Wednesday, May 30, 2012

Janar Buhari Ya Gudanar Da Bikin Ranar Demokradiyya a Jihar Nasarawa


Tsohon shugaban kasa, kuma dan takarar shugabancin kasa a zaben 2003, 2007 da 2011, sannan wanda talakawa ke burin ya sake tsayawa takara a 2015 wato Janar Muhammad Buhari ya gudanar da bikin zagayowar ranar Demokradiyya a garin Lafia fadar gwamnatin jihar Nasarawa.

Janar Buhari ya isa garin na Lafia da misalin 10:30 na safe, duk da zuwan nasa na ba zata ne, wato ya kai ziyarar ne ba tare da sanarwa ba, amma duk da haka bai samu isa filin da aka tanada don yin taron ba sai wajen 11:30 saboda dafifin magoya baya, daga nan taro ya fara, manyan baki suka yi jawabai ciki har da Mai Girma Gwamnan jihar Nasarawa, Alhaji Umar Tanko Al-Makura, amma mai gayya mai aikin Janar Buhari bai samu damar yin jawabin a wurin ba.

Idan ba a manta ba Janar Buharin ya taba kai irin wannan ziyata ta ba zata jihar ta Nasarawa a shekarar da ta gabata lokacin rantsar da gwamna Al-Makura.

Janar din ya samu rakiyar mutane da dama ciki har da tsohon ministan birnin tarayya Abuja, Malam Nasir El-Rufai.

No comments:

Post a Comment