Wannan Dandali Matattarar Tunani na ce, wato inda nake Bayyana ra'ayina game da al'amura daban - daban dake faruwa a harkokin rayuwarmu ta yau da kullum. Musamman akan siyasar Kasarmu Nigeria, nahiyarmu Africa, wani lokacin ma da duniya baki daya. Allah yayi mana Jagora!
Wednesday, May 30, 2012
Taimako: Bankin Musulunci na Barazanar Rashin Abokan Harka
Wani lokacin abubuwa suna bani mamaki, ka fin bude Ja'iz Bank PLC a kasar nan, wato bankin Musulunci da ba riba ko ruwa a cikinsa, abin kusan zama yaki yayi tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kirista. Ta bangaren Musulmai mutane da dama suna ta hura hanci sai an bude wannan banki, tunda dai Musulmai ne ke da rinjaye a Nijeriya, da sauran maganganu daban daban. Har wannan dalili ya sa daya bangaren mabiya addinin kirista suka shiga gaba da abin saboda a tunaninsu yin hakan kamar Musuluntar da kasar ne baki daya. Ba na mantawa har zanga - zangar nuna kin amincewa da kafuwar Bankin Musulunci a kasar nan, shugaban mabiya addinin kirista ya jagoranci wasu matasa. A haka cikin yardar Allah dai har aka kai ga nasarar bude bankin a wasu sassa na kasar nan.
Saboda jajircewa da gwamnan Babban Bankin Kasar nan, ya nuna Malam Sanusi Lamido Sanusi har bakin jini yayi a lokacin a wurin wadanda ba sa goyon bayan zuwan bankin.
Wani abin haushi yau gashi an bude bankin, kuma Musulman da suke ta fadin ko ana ha maza ha mata, ko ta halin kaka sai an bude bankin, yanzu sun ja baya, sun zubawa bankin ido kowa ya ki zuwa ya bude account ya fara ajiya a ciki. Wannan dalilin yasa bankin ya shiga barazanar rashin abokan harka (costumers), wanda kuma idan aka tafi a haka komai na iya faruwa.
Tabbas idan muka zuba ido muna gani wannan banki ya durkushe to lalle za ayi mana dariya, za a yiwa addininmu isgilanci, kuma za a dauke mu masu son addininmu a iya fatar baki, kuma wallahi idan hakan ya faru ko a ranar lahira sai Allah ya tuhume mu akan hakan.
Ya ku 'yan uwana Musulmai maza da mata, mu taimaki wannan banki, mu taimaki addininmu, mu garzaya zuwa cibiyoyin wannan banki na Ja'iz da suka fara aiki domin fara ajiya a ciki, hakan ne kadai zai taimaki wannan banki daga barazanar daya ke ciki a yanzu.
Ja'iz Bank PLC na da reshina a birnin tarayya Abuja, jihar Kano da kuma jihar Kaduna.
Fatan za ka/ki sanar da wadanda ba su sani ba.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Allah ya saka da alheri sa,amma baka bamu chikekin adereshin su ba a Abuja,da kaduna.dayawan mu bamu san ta fara aiki ba.
ReplyDeleteEh na san dai location din inda na Kano yake, wanda yake akan titin Murtala Muhammad Opp. Zenith Bank. Amma zan yi kokacin dubo inda na Abuja da na Kadunan suke.
ReplyDeleteAllah Ya saka da alheri...A gaskiya al'ummar musulmai muna da sakaci sosai,wannan damace da zamu tallafama kammu da kammu idan muka duba banki nawa muke dashi acikin wadannan commercial banks dake akwai a Nigeria? don haka ya kamata mu buda account a wannan banki domin cigaban addini, yankimmu dama kasa baki daya! Ga adireshin JA'IZ Bank a Abuja:
ReplyDeleteNO 73 Ralph Shodeinde Street,
Central Business District,
Abuja
Ofishin yana kusa da Ministry of Finance, haka kuma idan kazo Babban cocin Abuja ta baya zaka iya ganin bankin. Allah yasa mu dace
Malam Sunusi muna godiya da wannan gudunmawa taka. Allah ya saka da alheri fatan 'yan uwa musulmi za mu farka.
ReplyDelete