Thursday, September 12, 2013

Jaridar Rariya Ta Gobe Juma'a

Jaridar RARIYA ta gobe Juma’a ta zo muku da babban labari kan yadda GUGUWAR CANJI ta taso a siyasar kasar nan, guguwar dai idan ba a zauna an yi karatun ta nutsu ba, za ta iya tashi da hular malam Bahaushe, Bayerabe, inyamuri kai har da malafar kananan kabilu ma da alamu ba za ta gyale ba.

Tun a yanzu guguwar tana neman tarwatsa gamayyar ‘yayan jam’iyyar PDP saboda kuwa a ...halin da ake ciki jihohi 17 sun bude ofisoshin sabuwar jam’iyyar. Ga kuma wasu gwamnoni sun bada wa idonsu toka suna jiran ko ta kwana, haka kuma saura kadan guguwar ta kwance zanin Namadi Sambo.

A yunkurin tsira daga wannan guguwar shugaba Goodluck Jonathan ya yunkura ya sauke ministocinsa har guda 9 da yake ganin ba za su iya tabuka masa komai ba wurin tserar da shi daga GUGUWAR CANJIN da take nuna alamun za ta iya tafiya da kujerarsa.

Domin jin ta inda wannan guguwa ta bullo da irin barnar da take neman yi wa wasu gaggan ‘yan siyasa da masu rike da mukaman gwamnati, sai a garzaya a nemi #RARIYA a gobe a wuraren saida jaridu mafi kusa da ku.

Kar ku bari a baku labara.


Ku nemi Rariya a Facebook don samun labarai da dumi-duminsa.

No comments:

Post a Comment