Tuesday, May 29, 2012

Sakona Zuwa Ga Shugaba Goodluck Jonathan


Kamar yadda kowa ya sani yau May 29 rana ce ta farin ciki ga kasar Nijeriya, amma kuma ranar bakin ciki ga mafiya yawan 'yayanta, saboda ranar ne ake nada sabbin barayi a matsayin jagororinmu.

A kashen duniya daban daban musamman masu bin tafarkin demokradiyya idan irin wannan rana ta zagayo musu 'yan kasar sukan rubuta sakonni kala kala don aikawa da shugabanninsu na taya murna da zagayowar ranar da kuma neman ayi musu wasu ayyukan ci gaba a wasu bangarori dake bukatar hakan. Sannan kuma shugaban ya fito fili ya yiwa 'yan kasar jawabin irin ci gaban da suka cimma a shekarar da ta gabata.

To yau ni ma zanyi koyi ga irin wadannan al'ummoni, wato zai aikawa shugaba Goodluck Jonathan sakona a wannan rana ta farin ciki.

Sakona zuwa ga shugaba GEJ: Ya mai girma shugaban tarayyar Nijeriya da ta hada da shiyoyi guda shida, jihohi 36 tare da birnin tarayya Abuja, ina taya ka da sauran 'yan kasa murnar zagayowa wannan rana wadda ka cika kwana 365 a karagar mulki baya ragowar mulkin Marigayi Malam Umar Musa Yar'adua da ka karasa. Ya mai girma shugaba muna yaba ma da irin kokarinka na fitowa kafafen yada labarai kana bayyana irin tsare tsarenka, sai dai kash! Har yanzu baya karasowa wurin talakawa bamu sani ba ko baka san da hakan ba.

Shugaba GEJ yau shekararka daya kenan akan gadon mulki, a lokacin da kazo jiharmu Kano yakin neman zabe ka yi mana alkawarin za mu shaki Fresh Air idan ka samu damar kaiwa bantenka, amma sai gashi har yanzu iskar ko yankinmu na Arewa ma bata karaso ba, kuma wadda muke amfani da ita a da, tun daga hawanka ta gurbace, fatan za ka tuno alkawarin da ka daukar mana kuma ka cika mana shi. Kafin wata shekarar mai dawowa. Muna yiwa maka fatan karasa mulkinka lafiya.

A karshe ina fatan sakona zai samu isa kunnuwan mai malafa.

No comments:

Post a Comment