Saturday, September 14, 2013

NAZARI: Labaran Maku Ya Zama Ministan Tsaro

Hausawa na cewa "Taura biyu ba ta taunuwa a baki daya" amma a kasar nan musamman a cikin gwamnatin Shugaba Goodluck ba haka abin yake ba. A irin wannan lokaci da kasa ke fama da tabarbarewar tsaro, da kuma ta'addanci ke kara yawaita, sai ga sanarwa daga gwamnati, ministan yada labarai, Labaran Maku ya zama ministan tsaro na riko, ba kuma tare da ya ajiye mukaminsa, wato dai yanzu ya zama ministan yada labarai da kuma ministan tsaro.

An ya kuwa hakan na nufin gwamnatin tarayyar kasar nan ta shirya kawo karshen tabarbarewar tsaron ta take kukan ana fama da ita? Shin ko ta manta da irin barazanar tsaron da jami'an tsaro da jama'ar kasar nan ke fuskanta? Ko ta manta da sace - sacen da ya addabi mutane, bayan satar kudi, ga satar albarkatun kasa (man fetur) kai uwa uba ga satar mutane da take neman zama ruwan dare game ko'ina. Idan duk tana sane da hakan to ya kamata ta sake tunani.

Nauyin ministan tsaro ba karamin nauyi ba ne, hasalima ba a fiye bada mukamin ga kowa ba, sai wanda ya san mene ne tsaron kasa, wato dai wanda ya dade yana aiki a bangaren tsaron, kuma yayi nasara a aikin nasa. Idan har da gaske ake yi ana so a kawo karshen lalacewar tsaron kasar nan ya kamata gwamnati ta sake tunani.

Sai dai kuma shi sabon ministan tsaron, Labaran Maku a lokacin da yake karbar aiki daga hannun karamin ministan tsaron da siyasar sauke ministoci ta hada da shi, Erelu Olusola Obada, ya tabbatar da cewa zai kawo gyara da samar da ci gaba a hukumar tsaron, wanda a cewar sa shi kansa shugaban kasa Goodluck Jonathan ya san zai iya shi yasa ya dakko shi ya kara masa da wannan aiki bayan wanda yake kansa, sannan ya yi alkawarin zai yi iya kokarinsa don ya ga bai bawa shugaban kunya ba.

Anan idan aka yi la'akari da jawabin Maku na kama aiki, sai a yi masa fatan alheri, da addu'ar Allah ya kawo wa tsaron kasar nan dauki ta inda ma ba mu yi zato ba.


Daga jaridar Rariya

No comments:

Post a Comment