Tuesday, January 7, 2014

Asari Dokubo: Mahaukaci Da Gata!


Asari Dokubo

Ashafa Murnai Barkiya (Editan Jaridar RARIYA)

A lokacin da na kama hanya zan tafi yi wa mahaukacin Neja Delta, Dokibo Asari intabiyu, da dare ne, bayan na yi sallar Isha’i. Duk wani tarihi nasa na irin na irin kashe-kashen jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ‘yan sanda, tabargaza da barnata dukiyar basa da ya yi babu wanda ban sani ba. Asari ya mallaki manyan makaman da yawanci ma wasu jami’an tsaronmu ba su san yadda ake sarrafa su ba. A tattaunawar da na yi da shi, cewa ya yi shi bai ajiye makamai ba, ya dai zauna hutun karon da ya gwabza da maza ne kawai tunda dan’uwansu Jonathan aka ba mulkin kasar nan, dama abin da suke so kenan.

Ni dai na san ban ci maganin bindiga ko na gurneti ba, ballantana layar zana. Haka na yi kumumuwa na afka gidan babban gogarman dan ta’addar kasar nan muka yi doguwar tattaunawa da shi. Jiki na ya fara bari a yayin da yake ratattakar ‘yan Arewa. Ji na yi kawai ina tsima, ina kuma tunanin ta ina zai kai min naushi saboda ni dan Arewa ne? Domin irin yadda yake magana, yana kugi, yana karaji yana zagin ‘yan Arewa, ban yi zaton zan fito gidansa da raina ba, kada giwa ta taka kwado, wato kada ya ce bari ma ya fara da wannan dan tsigigin.

A yadda na fahimci Asari, to duk mai shiryawa ma ya shirya, makamansa na nan jibge, kuma mabiyansa na nan ba su tarwatse ba, tunda dama ya ce min shi bai yarda da afuwa ba, wato shirin amnesty da aka yi wata ‘yan ta’addar Neja Delta. Ranar komawa bakin daga ko ranar komawa aika-aika kawai yake jira. Mai tababar zance na ya farka daga barci, ya je ya sake karanta hirar da na yi da shi, zai tabbatar da haka.

Kada kuma a manta, Asari ya tsine wa Nijeriya, ya ce Allah ya kawo bala’in da zai tarwatsa ta. Amma irin wadannan ‘yan ta’addar ne ke mara wa shugaban kasa na yanzu baya, har yana yi mana barazanar yaki. Sai dai me, ba na ganin laifin Asari, laifin Jonathan nake gani da kuma wadanda suka kinkimo shi. Idan shugaba dai shugaba ne, kai ko da shugaban gidan giya ne, ba zai bari a cikin mashayarsa ya ji gogarman dan takife ko wani dan banzan day a sha ya yi mankas ya rika yin irin kalaman da Asari yake yi ba don goyon bayan shugabancinsa.

Ya ce idan Jonathan bai ci zade ba za a yi yaki a kasar nan? To ni dai ban san yadda Jonathan ke nufi da makomar kasar nan ba, da har yake barin ‘yan’uwansa na yaba bakak-en maganganu dangane da makomar kasar nan. Ko bai san ana yi ba ne? Saboda ganganci har wasu gurzagullan karti ke tsayawa a kan titunanmu da sunan tsaro, ga bindigogi an damka wa kowa. Su kwana bakwai suna bincikar motoci ba su samu ko basilla a cikin kayan wani ba. An yi asarar kudin tsaro kawai! Amma abin haushi ga su Asari can suna kada gangar gangamin tarwatsa kasar nan an kyale su sai iskanci suke yi a Abuja.

Cikin shekarun nan biyu duk wani dan Arewa ya san cewa Abuja ta koma Abu-baka! Saboda wasu bakaken halittu masu bakaken kaya sanye da b akaken huluna sun cika garin, ko kuma sun yi wa ko’ina a cikin birnin kaka-gida. A Abuja duk ma’aikatar da ka shiga da rawani, to ka tabbata a ranar ka raba hanya da sa’a. Amma idan kana so a dauke ka da mutunci, to ka sa bakar hula ka shiga wata ma’aikata ko da kuwa dan Arewa ne ke shugabantar ta.

Muna da ministan tsaro, Sufeto Janar na ‘yan sanda da kuma shugaban SSS. Ga mahaukaci da sanda ya kutsa cikin kasuwa amma sun sa masa ido sai dukan mutane yake yi. Amma da wani dan jarida ne ya yi biji-biji da Jonathan, to shikenan ya yi laifi. Da gwamnoninmu mu suke wakilta, ya kamata a ce sun yi taron gaggawa sun tsine wa Asari Dokibo, tunda yana neman kasar nan da bakar fitina. Sannan su gaggauta umartar shugaban kasa ya nisanta kansa da shi. Su ma wakilanmu na majalisar dattawa da na tarayya duk su yi haka. Sannan su tilasta wa Sufeto Janar na ‘yan sanda ya gaggauta kama Asari Dokubo. Ammma ya muka iya da ranmu? Na ji majalisa ta bada umarni.

Tun da gwangwanaye gare mu ba gwamnoni ba. Kuma ’yan zaman majalisa gare mu ba ‘yan majalisa ba? Idan ba a kama shi ba babu abin da za su yi. Shi kansa Sufeto Janar din idan har sufeton da ya sufetantu da sufetacciyar akidar aikin dan sanda ne, ya kamata a ce ya kama Asari Dokubo.

To ai dama Bahaushe ya ce idan ka ga mahaukaci da makami, yana yadda ya ga dama, to yana da gata shi ya sa ba ya tabuwa, kuma ba ya kamuwa. Maganar nan fa gaskiya ce, tunda kuwa an ce rikon mahaukaci sai sarki. Shin Asari Dokubo mahaukacin wane ne?

An buga wannan rubutu a shafin Gyaran Ganga a jaridar RARIYA, kuma rubutun hakkin mallakar jaridar ne.

No comments:

Post a Comment