Tuesday, January 7, 2014

Ko Wa Ya Kaiwa Mahaifin Gwamnan Kano Hari?


Gwamna Rabiu Kwankwaso
Wani labari da jaridar RARIYA ta labarto ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun kai wa mahaifin mai girma gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, Alhaji Musa Kwankwaso, farmaki, a daren jiya, sai dai Allah bai ba wa wannan ‘yan ta’adda ikon kashe mahaifin gwamnan ba, sai dai sun harbi mutane da dama a hanyarsu da kai masa harin.

Alhaji Musa Kwankwaso, shi ne hakimin karamar hukumar Madobi, kuma yana rike da sarauta mai daraja ta ‘Maji Dadin Kano’ a fadar mai martaba Sarkin Kano.

Shin ko wane gungun ‘yan ta’addane suka kai wa Maji Dadin Kanon wannan farmaki?

Allah ya kara kare mu, ya kara kawo mana zaman lafiya a jiharmu Kano da kasarmu Nigeria baki daya.

3 comments: