Wednesday, March 14, 2012

Wasu Saurari da Budurwa Masoyan Juna Sun Mutu a Lokaci Daya a Cikin Mota


ABIN AL'AJABI - Da sanyin safiyar ranar 14 March, 2012 ne wani abin al'ajabi ya faru a yankin unguwar Kundila dake cikin kwaryar birnin Kano. An samu gawar wasu bayin Allah su biyu, Abubakar Abba da Ummulkhair Muhammad, saurari da budurwa a cikin karamar mota kiran Peugeot 406, mallakin saurayin Abubakar Abba.

Matasan guda biyu, wadanda aka bayyana cewa dukkansu dalibai ne, dake karatu a makarantar Kwalejin Sa'adatu Abubakar Rimi, sannan dukkansu suna kan ganiyar samartakarsu da basu wuce shekaru 25 ba. Kuma sun dade suna son juna, wanda har iyayensu sun shiga maganar soyayyar tasu.

ASP Magaji Majiya, jami'in hulda da Jama'a na hukumar 'yan sandan jihar Kano, ya tabbatar da faruwar wannan al'amari, kuma yace har yanzu ba'a san menene musabbabin rasuwar matasan ba. Sannan ya bayyana cewa a halin yanzu hukumar 'yan sanda tana kan bincike.

Ya Allah ya jikan wadannan MATASA masoyan juna, ya kai rahma kabarinsu.

2 comments:

  1. To allah ya sawake ya kuma kiyaye Muna kuma yan' baya allah Yasa ya xama mana ishara a rayuwanmu don haka samari sai muyi hattara daga mmb azare

    ReplyDelete