Thursday, August 15, 2013

Tsakure Daga Littafin: "KOGIN BARKWANCI" - Bashir Yahuza Malumfashi

Ya ku 'yan uwa da abokan arziki da masoya, ina neman addu'arku, a yayin da nake gabatar maku da kad'an daga gabatarwar sabon littafin da a yanzu haka nake aiki a kansa. Sunan littafin dai: "Kogin Barkwanci!" Yana d'auke da dad'ad'an labaran barkwanci har guda 200, wad'anda suka shafi tsokana tsakanin Kanawa da Zage-Zagi, Katsinawa da Nufawa da Gobirawa da Had'ejawa, tsakanin Bare-Bari da Fulani da sauransu. Kafin in k'ark'are aikinsa, ga tsakure:

Alk’alami Ya Fi Takobi, shi ne taken shirin da marubuci, Ado Ahmad Gidan Dabino yake gabatarwa a Gidan Rediyon Freedom da ke Kano. Kamar yadda ya saba, a sabon shirinsa na wannan makon, ya bijiro da wata gagarumar sanarwa, wacce ke wa masu sauraron shirin nasa albishir mai kima, musamman dangane da ingantaccen shirin da Gidauniyar Bukar Usman ke yi, na gabatar da gasar nishad’antarwa mai taken ‘Kogin Barkwanci.’

“Jama’a masu sauraro, yau kuma d’auke muke da wata tsaraba mai muhimmanci, sabuwa ful daga Gidauniyar Bukar Usman.” Inji Ado, yana magana cikin zazzak’ar murya, tare da jan hankali.

“Ina al’ummar Fulani, abokan wargin Bare-bari? Wannan shiri yana tare da ku. Ku ma Bare-barin, kada ku bari a ba ku labari, shirin naku ne; balle ma d’an uwanku ne ya yanke wa shirin cibi, kasancewarsa d’an k’abilar Bura daga Biu, Jihar Adamawa.” Daidai nan sai muryarsa ta kau, aka zizaro wak’ar Dokta Bukar, wacce ‘Dank’wairon Biu ya rera masa, mai taken: ‘Jarumi.’

Ado ya ci gaba da sanarwarsa: “Ina Katsinawa? Ina Gobirawa? Ina Nufawa? Ku karkad’e kunnuwanku, ga bikin zuwa ya samu; domin kuwa shirin ‘Kogin Barkwanci’ naku ne, tare da ku za a fara kuma tare da ku za a k’ark’are shi.”

Gidan Dabino bai gushe ba, sai da ya cinye tsawon minti talatin na filinsa, yana gabatar da wannan sabon shiri da Gidauniyar Bukar Usman za ta gabatar.

A tak’aice dai Ado ya sanar da al’umma yadda Gidauniyar ta d’auki nauyin farfad’o da nishad’in gargajiya, yadda zai dace da zamani. Gasa ce aka tanada tsakanin k’abilun Najeriya, musamman Katsinawa da Gobirawa da Nufawa da Bare-Bari da Fulani da Kanawa da Zage-zagi.

A gasar, an tanadi alk’alai, wad’anda za su rik’a raba wa masu barkwancin maki, a duk lokacin da suka gabatar da labarinsu. Daga k’arshe za a fitar da wad’anda suka yi nasara, wato wanda ya d’auki na d’aya da na biyu da kuma na uku.

Kamar yadda Ado ya gabatar, alk’alan sun had’a da shahararren malamin nan na Adabin Hausa, Farfesa Ibrahim Malumfashi da Farfesa Abdallah Uba Adamu da kuma shahararriyar ’yar wasan fim d’in Hausa, Saratu Gid’ad’o (Daso) da Kabir Assada Sakkwato da Mahmoon Baba Ahmad.

Kamar yadda aka tsara, za a gudanar da gasar ne tsawon wata d’aya, a zauren taro na Dandalin Gamji, Kaduna. A kullum da maraice, bayan mutum ya sayi tikiti, zai shiga zauren ya zauna kan ingantattar kujera, sannan ya kalli shirin, tare da kallon wasannin gargajiya na wak’e-wak’e da raye-raye.

A wannan littafi na ‘Kogin Barkwanci,’ za ku karanta yadda wannan gagarumar gasa ta kaya, za ku ga wanda zai yi nasara cikin taurarin da suka fafata. Taurarin kuwa sun kasance gwanayen barkwanci na wannan zamani. Kafin ku ga irin aikinsu, ga jerin sunayensu:

1 - Tantak’washi: Bakatsine, wanda ya k’ware wajen iya barkwanci. Ya haddace labarun barkwanci masu yawa, musamman wad’anda suka shafi Gobirawa da Nufawa da Had’ejawa. Ya samu damar shiga gasar nan ne, bayan ya doke ’yan takara guda biyu a jiharsu ta Katsina. ’Yan takarar da ya doke kuwa, sun fito ne daga shiyyoyin Katsina da Daura. A matsayinsa na mai wakiltar shiyyar da ya fito, wato shiyyar Funtuwa, shi ya yi nasarar zama tauraron Jihar Katsina, wanda kuma zai wakilce ta a babbar gasar barkwanci da Gidauniyar Bukar Usman ta d’auki nauyin gabatarwa.

2 - Tantabara: Ta kasance Banufa, wacce ta gwanance wajen iya tsokanar Katsinawa. Da ita za a fafata a wannan gagarumar gasa ta Kogin Barkwanci, wanda Gidauniyar Bukar usman ta d’auki nauyin gabatarwa. Tantabara, ita ce wakiliyar Jihar Neja, a wannan gagarumar gasa.

3 - Gizago: Gizago ba ka da sabo, masassak’i ka tsare annunka. Wannan bawan Allah Babarbare ne, wanda ya fito daga Maiduguri, amma Allah Ya hore masa iya wasan kwaikwayo. Kafin ya samu nasarar shiga wannan gasa, sai da aka tabbatar ya gwanance wajen sanin sirrin Fulani. Da yake yana auren Bazazzagiya, shi ya sanya wani lokaci yake alak’anta kansa da Zariya. Dalili ke nan ma ya sanya ya tattara labarun barkwanci na tsokanar Kanawa. A wannan gasa ma, ya yi alk’awarin jefo su kad’an-kad’an. Shi ne wakilin Jihar Borno a wannan gasa.

4 - Dangarama: Mace ce ita mai iya raha. Ta kasance Bagobira, wacce ta fito daga Sabon Birni a Jihar Sakkwato. A jiharsu, ta doke ’yan wasan barkwanci da dama, kafin ta tsallake shingen shiga wannan gasa ta ‘Kogin Barkwanci.’

5 - Jauro: Shi ne mutum na biyar da ya samu shiga cikin wannan gasa. Bafulatani ne shi mai kaifin wayau da iya sarrafa magana. A tsawon rayuwarsa, ya-shiga-ya-fita, ya tattara labaran tsokana da barkwanci masu yawa, waxanda suka shafi Bare-Bari. Da yake kuma shi Bakano ne, ya had’a da lak’antar labarun tsokanar Zage-Zagi. Babu shakka za a yi gumu da shi a wannan gasa ta ‘Kogin Barkwanci.’ Ya fafata da abokan karawarsa a matakin jiha, inda ya zama zakara, ya d’auki kambin kare Jihar Kano a wannan gagarumar gasa.

Masu iya magana sun ce, ba a san maci tuwo ba sai miya ta k’are. Mu shiga zauren mu ga yadda za ta kaya, a wannan gagarumar gasa ta ‘Kogin Barkwanci.’

No comments:

Post a Comment