Kungiyar Chelsea da ke taka leda a kasar England za ta iya yin nasara a karawar da za tayi da kungiyar Bayern Munich ta kasar Germany a was an karshe na cin kofin zakarun turai (UEFA Champions League) wanda za a fafata a ranar 19 ga Mayu da muke ciki, a filin wasa na Allianz Arena take birnin Munich.
Akwai wasu dalilai da idan tarihi ya maimaita kansa za su sa Chelsea lashe kofin na zakarun turai. Wadannan dalilai ko nace tarihi sune:
A duk lokacin da Munich ta dauki nauyin wasa karshe, ana samun kungiyar da bata taba daukar kofin ba tana yin nasara. An yi wasannin karshe a filin na Allianz Arena sau uku, wanda Nottingham Forest ta kasar England ta samu nasarar lashe kofin karo na farko a shekarar 1979, sai Marseille ta kasar France ita ma ta dauki kofin karo na farko a filin wasan a shekarar 1993, sai kuma Dortmand ta Germany tayi nasara a shekarar1997 ita ma a karo na farko.
To saboda haka idan Chelsea ta dage za ta iya zama kungiya ta hudu da ta fara yin nasarar daukar kofin a filin na Allianz Arena.Sai kuma wani tarihin makamancin haka, tarihi ya nuna ba kungiyar da aka taba yin wasa a filin wasanta kuma tayi nasarar daukar kofin, hasalima kungiyar AS Roma ta kasar Italy itace kadai ta taba yin nasarar zuwa wasan karshe ta doka a filinta, sai kuma Bayern Munich a wannan lokaci.
Ita ma Roma ba ta yi nasarar daukar kofin ba a filin wasanta na Olympic wanda ya gudana a shekarar 1984.Wannan ma wata dama ce da za ta karawa kungiyar ta Chelsea kwarin gwiwa, ita da magoya bayanta baki daya.
To mu dai kallo ne kadai namu, sannan “ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare” in ji masu iya magana.
Bashir Ahmad
bashgy90@yahoo.co.uk
No comments:
Post a Comment