Monday, April 30, 2012

Shekara Daya Bayan Zaben 2011

A nawa tunani ba abin da ya kai tarihi dadi. Dadin nasa kuwa ya fi armashi a lokacin da mutum ke biye da aukuwar tarihin cikin natsuwa da fahimta da kuma nazari. Shi tarihi kamar yadda masana suka yi nuni ba wani abu ba ne sai wanzuwar al’amurran da mutum da kan sa ya gina ya kuma tabbatar da gudanuwarsa. Dukkan abin da ka aikata dazu-dazun nan ko jiya ko shekaran jiya ko kuma wasu kwanaki ko watanni ko ma shekaru a baya su ne tarihinka ko tarihin al’umarka. Yake-yake da takaddamar mulki da aure da siyasa da neman ilmi da ma dukan zamantakewar yau da kullum cike take da taskokin rayuwa na tarihi. To amma shi tarihin nan da muke magana ba kowa ke gane aukuwarsa ba, ba kowa ke fahimtar irin wainar da ya toya ba, ba kowa ne ke cin moriya ko gajiyarsa ba. Ba kuma wani abu ya jawo haka sai ganin cewa sinadiran da ke dabaibaye da aukuwar tarihi masu sarkakiya ne, fahimtar su sai mai riskar al’amurran bisa yadda ya kamata. Ke nan tarihi shi ne rayuwa, fahimtarsa ko gane aukuwarsa ita ce gishirin rayuwar, aiki da abin da tarihin ya kyallaro kuma shi ne abincin rayuwar. Shi ya sa masana ma ke ikirarin duk wanda bai san abin da ya faru ba( a gidansu, ko unguwa ko kauye ko kasa) kafin a haife shi, wato bai nakalci tarihin rayuwarsa ba, zai kasance tamkar jariri ne, wato bai san komi game da rayuwa ba. Shi kuwa jariri ai mun san ba kawai rashin sanin abin da ya wakana ba ne ya dame shi, a’a, jikinsa da kwakwalwarsa da yanayin ginuwarsa duk suna da nakasu. Ke nan bai da wani amfani a irin wannan rayuwa. Idan haka ne, kuma hakan ne, me ke nan za mu ce mun karu da shi a lokacin da muke bikin cika shekara daya da zaben shugaban kasa da aka yi a watan Afrilun shekarar 2011 a wannan makon? Wadanne darussa muka karu da su daga abin da ya faru cikin wannan shekara guda mai dimbin tarihi? Shin tarihin da muka baro a baya ya kasance mai dadin ji ne ko gani? Shin akwai ma tarihin da za mu iya tsinkaya a cikin wannan shekara guda? Ko kuwa dai abin nan ne da masana ke nuni, ga tarihin ya auku amma mun kasa fahimta saboda tulin jahilci. Abin da zan yi a wannan karon bai wuce kokarin komawa baya ba domin na ga irin rawar da muka taka ko kuma in mun karu da wani abu na a-zo-a-agani! Haka kuma da kokarin ganin ko za mu iya dorawa daga inda muka baro. Domin kuwa amfanin tarihi shi ne kada a bari ya maimaita kansa, duk kuwa da masana na nuni da cewa da ma can bai maimaita kan nasa. A nan ina magana ne ko za mu iya hasashen gaba daga abin da jiya ta haifar mana a yau. Mu soma da hayaniyar da ta biyo bayan zaben shugaban kasar da aka yi a watan Afrilun 2011 din. Shin kashe-kashe da tashin hankali da ya faru me ya koyar da mu? Ba wani abu da ni na fahimta da ya wuce talakawan kasar nan har yanzu ba su gama wayewa ba. Duk da irin hayaniyar da aka yi da tashin-tashinar da ta biyo baya ganin wai an hana mutane zaben wadanda suke bukata, har yau ba ta sauya zane ba, domin kuwa ko bayan badakalar Jega ta 2011, har yau ana nan inda ake. An sake gudanar da zabubbuka a wasu jihohi, kuma tamkar jiya i yau! Shin talakawan sun sami damar barje guminsu? Ko alama! Abin da ya faru a jihohi biyar da aka sake gwabzawa a fagen zabe ya ishe mu misali? Nan ma din ba a bar talaka ya sake zabar wadanda yake so ba ne? Na yi wannan tambayar ne domin kuwa da alama akwai muna-muna dangane da kowane irin zabe a kasar nan, ciki kuwa har da hadin bakin talakawan da ke kukan ba a ba su dama suka zabi wadanda suke so ba. Me ya faru a Sokoto da Adamawa da Kogi? Shin mun koyi wani abu daga tarihin abin da ya wakana a zaben 2011 daga wannan zabe da aka yi a wadannan jihohi? Da alama ba mu koyi komi ba, ko kuma ba mu damu da mu koyi komi ko kuma mun koya mun dai kasa aiki da abin da muka koya. Bai yiwuwa a ce an yi kashe-kashe da raunatu mutane bilahaddin da lalata dukiyoyin jama’a saboda ba a son abin da ya faru bayan zabe, sa’annan a ce ‘yan watanni kadan angulu ta koma gidanta na tsamiya. Akwai dai wani abu da kila har yanzu ba mu kai ga gane shi ba. Idan kuma wannan bai ishe mu misali ba, to me za mu ce game da zaben da Jega ya gudanar a jihar Kebbi? Shi kuma wane tarihin ne ya koya mana na irin wannan badakalar? Shin da gaske ne mutanen jihar Kebbi sun sake yi zabe bayan wanda aka gudanar a shekarar 2011? Ina jam’iyyar CPC a jihar Kebbi? Ina dan takararta da ya fadi zabe ya tafi kotu, kotun ta ce a sake zabe? Ina ya shiga, me wannan ya koya mana? Shin ba a sake zaben ba? Wane darasi ke nan muka karu da shi daga zaben 2011 da ya sa muka yi wannan juyin-juya- hali a jihar Kebbi da aka je har kotun koli, aka rushe zabe, amma jam’iyyar da ta yi nasara ta bar wa wanda ta kada a kotu fili domin ya wataya? Wane irin tarihi ne wannan? Ba wannan kadai ba, shin tun da aka kammala zaben shekarar 2011 zuwa yau wane irin ci gaba muka samu? Shin gwamnatocin da muka ‘zaba’ wane irin ci gaba suka kawo mana? Idan babu to wane darasi ko tarihi muka tsinkaya? Shin alkawurra nawa gwamnatocin nan suka yi mana kafin da bayan zabe, shin nawa suka cika? Idan ba su cika ko daya ba to me muka koya daga wannan tarihi? Shin zaben 2011 ya canza mana rayuwa ko yaya take a yanzu? Shin ina wadanda suka rasa gidajensu suke zaman gudun hijira saboda aukuwar wancan zabe? Suna nan a sassanin gudun hijira, shekara guda da yin wancan zabe? Ina darasi a nan? Shin tallafin albarkatun man fetur da aka janye ya kare mu da wani abu? Shin zaben nan ya kawar da tashin-tashina irin ta Boko Haram da fashi da makami da kashe-kashen addini da kabilanci da makamantansu? Idan duk tsawon shekarar nan ba ta canza zane ba, me ya sa? Wane tarihi muka hango game da haka? Anya kuwa muna karuwa da wani abu ko dai dodorido ne makomarmu da makomar kasarmu? Wani zai iya cewa ai cikin shekara guda da zaben 2011 kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. To sai me? Wane darasi muka karu da shi daga abin da ya faru? Wannan shi ne abin tambaya! Saboda haka ni dai abin da na hanga na hango a cikin tsawon shekarar nan guda tun da aka yi zaben 2011 shi ne ‘yan siyasar da muke da su, ba su canza hali ba, kuma da alama ba su da niyyar canzawa, domin ba canji suke neman su yi ba. Canjin da kawai za mu gani ko nan gaba shi ne na motoci da tufafin da suke shiga da sanyawa da kuma maka-makan gidajen da suke ginawa. Tattalin arzikin kasar nan bai ci gaba ba kuma da alama ba zai ci gaban ba, domin kuwa ba wani tubalin gini da aka aza shi bisa, in ma akwai to tubalin toka ne. Haka kuma rayuwar talaka ba za ta canza ba, domin ba a yi wata shimfida da za ta taimaka ta canza ba tun azal. Ke nan talauci da yunwa da fatara da jahilci da komadaddar rayuwar da muka baro cikin wancan tsohuwar shekarar su ne za mu ci gaba da kai da kawo da su shekara mai zuwa, idan ba mun tashi mun yi wa kanmu maganin matsalar ba. Menene maganin matsalar? Ina jin ba sai na bada amsa ba! Allah ya nuna mana shekara mai zuwa mu ga ko mun nazarci wani abu ba wai daga tarihin ba, hatta daga wannan rubutun! Daga Dr. Ibrahim Malunfashi, marubuci akan al'amuran da suka shafi rayuwar yau da kullum, musamman game da kasarmu Nijeriya.

No comments:

Post a Comment