Friday, July 27, 2012

Duniya Ina Za Ki Damu?


Wannan hoton wani matashi ne da jami'an tsaro suka cafke a Abuja dauke da kan yaron wani makwabcinsa dan shekara bakwai.

Matashin mai suna Joan Yakubu dan shekara 25, jami'an tsaron sun yi nasarar cafke shi ne a AYA, Asokoro tare da rakiyar wani abokinsa mai suna Ishaya Dukulung mai shekaru 30.

Kamar yadda matashin ya bayyana, ya ce abokinsa ne ya shawarce shi da su nemo kan mutum don su saida shi ga wani mutum a Abuja.

Rahoto Daga Jaridar Rariya

Barka Da Shan Ruwa!!!

Ranar Ba Ta Karya - Yau Za'a Fara Gasar Olympics a Birnin London


Hankulan mutanen duniya, ya karkata zuwa birnin London a yau, sakamakon kammaluwar shirin fara gasar wasannin Olympics a yau din, akalla mutane sama da biliyan hudu ne za su kalli wannan biki na bude gasar a sassan duniya daban daban

Firaministan Burtaniya, David Cameron ya bayyana cewa kasarsa ta shirya tsaf domin daukan bakuncin gasa mafi girma a duniya, gabannin bikin bude gasar wasannin Olympics da za a yi nan gaba a yau.

Mr. Cameron ya ce "Gasar wani abun alfahari ne ga Burtaniya, kuma ya kamata jama'ar kasar su karbe ta hannu biyu-biyu".

Tun farko dai an kada karaurrawa a sassa daban - daban na kasar ta Burtaniya, kuma an yi ta zagayawa da wutar gasar wasannin ta Olympics a kan kogin Thames dake tsakiyar birnin na London a cikin wani jirgin ruwan Gidan Sarauta da aka kawata shi da adon Gwal.

'Yan wasa sama da 15,000 za su fafata a wasanni sama da 300 a gasar ta Olympics.

Wednesday, July 25, 2012

Gajeren Sako Ga Makaranta Wannan Dandali

Aminci A Gare Ku!!!

Ina taya mu murnar shigowarmu watan Ramadan mai Alfarma, Allah ya gafarta mana, ya biya mana bukatun mu alfarmar wannan wata, ya sa muna daga cikin wadanda za a 'yanta a cikin wannan wata.

Nayi wannan rubutu ne a yanzu sakamokon kirana da wasu bayin Allah da suke karanta abubuwan da nake rubutawa a wannan Dandali, a waya suke tambaya ta ko lafiya kwana biyu ban cika yin rubutu ba kamar yadda na saba yi a da?

Na san wasu za su iya sanin dalilin yin hakan, ba komai bane kuwa sai don shigowar wannan wata, saboda akwai bukatar idan watan ya shigo duk wani abu da mutum yake yi ya dakatar da shi ya kusanci Allah, yayi ta rokon gafara da rahama, saboda kuwa idan wannan dama ta wuce sai kuma Allah ya kaimu wata shekarar, wanda kuma hakan ne babu tabbacin ko zamu sake ganin wani Ramadan din na gaba.

Ya Allah ya amshi ibadunmu.

Sunday, July 15, 2012

Hadin Kai Tushen Nasara: ACN/CPC Sun Yi Nasara a Jihar Edo



Gaskiyar Turawa da suka dade suna fada da nanatawa a harshensu na Turanci ko nace na Nasara cewa "United We Stand" Domin kuwa na fahimci hadin kan shi ne tushen nasara, ba komai ya sa na fahimci hakan ba sai don yadda naga cewa duk lokacin da wasu gungun mutane ko daidaiku suka hada hannun domin cimma wata manufa to tabbas ko shakka babu sai naga sun yi nasara, ba tare da shan wasu wahalhalu ko haduwa da wani kalubale ba, irin haka ta sha faruwa shekaru daruruwa da suka shude, kuma wani abin mamaki har a yanzu wannan lokaci hakan na ci gaba da faruwa, kuma faruwar hakan a wannan zamani shi ne yake tabbatar mana da lallai hakan zai faru anan gaba, faruwar hakan a gaba kuma manuni ne na ci gaba faruwar haka har abada, wato har karshen wannan zamani kenan.

Na fara da wannan batu ne na hadin kai saboda yadda naji zaben jihar Edo ya wakana a jiya Asabar, wanda ya bawa Adams Aliyu Oshiohomle nasara, karkashin jam'iyyarsa ta ACN tare da hadin gwiwar jami'yyar CPC, da gagarumin rinjaye akan jam'iyyun PDP da ANPP da suka fafata a zaben.

Wannan nasara da Adams Oshiomhole ya samu wani darasi ne da dukkan 'yan Nijeriya masu sun canji na alheri da ci gaban kasar da al'ummarta. Darasin da ke cin wannan nasara ta Oshiomhole shi ne hadin kan da jam'iyyar CPC da ACN suka yi har suka samu nasara.

Sai naga ashe da wadannan jam'iyyu na CPC da ACN da wasu sauran jam'iyyun da suke ikirarin suna yi ne don talakawa to da ashe a lokacin zaben 2015 da mun samu nasara, saboda Hadin Kan shi ne Tushen Nasara.

Monday, July 9, 2012

Shafin Sada Zumunta Na Facebook

Sunan Facebook ba boyayye bane ga matasan wannan zamani maza da mata, musamman masu mu’amala da fasahar yanar gizo. Domin kuwa koda mutum baya amfani da shafin ba zai kasa jin masu mu’amala da shi suna zancensa ba.

Duk da dai ba duk aka taru aka zama daya ba wato dai ba za’a rasa ‘yan tsirarun mutanen da basu san wannan shafi na Facebook ba, ko kuma idan sun san shi basu san wace irin mu’amala ake dashi ba, kai wasu ma suna amfani da shafin amma basu fahimce shi ba, domin kuwa idan zaka tambaye su menene amfanin Facebook, ka basu aiki ba karami ba. To idan kana daya daga cikin wanda basu san menene Facebook ba ko kuma kana daya daga cikin wadanda sun sanshi amma basu san amfaninsa ba, kai har ma da wadanda suka san shafin kuma suka san amfaninsa ku dan bani hankalinku na dan lokaci dan sanin menene Facebook, wa ya kirkire shi, don me aka kirkire shi, menene amfaninsa da sauran batutuwa makamantan hakan.

Facebook dai dandali ne na sada zumunta kuma yana daya daga cikin miliyoyin shafukan dake kunshe a rumbun yanar gizo wato Internet. Kamar irinsu shafukan Twitter, MySpace, Google+ da sauransu, sai dai shafin na Facebook ya banbanta da shafukan dana bayyana a sama ta hanyoyi da dama. Facebook shafi ne da wani dalibi mai suna Mark Zuckerberg ya kirkire shi tare da wasu abokan karatunsa su uku Eduardo Saverin, Dustin Moskovitz da kuma Chris Hughes, a ranar 4 February 2004. A makarantar Harvard a jihar Califonia dake kasar Amurka.

Wadannan dalibai sun kirkiri shafin ne don amfani dashi a makarantarsu kawai, don haka cikin dan lokaci kankani shafin ya baibaye ilahirin wannan makaranta, saboda irin farin jinin da shafin ya samu a wurin daliban makarantar Harvard ba’a dau lokaci mai tsawo ba shafi ya tarwatsu zuwa sassan manyan makarantun kasar Amurka baki daya. Kafin kace me tuni shafin ya tsallaka zuwa kasashen Canada da England, wajen shekarar 2005 shafin ya karade gaba dayan yankin kasashen turawa da yankin Amurka ta kudu.

A ranar 26 ga watan 9 na shekarar 2006 kamfanin Facebook ya bayyana cewar kowa zai iya mallakar shafin a duk inda yake a duniya indai ya haura shekaru 13 da haihuwa. Shafin Facebook shafi ne da kowa zai iya amfani dashi cikin sassakar hanya, shafi ne da masu amfani dashi ke samun damar haduwa da mutane kala kala daga kasashen duniya daban – daban, shafin yana da kayatarwa, nishadantarwa, ilimintarwa, shagaltarwa har ma da wa’azantarwa. Shafi ne daya hada al’ummatai kala – kala mabanbanta ra’ayi, kabila, addini, yare da kuma tarbiya. Haka yasa duk irin manufar da tasa mutum amfani da shafin yake samun ‘yan uwansa.

Facebook ya bawa masu amfani dashi dama wurin baje kolen ra’ayinsu, ba tare da tsangwama ko hana ‘yancin magana ba, wannan dalilin yasa Facebook ya tserewa dukkan wani shafi na sada zumunta wato social network a turance yawan masu amfani dashi. Kamar yadda kamfanin ya shaida cewar yana da sama da mutum miliyan 750 masu amfani da shafin a kiyashin da akayi a watan bakwai na shekara ta 2011.

YADDA AKE BUDE SHAFIN FACEBOOK

Da farko mutum zai tanadi adireshin email mai amfani ko kuma lambar waya, sannan sai mutum ya zarce kai tsaye wurin da yake shigar da adireshin gidajen yanar gizo idan zai nemo bayanai (browsing) a na’ura mai kwakwalwarsa (computer) ko kuma wayarsa ta hannu (handset). Sai ya shigar da adireshin shafin na Facebook kamar haka http://www.facebook.com idan kuma a wayar hannu ne sai ya shigar kamar haka http://m.facebook.com da zarar ka shiga zaka ci karo da inda aka rubutu SIGNUP sai a latsa nan daga nan kuma za’a aiko ma da form da zaka cike don zama daya daga cikin miliyoyin dake amfani da shafi.

Bayan an kammala cike form din gami da shigarwa, anan za’a bukaci ka tabbatar da email ko lambar wayar da kayi amfani dasu naka ne, wato kamfanin na Facebook zai turo sako ta cikin abinda ka zaba wurin budewar email ko lambar waya, hade da adireshin da zaka latsa ko lambobin sirri da zaka shigar don kammala rijistar Facebook din naka, da zarar ka shigar ko ka latsa adireshin da aka turo ma shi kenan ka zama daya daga cikin masu amfani da dandalin sada zumunta na Facebook.

Bayan nan kuma sai ka shiga shafin naka don sa hotonka gami da karasa cike ‘yan bayanai da suka dangance ka misali kamar: sunan garinku, addininka, abinda kafi sha’awa, yaren da kake ji, makarantar da kayi ko kake yi ko kuma wurin da kake aiki da sauran bayanai da suka shafe ka, domin saukakawa masu son mu’amula da kai ba dole sai suna tambayarka ba.

Daga Mujallar Duniyar Computer

Bashir Ahmad
Bashirgy@yahoo.com
08032493020

Ra'ayin Aminiya: Kalubalen Dake Gaban Sambo Dasuki


Mako biyu da suka gabata ne Shugaba Goodluck Jonathan ya bayar da sanarwar sallamar Janar Andrew Owoeye Azazi daga mukamin Mai Bayar da Shawara ga Shugaban kasa kan Harkokin Tsaron kasa (NSA). Kuma ya sallami Dokta Bello Haliru Muhammad daga mukaminsa na Ministan Tsaro. Kuma a take cikin sanarwar ya bayyyana nada wani Kanar din soja mai ritaya Alhaji Sambo Dasuki a matsayin Mai Bayar da Shawara kan Harkokin Tsaro na kasa don maye gurbin Azazi; sai dai ba a fadi wanda zai maye gurbin Dokta Halliru ba. Sauye- sauyen manyan shugabannin tsaron kasa sun zo a lokacin da kasar take fama da kalubale a bangaren tsaro. Don haka Sambo Dasuki ya san irin aikin da ke gabansa.

kalubalen Boko Haram na nan, wadda a fagen siyasa ake kallonsa a matsayin babbar barazana ga dorewar kasar nan a matsayin kasa daya. Tun shekarar 2009 kungiyar ta fara adawa ga hukumomin kasar nan inda a karshe ta kai ga kaddamar da hare-haren da suke jawo hankalin manyan kasashen duniya kan yadda Najeriya ke neman zama dandalin ayyukan ’yan ta’adda. Kuma a makon jiya sai ga sashin harkokin cikin gida na Amurka ya bayyana wasu fitattun ’yan Boko Haram uku a matsayin ’yan ta’adda. Yin hakan kowa wani cikasa ne ga kasar nan da al’ummarta. Sai dai ba Boko Haram ne kawai matsalar da ke barazana ga zaman lafiya a tsakanin ’yan Najeriya ba, kuma ke kawo gibi a tsakanin hulda tsakanin Najeriya da sauran kasashe ba.

Mugun aikin nan na sata da garkuwa da mutane don a samu kudi da aka fi yi a kudancin kasar nan shi ma matsala ce da ke damun kasar nan, kuma ga alama matakan da hukumomi ke dauka sun kasa kawo karshen lamarin. Matsalar ta fi kamari a yankin Neja-Dalta, inda babban dalilin yin hakan shi ne a kwakuli kudi ko ta halin kaka. A wasu lokuta wadanda aka yi garkuwar da su kan rasa rayukansu koda an biya kudin fansar. Fashi da makami ma wata mummunar matsala ce ga harkokin tsaron kasar nan.

A ’yan kwanakin nan an rika cuda ayyukan da suka shafi keta harkokin tsaro ta hanyar fashi da makami da batun Boko Haram, a wasu lokuta akan bayar da bayanan karya kan hakikanin barazanar kungiyar a wasu jihohi musamman a Arewa. Kuma babban bangaren da mabarnata suka fi baje kolinsu shi ne bangaren satar man fetur, inda kasar nan ke tafka asara daga gagarumar satar danyen manta. Ba abin mamaki ba ne da suka mayar da hankali wajen wannan aika-aika a yankin Neja- Dalta.

Manyan kamfanonin mai ciki har da Shell sun ruwaito mummunar sace danyen man fetur da ake yi wa Najeriya. Wasu su kiyasta ana sace danyen man ganga dubu 400 a kullum. Muhimmancin kawo wadannan bayanai ita ce, duk da kasancewar jami’an tsaro a daidaikunsu da kuma a hade ta hanyar Rundunar Musamman ta Soja (STF) da ke suke aiki domin dakile wadancan barayi, satar tana ci gaba da gudana, inda barayin ke samun biliyoyin Dala a shekara, kuma akwai yiwuwar da hadin bakin jami’ai ko hukumomin tsaron. Idan aka tattaro irin wadannan matsaloli za a ga cewa Sambo Dasuki zai fuskanci matsaloli masu yawa kuma masu wahala da suka shafi tattalin arziki da siyasa ba sun takaita ga ayyukan Boko Haram na zubar da jini kadai ba ne.

Yana da kyau Dasuki ya fahimci yanayin hadakar al’ummar Najeriya da dalilan da suke kawo irin wadancan miyagun ayyuka a tsakanin jama’a, domin nemo maslahar da ta dace. Akwai matsalolin da suke da tushe daga siyasa saura kuma daga kuncin rayuwa. Mafi yawansu kuma tantagayyar ayyuka ne na miyagu. Kowanne zai bukaci magani na daban; fahimtar tushensu zai sa a samu maganin da ya dace wajen kawar da su. Wajibi kuma Dasuki ya koyi darasi daga kura-kuran Azazi, babba daga ciki dabi’ar bangaranci da ya kawo a yayin gudanar da aikinsa na Mai bayar da Shawara kan Harkokin Tsaro na kasa. A lokacinsa, tunanu da inda yake zuwa sun takaita ne ga halartar tarurruka da al’amuran da suka shafi tsaro idan wurin da ake taron yana yankin Kudu maso Kudu. Ya shuka tare da rainon tunanin cewa matsalar tsaro abu ne a tsakanin Arewa da sauran sassan kasar nan, ya daukaka matsayin Boko Haram zuwa babbar ko ma ita ce kadai barazana ga mulkin Shugaba Jonathan ta kokarin kakabata ‘ga ’yan siyasar Arewa da janar-janar masu ritaya.’

Babu wani bayani da ya nuna Azazi ya taba ziyartar wuraren da aka yi artabu a Arewa, musamman Damaturu a Jihar Yobe da Maiduguri a Jihar Borno, tunda aka fara kai hare-haren bama-bamai shekara biyu da suka gabata, domin gane wa idonsa akalla koda ya fahimci irin kalubalen da ake fuskanta. Ta hanyar zuwa wuraren a Alhamis din makon jiya, Dasuki ya nuna ya yi niyyar gano bakin zaren wannan matsalar. Kuma wajibi ne ya tafi Kudu ya duba wurare masu matsaloli ya auna abubuwa da kansa kafin ya zauna don fuskantar wannan babban kalubale ba tare da ya jefa kansa a cece-ku-ce marasa amfani ba.

Daga Jaridar Aminiya

Sunday, July 8, 2012

Seydou Keita Ya Bar Barcelona Zuwa China


Seydou Keita dan kasar Mali ya bar kungiyar Barcelona bayan shekaru hudu a kungiyar.

Dan wasan tsakiyar ya sanar da cewa ba zai cigaba da bugawa kungiyar wasa a kakar wasanni mai zuwa ba. A nata bangaren kungiyar Barcelonan ta yabawa Seydou Keita a kan gudummawar da ya baiwa kulub din a shekarun da suka gabata tare kuma da yi ma sa fatan alheri a rayuwarsa ta wasan kwallon kafa da kuma harkokinsa na rayuwa.

Keita wanda ya dauki kofuna goma sha hudu da Barca ana ganin ya na shirin komawa kasar China da wasa a kungiyar Dalian Aerbin. Keita dan shekara 32 ya koma Barcelona ne daga kungiyar Seville a 2008 kuma shi ne na farko da Pep Guardiola ya fara dauka da ya zama kocin kungiyar.

A shekara ta 2014 ne kwantiragin dan wasan zai kare da Barcelona, amma a bisa yarjejeniyar da suka kulla , ya na da damar barin kulub din idan ba a sa shi a farkon wasannin kungiyar ba a akalla rabi na kakar wasannin da ta gabata.

Guardiola ya rika sanya dan wasan a matsayin canji na tsawon lokaci, kuma Keita ya taimakawa kungiyar ta sami nasarar daukar kofunan Laliga uku da na zakarun Turai biyu da Kofin Sarki (king's cup) guda biyu da sauransu. Seydou Keita ya bugawa kungiyoyin Marseille da Lorient da Lens dukkanninsu a Faransa kafin ya tafi Spain inda ya yiwa Seville wasa na shekara daya sannan daga bisani ya koma Barcelona, wadda ita ma yanzu ya bar ta.

Yanzu dai Keita ya bi sahun Didier Drogba da Frederick Kanoute da Yakubu Aiyegbeni wajen komawa China don wasa.

Daga BBCHausa.com

Sunday, July 1, 2012

Kukan Kurciya: Tattaunawa Tsakanin Malam Habu Da Malam Jatau Game Da Kudirin Kayyade Haihuwa


Malam Habu! Malam Habu!! Dakta Habu!!! Malam Ha.......

Na'am! Na'am!! Malam Jatau, ina zuwa haka da ranan nan?

Hhmm! kafin na baka amsar tambayarka, anya lafiya kuwa ka zauna kake irin wannan tunani, nayi ta kiranka kusan sau hudu kafin ka amsa?

Malam Jatau kenan, ni fa da kai duk 'yan Nijeriya, kuma zan iya cewa ba zai zama abin tambaya ba, ga duk dan Nijeriyar da ka gani ya dukufa ya bata lokaci mai tsawo yana tunani, saboda a wani lokaci da muke ciki ko kankanin yaron da bai san menene tunani ba, za ka ganshi lokaci lokaci yayi shiru baya cewa da kowa komai, da kuwa za kayi katarin tambayarsa mai yake damunsa? Amsar da za ta fito daga bakinsa zai ce ma "Halin da Nijeriya ke ciki" to ka ga kuwa ni ma idan ka ganni cikin wannan hali bai kamata ka daga hankalinka ba.

Malam Habu kenan gwanin iya sarrafa zance, to kai yanzu menene ya saka wannan dogon tunani game da Nijeriyar?

Hhmm zahiri abubuwa ne marassa adadi suke damuna da hana zuciyata sukuni game da wannan kasa tamu, yau kwana uku kenan ina yin tattaki har gidanka, domin mu zauna mu tattauna akan wannan al'amari daya ta so, amma bana yin sa'ar samun ka, kullum sai mai dakinka ta bayyana min cewa tun sassafe ka tafi gona, kuma ba cika dawowa ba sai daf da Magriba.

Eh haka ne kam, ka san manomi da zarar ruwan damuna ya sauka ba shi da wani lokaci na kashin kansa da ya fi ya je ya ziyarci gonarsa, koda kuwa ba shi da wani muhimmin aiki a gonar. Kuma wani abin mamaki duk bacin ran dake addaba ta da zarar na isa gonata, sai kaji komai ya zama tarihi. Ku ba kun tsaya ba, wai ku 'yan boko sai zuwa Office, da yaki da biro da takardu, kun manta da cewa noman dai shi ne gatanmu. Mu bar dai wannan zance, Malam Habu menene al'amarin da kake son mu tattauna akansa?

Malam Jatau ba komai ya tayar min da hankali ba, sai wata magana da shugaban Jamhuriyar nan, wato shugaba Mai Bakar Malafa ya yi game da maganar kayyade iyali, kuma ka san fa wannan ba karamin laifi ba ne addininmu, kai har ma a addinin nasu, babban laifi ne, aikata wannan kuduri na shugaban.

To ban da abinka Malam ko nace Dakta Habu menene zai daga maka hankali akan hakan, har ka shiga irin wannan tunani?

Ba komai ya daga min hankali ba, sai gaskata maganar Mai Malafar da nayi, saboda kuwa duk abinda ya furta cewar zai yi to fa sai ya yi, ko da kuwa ana muzuru ana shaho, ma'ana idan shi kadai ya yanke hukuncin zai yi abu kaza, ko duk kasar nan za su nuna rashin goyon bayansu, bai dame shi, kai ko jama'ar kasar za su shiga wani hali, an yi irin haka da shi ba sau daya ko sau biyu ba, idan za ka tuna janye tallafin albarkatun man fetur da yayi, ko karin kudin wutar lantarki daya yi, duk 'yan kasa sun nuna kin amincewarsu, majalissun kasa ma duk biyun basu amince ba, kungiyoyin da bana gwamnati ba har zanga - zanga cin amincewa suka yi tayi amma duk a banza, yayi kunnen uwar shegu sai da ya aiwatar da kudirinsa.

Maganarka tana kan hanya domin a baya bayan nan ma, sai daya canja sunan Jami'ar Legas, duk ba tare da yardar kowa ba, to amma idan haka ne ai akwai wani alkawari daya dauka amma ya kasa cika shi.

Wannan wane alkawari ne kuwa, amma dai zai amfani talakawa ko?

Sosai ma kuwa, alkawarin da yayi na kawo karshen kungiyar Boko Haram a watan June, ga shi har mun yi bankwana da watan mun shigo watan July, kai wani abin mamaki ma, kungiyar kamar karfi ta kara a cikin watan June din, maimako a murkushe ta kamar yadda shugaban ya dauki alwashi.

Hahahahaha! Malam Jatau har ka bani wata budurwar dariya, ai daman shi shugaba Mai Malafa a yadda masu bibiyar al'amuran yau da kullum da ya shafi kasar nan suka bayyana shi baya nuna bajintarsa da matsawarsa, a komai sai inda talakawan kasar nan za su shiga wani mawuyacin hali, kuma idan kayi nazari za ka gane wannan batu haka yake babu ja ko kadan.

To a karshe menene matsayinka a game da kudirin kayyade haihuwar da kace yana yunkurin yi?

To daman ai Malam Jatau neman da nake yi ma kenan har kwana uku don naji ra'ayinka da shawararka akan kudirin?

Malam Habu da ma baka wahalar da kanka wurin jigilar nema na ba, domin kuwa ni tuni na dade da daina tofa albarkacin bakina a komai daya danganci kasar nan, saboda kuwa sai mutum ya je ya sanyawa kansa hawan jini ya tafi ba tare da lokacin tafiyar tasa ya yi ba. Kai bari ma na karashe ma maganar tun ruwan farko na baiwa Malam Mati makocina rediyo na kyauta, hankalina kacokan yanzu ya koma kan gonata, fatana Allah ya ba mu damuna mai albarka. Ga ga tafiya ta, sai an jima!

Malam Jatau! Malam Jatau!! Malam Jatau!!! Malam Jatau...... (Zancen zuci) Kai lalle Malam Jatau ya watsar da al'amuran Nijeriya sai ka ce ba shi ne kullum ba shi da zancen daya fi na Nijeriyar ba. Kai anya nima kuwa ba tattarawa zanyi na hakura da bata lokaci akan tunanin gyaruwar NIJERIYAr ba? To idan kuma muka daina yunkurin gyaruwar kasarmu, wasu za su zo daga wata kasar ne su gyara mana kasar tamu sannan su koma kasarsu? Tunda nake karanta tarihin kasashen da suka ci gaba, ban taba karanta tarihin kasar da baki suka zo suka daidaita kasar bayan ta rikice ba, ko suka kawo mata ci gaba a lokacin da take sahun koma baya. Amma dai zanyi tunani akai kafin na yanke hukuncin karshe.

To 'yan uwana Maza da Mata 'yan DANDALI sai mu taru mu taya Malam Habu yin tunaninsa na karshe kafin ya yanke hukunci ci gaba ko daina tunani akan makomar kasarsa anan gaba.

Shin ya kamata ya ci gaba da tunanin gyaruwar Nijeriyar ko ya hakura ya fuskanci harkokin da ke gabansa?