Thursday, January 9, 2014

Mu Cigaba Da Son Matanmu Bayan Aure

Akwai wani mutum mai suna Balarabe, yana neman wata budurwa mai suna Ladidi da aure. Kullum yana zuwa hira gidansu da yamma budurwar tana kawo masa ruwan sha a duk lokacin da ya zo gidansu hira.

Wata rana da ya zo sai kakar Ladidi ta ce mata: “Ga kunu mai dumi ki kai wa Balarabe ko zai sha.”

Ladidi ta ce to, sai ta zo ta tambayi saurayin cewa zai sha kunu? Bayan ya yi dan murmushi ya ce "eh zan sha", sai Ladidi ta koma cikin gida ta dauko kunun da nufin ta kawo masa. Tana zuwa kusa da shi sai santsi ya dauke ta ta zame ta yi tangal-tangal ta fadi, kwanon kunun nan ya kife a jikin sabon dinkin shadda da wannan saurayi ya ci ado da ita. Hankalin wannan budurwa ya tashi, ta rude ta rasa me za ta ce masa. 

Amma shi gogan naka bai damu da jika shi da kunun da ta yi ba, hankalinsa yana kanta ne, yana cewa: “Ladidi sannu, ina fatan dai ba ki ji ciwo ba?”

Yana ta kokarin dagata da lallashinta, ita kuma da ta tashi abin da ya fi damun ta shi ne yadda ta bata masa ado da ruwan kunu. Nan take ta je ta debo ruwa a buta tana zuba masa yana wanke jikinsa, tana ta ba shi hakuri. Shi kuma yana murmushi yana ce mata, ai ba komai.

Da ya ga Ladidi tana ta nuna damuwarta kan abin da ya faru, sai ya nuna mata alamun cewa za ta bata masa rai, ya za a yi ta rinka damuwa kan abin da baitaka-kara-ya karya ba! A haka dai abin ya wuce.

Bayan wani lokaci sai aka daura auren Balarabe da Ladidi, Allah Ya azurta su da ’ya’ya guda biyu.

Wata rana da yamma Balarabe ya dawo gida don yin wanka, sai Ladidi ta kawo masa abinci. Bayan ta ajiye, sai ta je debo masa ruwa a kofi da nufin idan ya gama cin abincin ya sha ruwa. Bisa tsautsayi, sai ga babbar rigar da Balarabe ta sarkafe Ladidi ta fadi kasa, ruwan da ke kofin ya zube a jikin Balarabe, ai sai ya mike tsaye ya rinka bambami, kai ka ce wuta ta zuba masa.

“Ke dai wallahi ban san ranar da za ki yi hankali ba! Sam ba ki da lissafi da natsuwa! Idan ban da hauka da rashin hankali, me ya jawo
haka? Ke dai kam Allah wadaran ki........!”

Karshe dai wannan dalilin sai da ya janyo Balarabe ya saki Ladidi.

Mu yi nazarin wannan abin da idon basira, lokacin da Balarabe ke neman matarsa da aure, ta yi masa barin kunu mai zafi a jikin sabbin tufafinsa, amma bai nuna bacin ransa ba, hasali ma yana nuna wannan abin ba komai bane illa tsautsayi. Amma yau barin ruwan sanyi ya zama tamkar ruwan narkakkiyar dalma!

Mu duba yadda ya damu da ita a wancan lokacin, amma yau ba damuwarsa ne ta ji ciwo ko ba ta ji ba, shi dai kawai laifin da ta yi masa yake kallo.

Ya kamata maza mu rinka tuna baya, bai kamata a lokacin da matayenmu suka saba mana za mu ke yanke hukunci ba. 

-  Maimaitawa, na taba rubuta wannan rubutu a wannan shafi a ranar 14 ga watan Disambar 2010.

No comments:

Post a Comment