Saturday, April 14, 2012

Har Yanzu Talakawan Nijeriya Ba Su Gaji Da Zaben Gen. Muhammad Buhari ba

Tun bayan maganar da Janar Muhammad Buhari ya fada a lokacin da wasu magoya bayansa suka kai masa ziyara a gidansa dake Kaduna wadda ya bayyana cewa "Zai kasance a harkokin siyasa har sai lokacin da abubuwa suka daidaitu, sannan talakawan Nijeriya suka fara cikin ribar demokradiyya a kowane mataki na gwamnati"

Wannan magana da Janar Buhari ya yi ta zama kamar wata allura ya zikarawa talakawan kasar nan, ba don komai ba sai don a tunanin talakawan wannan maganar da Buhari ya yi na nufin zai sake tsayawa takarar shugabancin kasa a zaben 2015 kenan. A cewa wasu da dama sun bayyana cewa tun da Janar ya yi wannan magana to zai sake yin takara kenan, saboda har yanzu babu wanda zai iya daidai al'amuran kasar nan har talaka ya fara cin ribar dimokradiyya idan ba Baba Buharin ba.

Wasu kuma goyon bayansu suka nuna ga Janar Buhari tun kafin ya bayyana da bakinsa cewa zai tsaya takarar a 2015, inda za kaji suna fadin "Za mu ci gaba da dangwalawa Buhari kuri'armu koda za'a ci gaba da murde mana" wani bangaren kuma na fadin "Idan Buhari zai tsaya takarar sau 1000 ana murde masa ba zamu taba gajiya ba, za mu zabe shi sau 1000" da dai sauran maganganu na nuna kwarin gwiwa da rashin gajiyawa a wurin magoya bayan Buharin.

Idan ba'a manta ba Buhari a lokacin yakin neman zabensa a 2011, ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takara ba, idan kuma yayi nasara to shekaru hudu kadai kawai zaiyi, ba don komai ba saboda yawan shekaru, wanda shekarunsa za su kasance 72 a shekarar 2015.

An nakalto daga Dandali Bashir Ahmad Facebook http://bit.ly/dandali

1 comment:

  1. A gaskiyar magana talakan Nijeriya na matukar son ganin Janar Buhari akan kujerar shugabancin kasar nan.Amma sai dai kash,mu a jihar Katsina an sami babbar matsala wadda ta kawo ci baya ga tafiyar Janar Buhari.Wannan matsala kuwa ko ana so,ko ba a so sai an gyara ta sa'annan abubuwa su daidaita.Duk mai kaunar Buhari na gaskiya ya san cewar talakan jihar Katsina bai zabi Sanatoci biyu daga cikin ukun da ke majalisa yanzu ba.Haka kuma kowa ya sani jam'iyyar PDP ba ta yi takara da wadannan 'yan majalisar tarayya su takwas ba.Don haka kowa ya sani cewar babu yadda za ayi ka dauki kujera ka baiwa mutumin da bai shiga 2ndary election ba,kuma ka yi tunanin wai PDP ta zura ido.Kowane dan Adam na iya yin kuskure a rayuwa,amma ba zai sake zama kuskure a sake maimaita wannan abun da aka kira kuskure ba.Ya zama dole talakan jihar Katsina ya nuna fushinsa akan haramta masa abin da ya sha rana da yunwa ya zaba.Bugu da kari kuma sai ga shi su mutanen da ke majalisar sun tozartar da tunanin talaka na samun hanyar da za a rage masa radadin talaucin dake addabarsa.Bashir idan dai da gaske ne kuna son Janar Buhari tsakaninku da Allah,to ya kamata ku sake nazarin abubuwan da suka faru a baya don ku gyara.Amma idan kuma kuna tunanin abin da aka yi daidai ne to sai mu yi addu'ar Allah ya saka ma duk wanda aka zalumta koda kuwa ba musulmi ba ne.

    ReplyDelete