Thursday, August 15, 2013

Labarin Wani Mahaukaci Mai Hikima

Wasu mutane ne ke cikin tafiya a cikin motarsu a tsakiyar daji sai suka ji tayar motar ta gaba tana rawa. Sai suka tsaya suka duba sai suka ga ashe notocin dake daure da taya daya ta gaba notoci uku sun kwance sun fadi saura noti daya kawai ke rike da tayar shi yasa take ta rawa zata fita.

Suna ta shawarwarin abin yi don tsakiyar daji ne ba gari a kusa kuma ababen hawa basa wucewa sannan waya ba zata yi rana a wajen ba don su baki ne masu wucewa. Can sai ga wani mahaukaci zai wuce sai ya kalle su ya kalli tayar data kwance sai ya kwashe da dariya har yana tuntsurawa kasa yana cewa "aradu in nine sai in dauko daya can daya can kuma daya can sai in har hada su in daure shegiya dasu, habawa sai tafiya aradu hahaha... wani aiki sai ni, su kuwa ba za su iya ba" *sai ya kara tuntsurewa da dariya*

Duk basu kula da zancen mahaukacin nan ba sai mutum daya ne daga cikin su ya mayar da hankali yake ta sauraren bankauran mahaukacin nan, sai ya natsu da kyau yaga akwai hikima cikin zancen mahaukacin nan sai shima ya fashe da dariya.

Da sauran abokan suka waigo suga me yasa shi dariya sai yace:
Ai kawai zancen mahaukacin nan zamu bi ma'ana mu kwankwanto notuna daya-daya a sauran tayoyin uku sai mu daurawa na hudun data kwance kawai muyi tafiyarmu lafiya lau ba matsala don rashin noti daya-daya ba zai hana komai ba.

Sai sauran duk suka ce gaskiyarsa amma ya akayi ya tuno wannan dabarar haka su basu tuno ba? Sai ya nuna mahaukacin nan yace kun ga mai hankalin da ya fahimtar damu abin da bamu sani ba.

Duk sai dukkansu kowa ya cika da mamaki.

•Wannan labarin ya nuna cewa Allah ne yake sanya wa mutum ilhama da hikima ba wai hankalinsa ko dabararsa ba, saboda su da suke da hankalin Allah bai nufe su da yin tunanin da mahaukacin yayi ba.

17 comments:

  1. Enter your comment...dakyau abunn yayi armashi pa

    ReplyDelete
  2. Gaskiya ni mutum ne mai matukar son labaran nishadi: Ina son haka, hakan ya min, akafta

    ReplyDelete
  3. Gaskiya nima na cire wonda ohhhh sorry hula

    ReplyDelete
  4. Enter your comment...gaskiya kam tayi

    ReplyDelete
  5. It very cool game. So much better than the mixed number calculator game that I have played before.

    ReplyDelete
  6. hmmmm gaskiya ne wannan al amarin haka yake Allah yasa mudace lavarin yavada kala sosai Gdy ta musan man ga shugaba Allah yakara hasken ilimi

    ReplyDelete
  7. Toyaya akayi yafahimcesu yakuma.fahumci matsalarsu??
    Koyaji abunda suke fadine??

    ReplyDelete