Monday, April 2, 2012

Shin Gaskiya Ne Nasir El-Rufai Ya Fara Yakin Neman Zaben Shugabancin Kasa Na 2015?


A jiya 02/04/2012 jaridar Sunday Trust ta kamfanin Daily Trust ta wallafa rahoton cewa Malam Nasir El-Rufai tsohon Ministan Birnin Tarayya Abuja, ya fara yakin sunkuru a fafutukarsa ta neman samun damar darewa shugabancin kasar nan a shekarar 2015 a karkashin jam'iyyarsa ta CPC mai alamar ALKALAMI.

Wannan rahoto na Sunday Trust ya ja hankalin mutane masu yawan gaske, wanda hakan ya haifar da tattaunawa mai zafi a shafukan internet. Wani bangare daga cikin mutanen na nuna goyan bayansu, wani bangaren kuma na nuna rashin goyan bayansu, wasu kuma na addu'ar Allah ya kawowa kasarmu Nijeriya mafita.

Wannan dalili ya sa na dauki wayata domin kuwa ina da lambar wanda ake tattaunawar akansa wato Malam Nasir El-Rufai, kuma cikin ikon Allah yana daya daga cikin manyan mutanen da duk da karancin shekaruna suna bani damar tattauna abubuwa da su, masu amfani musamman game da ci gaban al'ummar kasar nan.

Na kira Malam da misalin 11:30 na daren jiyan domin na tabbatar da gaskiyar rahoton Sunday Trust daga bakinsa, saboda bada kwakkwaran amsa ga mutanen da suka tambaye ni gaskiya labarin.

Bayan mun gama gaisawa da Malam, kai tsaye na shiga abinda ya sa na kira Malam wato tambayar "Shin menene gaskiyar labarin da jaridar Sunday Trust ta wallafa a yau dangane da maganar fara yakin neman zabenka a matsayin shugaban kasa a 2015?" sai Malam ya bani amsa da cewa "Kamar yadda nake fada a koda yaushe bani da burin yin kowace irin takara a 2015, saboda haka ba ni na bada umarnin a fara yi min yakin neman zabe ba, babban burina a yanzu shi ne na ga jam'iyyar CPC ta samu nasara, amma duk da haka ina godiya ga masoyana"

Bayan amsar tambayata da na samu a wurin Malam, sai na sake jefa masa wata tambayar wadda ta dade a raina "Shin Malam ya maganar kwamitin sake yiwa jam'iyyar CPC garanbawul wanda kake shugabanta?" nan ma dai Malam ya bani gamsasshiyar amsa ba tare da nuna gajiyawa ba, kamar haka "Wannan kwamiti yana nan yana aiki ba dare ba rana, musamman a yankunan da CPC ba tayi karfi ba, sannan kwanan nan ku ma irin ku matasa za ku shigo tafiyar wannan kwamiti domin samun nasarar abubuwan da aka sa a gaba.

Daga nan muka yi Sallama da Malam, na yanke layin wayata.

A karshe kamar yadda Malam Nasir El-Rufai ya bayyana, ya kamata duk masu kudirin neman wata takara a 2015 musamman mabiya jam'iyyar CPC da su dakatar da wannan kudirin nasu, su zo don bada gudunmawar gina jam'iyyar tukunna, wannan ne kadai zai kawowa jam'iyyar nasara a dukkan zabukan da zata tunkara nan gaba.

Bashir Ahmad
bashirgy@yahoo.com
08032493020

1 comment:

  1. A Zahirin Gaskiya wannan shafi naka na dandalin Bashir ya hadu kuma pages dinka suna da kyauda abubuwa da yawa dana gani a ciki Allah ya saka maka da alkairi gaskiya zan i will bookmark yourpage
    you can check me www.nasiruloaded.blogspot.com

    ReplyDelete