Wednesday, April 25, 2012

Asalin Maguzawa

Babu wani takamaiman bayani a kan asalin kalmar ‘Maguzawa’, wato babu wanda zai ce ga daga inda ta samu, sai dai akwai bayanai na tarihi a kan Maguzawa. Ko da yake Maguzawa a yau suna nufin Hausawa wadanda ba Musulmi ba, wato wadanda suke bin addinin gargajiya.

A Kano wadansu masana suna ganin cewa Maguzawa kabila ne daga cikin kabilun da suka hadu suka yi Kanawa, suna ganin Maguzawa suna daga cikin birbishin jikokin Barbushe wadanda suka bai wa tsafin Tsumburbura gaskiya sosai. Su ne kuma suka ki karbar Musulunci a farkon lokaci, don haka duk Bahaushen da bai musulunta ba ake ce masa Bamaguje.

Ko ma dai yaya labarin yake, akwai Hausawa da suka ki karbar Musulunci a cikin birane, kuma hakan ya sa suka yi nesa da birane zuwa cikin dazuzzuka domin kubutar da tsohon addininsu da sauran al’adunsu na iyaye da kakanni. Haka kuma akwai wasu tarin Hausawa da suke cikin qauyuka wadanda sakon bai ma je musu ba, don haka suka ci gaba da addininsu na gargajiya.

Wadannan mutane a yau su ne ake kira Maguzawa. A iya cewa akwai bambanci tsakanin Arna da Maguzawa duk da cewa Sarkin Arna shi ne mai kula da tsafi tun kafin Musulunci a tsarin addinin gargajiyar Hausawa.

Kalmar arna an fi amfani da ita a yau a kan wadanda ba Musulmi ba sannan ba kuma Hausawa ba. Ba a cewa Arnan wata kabila Maguzawa, sai dai Arnan Hausawa kawai. Don haka a iya fahimtar cewa kalmar Maguzawa a Hausa tana da alaka da kabila ne, ba kawai suna ba ne na masu bin addinin gargajiya. A cikin tarihin Gobirawa sun ce masarautun kasar Hausa da suka sallamawa Sarkin Alkalawa (Gobir) su ne Adar da Yawuri da Mazamfara da Zazzau da Katsina.

Wadanda suka ki kuma su ne Kano da Daura da Rano da Hadeja. Sai sauran Hausawan da suke tare da Alkalawa suka kira wadanda suka ki bin su Maguzawa, wato Kano da Daura da Rano da Hadeja su ne Maguzawa. Wannan kuma shi ne asalin Maguzawa. Wannan kalma ta Maguzawa irin ta ce Turawan Ingilishi suke amfani da ita wajan bayyana waxanda ba Kiristoci ba, wato Pagan.

Ita wannan kalma sun are ta ne daga harshen Latin, wanda shi ne harshen daular Rome. Sarkin Rome Costantine shi ne farkon wanda ya karbi addinin Kiristanci, ya yi umarni da sauran mutane su karbi wannan addini. Kowa ya karba sai mutanan Pagus, don haka duk wanda ba Kirista ba ne, ake ce masa Pagus ko da ba daga yankin Pagus yake ba.

Wannan ya yi kama da dalilin da wasu suke cewa Maguzawa kabila ne daga kabilun Hausawa.

Shahararren marubucin Hausan ne Ado Ahmad Gidan Dabino ya rubuta wannan makala a shafin wannan dandali dake shafin sada zumunta na Facebook, Allah ya karawa Malam basira amin.

1 comment:

  1. Naji dadin rubutun ka domin kuwa ka wayar da kan mutane da dama.. Toh, tunda bamagujen da ya karbi musulunci ba a kiran shi bamaguje sai musulmi... Me yasa wadansu suke alakanta maguzanci ga hausawan dake kirista.. Ashe bamagujen da ya karbi adinin kirista shima ya wanku kenan daga wadancan tsofin al'adu? In ko hakane ya kamata ka wayar da kan mutanenka a wannan... In dai maganar da kayi gaskiya ce. Nagode, Ishaku daga kaduna

    ReplyDelete