To fa. . . . Bari dai na fara da mabudin kunne kafin na zarce inda na nufa “Aure rufin asirin Musulmai” na san daga jin wannan karin waka da yawa daga cikinmu za su fuskanci inda na nufa, hmmm! Kar dai kuce na cika ku da surutu bari na tafi kai tsaye:
Muhammad Gali Abubakar ne da amaryarsa Asma'u Lawan Hamza (Ummi) cike da farin ciki marar misaltuwa suke gayyatarku domin kuyi tururuwa da dafifi zuwa shaida daurin aurensu.
An tsara za a gudanar da bikin kamar haka:
Rana: Juma'a 2/11/2012 = 17/12/1433
Wurin Haduwa: Za a hadu a Goron Dutse Bayan Wreca Kano, Gidan Gwani Malam Lawan Gaya
Wurin Daurin Aure: Sheka Baranda Unguwar Kudu Kano, Gidan Malam Lawan Dan Gaya
Ango da amarya na cike da fatan dukkanku zaku dungumo ku shaida wannan daurin aure na su tare da taya su adduar fatan alheri.
Dandali ya samu wannan sanarwa ne daga Lawiza da Hauwa 'yayan Murtala Jar Kasa, Zuru, Jihar Kebbi.
No comments:
Post a Comment