Da tsakar ranar Talatar nan ne wasu yan fashi da makami suka kai farmaki kasuwar yan chanji dake Wapa a birnin Kano. Yan fashin su kimanin 9 da suke akan babura da kuma mota kirar Golf sun ringa harbi babu kakkautawa a kasuwar daga bisani suka kutsa cikin wani shago suka yi awon gaba da miliyoyin kudi da har yanzu ba a tantance yawansu ba.
Shugaban kasuwar Wapa Alhaji Auwal Umar Nagari ya bayyana takaici bisa rashin isowar jami'an tsaro akan lokaci da kuma yadda yan fashin suka bar wasu kwanson harsasai mai dauke da tambarin 'yan sanda lamarin da yasa suke zargin kodai akwai lauje cikin nadi. yawan fashi a kasuwannin jihar Kano dai wani babban al amari ne da a yanzu ke nema zama ruwan duk da yawan jami'an tsaro dake baje a hanyoyin jihar.
Freedom Radio FM, Kano
No comments:
Post a Comment