Monday, April 16, 2012

Ngozi Ikonjo-Iweala Ta sha Kaye A Zaben Shugabancin Bankin Duniya

Babban bankin duniya ya zabi dan Amurka Jim Yong Kim a matsayin sabon shugaban bankin inda ya doke ministar kudin Najeriya Ngozi Okonjo- Iweala.

A karon farko a tarihi, an kalubalantar mamayar da Amurka ta yi wa bankin na duniya - inda kawunan masu zaben ya rabu. Mr Kim ya samu goyon bayan kasashen Turai da Japan da Canada da kuma wasu kasashe masu tasowa kamarsu Rasha da Mexico da Koriya ta Kudu.

Kim wanda shi ne shugaban Dartmouth College, zai fara aiki a ranar 1 ga watan Yuli.

A ranar Juma'a ne dan kasar Colombia Jose Antonio Ocampo ya janye daga takarar yana mai cewa "siyasa ce kawai a cikin lamarin".

Dr Kim zai maye gurbin Robert Zoellick, wanda ya jagoranci bankin tun shekara ta 2007.

Turai ta goyi bayan Amurka A tarihi dai, Amurka ce ke jagorantar bankin tun lokacin da aka kafa shi a shekara ta 1944.

Yayin da jagorancin Hukumar bayar da Lamuni ta duniya kuma, ke fadawa hannun Turawa. Sai dai ana samun karin matsin lamba domin ganin an bude kofar neman shugabancin hukumomin biyu ga kasashe masu tasowa.

Masu sharhi kan al'amura musamman a kasashe masu tasowa na ganin Ngozi ce ta fi cancanta da mukamin, ganin cewa ta shafe shekara-da-shekaru tana aiki a bankin.

Kasashen Turai da Japan na da kashi 54 cikin dari na kuri'u a zaben shugabancin bankin na duniya.

Sabon shugaban bankin zai jagoranci kwararrun ma'aikata masana tattalin arziki da kuma ci gaban kasa 9,000, da kuma ikon bayar da bashin da ya kai dala biliyan 258 - kamar yadda ya bayar a bara.

Daga BBC Hausa

No comments:

Post a Comment