Saturday, August 17, 2013

Takarar Buhari Da Lissafin Siyasar 2015

Jaridar Daily Trust ta ranar 12 ga watan nan na Agusta ta ruwaito labarin tabbacin da Janar Muhammadu Buhari ya bayar game da sha’anin takararsa. Tsohon shugaban kasar ya ce lalle zai sake tsayawa takara a shekarar 2015. Idan har da gaske Janar ya yi wannan magana, ke nan wannan takarar tasa za ta zama ita ce ta hudu a kirga.

Wannan tabbaci da Buhari ya bayar a jaridar shi ne zai iya kawo karshen shakkun da manazarta suke tayarwa a kan batun takarar tasa, kazalika za a iya cewa, tabbacin zai alkibalantar da siyasar zaben shugaban kasa a 2015 na kasar baki daya zuwa ga fuskar da za ta zama mai sauki da dadi a nazari da bi-biya. Domin ko ba komai dai, sake fitowar Buhari ga takarar shugabancin kasar nan zai sanya jam’iyya mai ci wato PDP ta shiga taitayinta. Saboda adawar da takararsa ke bayarwa, bisa ga al’ada, adawa ce mai gajiyar da duk jam’iyyar da ke ci. Hakan ne kuma, domin tun ba a je ko’ina ba, tuni cikin wasu ’ya’yan PDP ya duri ruwa har ma sun fara daidaita sahunsu, musamman kan rikice-rikicen cikin gida da suka kunno kai cikin jam’iyyar, sun fara yayyafa musu ruwa da kansu. To sai dai kuma yayin da PDP ke kokarin gyatta gininta da ke neman rushewa saboda ganin yadda ginin jam’iyyar APC ke ginuwa cikin hanzari, musamman saboda tabbacin sake takarar nan ta Buhari, akwai wasu tambayoyi da ke tilasta kansu a kan ita dai wannan takara tasa.

Wannan kuma domin kasancewar takarar a kashin kanta tamkar wani tubalin gini ne mai karfi a harsashin ginin da APC ke yi.

Tambaya ta farko ita ce: shin Buhari zai iya cin zabe har ma ya zama shugaban kasa idan aka yi la’akari da nukurar da dattawan kasar nan suke nuna masa, musamman na Arewa wadanda a baya can suka yi ta nuku-nuku a kan sauran takarar da ya yi kafin wannan?

Tambaya ta biyu ita ce: shin wannan hadaka da aka yi da Yarbawa (CPC da ACN), za ta kai Buhari ga tudun mun-tsira game da sha’anin takararsa a 2015 ko kuwa abin nan da wasu Hausawa ke kira da ‘munafuncin’ Yarbawa zai taka rawa a zaben shekarar har Buhari ya gaza kai labari?

Tambaya ta uku ita ce: wane tabbaci Buhari yake da shi game da gaskiyar niyyar jagororin ANPP irin su Ibrahim Shekarau (wanda ake gani bai yi zaman dadi da Buharin a jam’iyyar ANPP ba) da Ali Modu Sharif (wanda ake zargi dan leken asirin jam’iyyar PDP ne a cikin ANPP) da Attahiru Dalhatu Bafarawa (wanda ake gani jin isarsa ya sa yana kallon kansa kamar yana gaba da Buharin a komai) tare da Ahmad Sani Yarima (wanda ake gani iskar son dauwama a mulki za ta iya kada shi zuwa ga wata jam’iyyar a kowane lokaci)? Wane shiri Buhari ya yi idan aka wayi gari wadannan zakakuran ’yan siyasa suka sake juya masa baya kuma suka yake shi daga cikin gida?

Tambaya ta hudu ita ce: Shin da gaske dabi’ar da ake kallon Inyamuri da ita ta sayar da komai nasa don ya samu kudi, ba za ta yi tasiri a tunanin Gwamna Rochas Okorocha ba yayin da wasu ’yan adawan ciki ko na waje suka tunkare shi da rashawa? Idan har hakan ya faru, to wane shiri Buhari ya yi na takara ba tare da la’akari da yankin Kudu maso- gabas ba? Yayin da ire-iren wadannan tambayoyi ke tilasta kansu a sha’anin takarar Buhari a karo na hudu hakazalika su kansu su Buharin, a yadda wannan marubuci yake kyautata zato, ba za su rasa tanadin abin da zukatansu ke raya musu cewa gamsassun amsoshi ba ne ga waxannan tambayoyi. Sai dai kuma abin la’akari a cikin zubin wannan lissafi na siyasa, shi ne sunan Janar TY Danjuma da yake ta karakaina a farfajiyar siyasar Arewa a ’yan kwanakin nan. Wannan karakaina ba zai zama kawai a kan hatsari ba, da walakin…Idan har masoya Buhari ba su yi dace ba, dattawan Arewa za su iya maida karfinsu ga TY Danjuma da bukatar ya fito takara kamar yadda tuni wasu manazarta suka yi ittifaki a nazarin hasashe. Wannan kuma zai yiwu ne idan har Shugaba Jonathan ya tilasta wa ’yan PDP sake tsayawa takara shi ma. Saboda dattawan za su fi samun natsuwa da mutum irin TY Danjuma ya mulke su maimakon a ce Buhari ne ya mulke su. Dalilan hakan kuma ba a bayan labule suke ba, ga su nan a bayyane: Na farko, game da PDP, idan har ya kasance kamar yadda ake zato, jam’iyyar ta ci nasarar magance dukkan kananan matsalolinta na cikin gida a taron kasa da za ta yi nan gaba, to kwadayi zai iya sa ta sanya Jonathan a gaba a takarar 2015. Wannan abu da za ta yi, hasashe na nuna cewa shi ne zai iya kawo karshen mulkinta a Nijeriya. Saboda takarar Jonathan, takara ce da ba za ta yi wa ilahirin dattawan kasar nan dadi a rai ba. Domin za a tauye buqatunsu da dama. Yayin da kuwa suka tabbatar za a iya tauye bukatunsu, to fa sai inda karfinsu ya kare.

Don haka takarar Jonathan a cikin PDP shi ne babban matsalar jam’iyyar. Na biyu, idan kuma har dattawan nan suka juya wa PDP baya saboda takarar Jonathan, to za su iya neman madogara a jam’iyyar APC saboda ita ce tumbatsarta ta tsallaka har ga sauran yankunan kasar kamar PDP, don haka ita ce za ta iya cin zabe.
A sannan ne kuma takarar Buhari za ta ci karo da mushkila mai girman taswira. Saboda dattawan ba za su so su gatanta wanda suke wa zaton zai daddaure su yayin da ya zama shugaban kasa ba. Ko kuma ba za su so su mara wa wanda suke jin yana nuna musu cewa ya fi su tsarki baya ba. A wannan lokaci ne kuma wadancan tambayoyi na baya za su zama ababen la’akari da idon basira a kan tilas. Domin dattawan za su iya sanya wanda ake gani shi ne jagoran Yarbawa a wannan hadaka da Buhari, wato Bola Ahmad Tinubu a gaba da magiya da rokon arzikin kada ya bari Buhari ya ci zaben furamare a APC.

Idan har hakan ta auku, marubucin nan ba ya ganin zuciyar dan siyasa irin Tinubu za ta iya bijire wa magiyar wadannan dattawa wadanda zai yi wuya a farkon tasowarsa (Tinubu) bai yi burin a sanshi tare da su ba. Kazalika a cikin jagororin nan na ANPP da aka ambata a baya, babu wanda shi ma ba zai karkata ga bangaren wancan magiya da rokon arziki na manyan dattawan da ko dai wasun su sun taba zama iyayen gidansu a da, ko kuma suna kallon takarar Buhari da irin wancan ido da dattawan suke kallo ba su ma. Haka lissafin yake ga hatta Gwamna Rochas Okorocha, wanda dama wasu majibintar Buhari na baya, sun taba zarginsa da cefanar da takararsa ta shugaban kasa tare da kokarin tayar da rigima a zaben furamare na jam’iyyar ANPP da aka yi da tsakar dare a dandalin Eagle Square a shekarar 2003. Hanyar kuma da za ta yi saurin karbuwa ga irin wannan juya baya ga Buhari a wannan yanayi, ita ce kutso da Janar TY Danjuma cikin farfajiyar siyasa.

Na farko saboda TY Danjuma yana da darajar zama tsohon janar na soja kamar Buhari. Na biyu saboda shi ma ana ganin yana da kamanta gaskiya kamar Buhari. Na uku saboda shi kirista ne, ana ganin zai fi karbuwa ga kiristocin kasar nan fiye da Buhari wanda har yanzu wasu kiristocin ke yi wa kallon mai tsaurin ra’ayin addini saboda kamfen da aka yi musu. Na hudu, wanda shi ne uwa-uba, saboda dattawan da mabiyansu a siyasa, kai har ma da masu juya al’amuran siyasar duniya da ke ketare, za su fi natsuwa da TY Danjuma wanda suke gani a matsayin nasu na kashin kansu ba bare ba kamar Buhari, wanda ba sa iya hasashen abin da zai yi idan ya zama shugaban kasa.

Kila mai bin wannan marubuci da karatu ya ce, to wai duk me ake nufi da wannan tsattsauran lissafi haka da bai da wata bushara ga talakan da ke son Buhari a karshensa? Wannan shi ne abin da ya kai zancen ga ra’ayin alkiblar nan. A ra’ayin alkiblata, a yanzu ne Janar Muhammadu Buhari yake da damar zama shugaban kasar Nijeriya fiye da kowane lokaci. Amma fa sai idan har shi da kansa ya gane dabarun da zai bi don wannan haka da ya jima yana hakilon yi ta cimma ruwa, in ba haka ba kuwa, takararsa ba za ta iya zama irin ta Abraham Lincoln na Amurka ba.

A bini bashin wadannan dabaru a rubutu mai zuwa idan har Mahaliccinmu (SWA) ya kaimu da rai da lafiya.

Daga jaridar Leadership Hausa

No comments:

Post a Comment