna cewa, hakan fa ko a jikinsa. Shugaba Jonathan ya kamata ya sani cewa, ya na rubutawa kansa tarihi ne ta hanyar sigar da ta tafiyar da Nijeriya. Don haka tilas ya sauya salonsa ya kuma fara nuna halin-ko-in-kula.

Daga Jaridar Leadership Hausa

No comments:

Post a Comment