Ranar 29 ga Mayu kowace shekara rana ce ta tarihi, kuma rana ce ta hutu a dukkan fadin kasar nan, tun daga shekarar 1999, wato a ranar ne mulki ya dawo wurin farar hula daga hannun sojoji masu kaki. Wannan dalili ya sa ake kiran ranar da suna "DEMOCRACY DAY" wato ranar Demokradiyya. Dukkan kasashen da suka kan tsarin demokradiyya 'yan kasar sukan shirya gagarumin bukuwa idan ranar irin wannan rana ta zagayo musu, ranar da mulki ya dawo hannunsu, suke da wuka da nama a cikinsa, wato suke da 'yancin zabe ko su shiga takara a zabe su.
Ba komai yake sa jama'a farin ciki ba idan irin wannan rana ta zagayo, sai don yadda 'yancinsu shi ne kan gaba sama da komai, saboda wannan dama da suke da ita ta 'yancin zabe, saboda ta haka ne kadai suke da damar canja duk wani shugaba da yayi musu alkawari ya kuma saba musu.
Saboda irin wannan 'yanci wasu kasashe da dama suka fafata yaki suka sadaukar da rayukansu domin samun 'yancin. A baya bayan nan kasashe irin su Tunisia, Egypt, Libya da sauransu duk sai da suka zage kwanji kafin 'yancin nasu ya samu. Amma mu Nijeriya mun samu wannan 'yancin ne cikin ruwan sanyi ba tare da ja'inja ba. Sai dai kash! Mafi yawa daga cikin al'ummar kasar ba sa amfana da wannan 'yanci, saboda ba kasafai suke zaben ake basu wanda suka zaba ba.
Wannan dalili yasa ko da irin wannan rana ta Demokradiyya ta zagayo ba mu fiye ba ta muhimmacin kamar wadanda suke cikin ribar demokradiyyar ba. Da dama cikin 'yan Nijeriya ba sa sani zuwan rana, balle sanin muhimmacinta. Duk kuwa da dumbin muhimmancinta a gare mu.
No comments:
Post a Comment