Monday, July 9, 2012

Ra'ayin Aminiya: Kalubalen Dake Gaban Sambo Dasuki


Mako biyu da suka gabata ne Shugaba Goodluck Jonathan ya bayar da sanarwar sallamar Janar Andrew Owoeye Azazi daga mukamin Mai Bayar da Shawara ga Shugaban kasa kan Harkokin Tsaron kasa (NSA). Kuma ya sallami Dokta Bello Haliru Muhammad daga mukaminsa na Ministan Tsaro. Kuma a take cikin sanarwar ya bayyyana nada wani Kanar din soja mai ritaya Alhaji Sambo Dasuki a matsayin Mai Bayar da Shawara kan Harkokin Tsaro na kasa don maye gurbin Azazi; sai dai ba a fadi wanda zai maye gurbin Dokta Halliru ba. Sauye- sauyen manyan shugabannin tsaron kasa sun zo a lokacin da kasar take fama da kalubale a bangaren tsaro. Don haka Sambo Dasuki ya san irin aikin da ke gabansa.

kalubalen Boko Haram na nan, wadda a fagen siyasa ake kallonsa a matsayin babbar barazana ga dorewar kasar nan a matsayin kasa daya. Tun shekarar 2009 kungiyar ta fara adawa ga hukumomin kasar nan inda a karshe ta kai ga kaddamar da hare-haren da suke jawo hankalin manyan kasashen duniya kan yadda Najeriya ke neman zama dandalin ayyukan ’yan ta’adda. Kuma a makon jiya sai ga sashin harkokin cikin gida na Amurka ya bayyana wasu fitattun ’yan Boko Haram uku a matsayin ’yan ta’adda. Yin hakan kowa wani cikasa ne ga kasar nan da al’ummarta. Sai dai ba Boko Haram ne kawai matsalar da ke barazana ga zaman lafiya a tsakanin ’yan Najeriya ba, kuma ke kawo gibi a tsakanin hulda tsakanin Najeriya da sauran kasashe ba.

Mugun aikin nan na sata da garkuwa da mutane don a samu kudi da aka fi yi a kudancin kasar nan shi ma matsala ce da ke damun kasar nan, kuma ga alama matakan da hukumomi ke dauka sun kasa kawo karshen lamarin. Matsalar ta fi kamari a yankin Neja-Dalta, inda babban dalilin yin hakan shi ne a kwakuli kudi ko ta halin kaka. A wasu lokuta wadanda aka yi garkuwar da su kan rasa rayukansu koda an biya kudin fansar. Fashi da makami ma wata mummunar matsala ce ga harkokin tsaron kasar nan.

A ’yan kwanakin nan an rika cuda ayyukan da suka shafi keta harkokin tsaro ta hanyar fashi da makami da batun Boko Haram, a wasu lokuta akan bayar da bayanan karya kan hakikanin barazanar kungiyar a wasu jihohi musamman a Arewa. Kuma babban bangaren da mabarnata suka fi baje kolinsu shi ne bangaren satar man fetur, inda kasar nan ke tafka asara daga gagarumar satar danyen manta. Ba abin mamaki ba ne da suka mayar da hankali wajen wannan aika-aika a yankin Neja- Dalta.

Manyan kamfanonin mai ciki har da Shell sun ruwaito mummunar sace danyen man fetur da ake yi wa Najeriya. Wasu su kiyasta ana sace danyen man ganga dubu 400 a kullum. Muhimmancin kawo wadannan bayanai ita ce, duk da kasancewar jami’an tsaro a daidaikunsu da kuma a hade ta hanyar Rundunar Musamman ta Soja (STF) da ke suke aiki domin dakile wadancan barayi, satar tana ci gaba da gudana, inda barayin ke samun biliyoyin Dala a shekara, kuma akwai yiwuwar da hadin bakin jami’ai ko hukumomin tsaron. Idan aka tattaro irin wadannan matsaloli za a ga cewa Sambo Dasuki zai fuskanci matsaloli masu yawa kuma masu wahala da suka shafi tattalin arziki da siyasa ba sun takaita ga ayyukan Boko Haram na zubar da jini kadai ba ne.

Yana da kyau Dasuki ya fahimci yanayin hadakar al’ummar Najeriya da dalilan da suke kawo irin wadancan miyagun ayyuka a tsakanin jama’a, domin nemo maslahar da ta dace. Akwai matsalolin da suke da tushe daga siyasa saura kuma daga kuncin rayuwa. Mafi yawansu kuma tantagayyar ayyuka ne na miyagu. Kowanne zai bukaci magani na daban; fahimtar tushensu zai sa a samu maganin da ya dace wajen kawar da su. Wajibi kuma Dasuki ya koyi darasi daga kura-kuran Azazi, babba daga ciki dabi’ar bangaranci da ya kawo a yayin gudanar da aikinsa na Mai bayar da Shawara kan Harkokin Tsaro na kasa. A lokacinsa, tunanu da inda yake zuwa sun takaita ne ga halartar tarurruka da al’amuran da suka shafi tsaro idan wurin da ake taron yana yankin Kudu maso Kudu. Ya shuka tare da rainon tunanin cewa matsalar tsaro abu ne a tsakanin Arewa da sauran sassan kasar nan, ya daukaka matsayin Boko Haram zuwa babbar ko ma ita ce kadai barazana ga mulkin Shugaba Jonathan ta kokarin kakabata ‘ga ’yan siyasar Arewa da janar-janar masu ritaya.’

Babu wani bayani da ya nuna Azazi ya taba ziyartar wuraren da aka yi artabu a Arewa, musamman Damaturu a Jihar Yobe da Maiduguri a Jihar Borno, tunda aka fara kai hare-haren bama-bamai shekara biyu da suka gabata, domin gane wa idonsa akalla koda ya fahimci irin kalubalen da ake fuskanta. Ta hanyar zuwa wuraren a Alhamis din makon jiya, Dasuki ya nuna ya yi niyyar gano bakin zaren wannan matsalar. Kuma wajibi ne ya tafi Kudu ya duba wurare masu matsaloli ya auna abubuwa da kansa kafin ya zauna don fuskantar wannan babban kalubale ba tare da ya jefa kansa a cece-ku-ce marasa amfani ba.

Daga Jaridar Aminiya

No comments:

Post a Comment