Saturday, March 24, 2012

Abinda Ya Faru A Kasar Mali Zai Iya Faruwa A Nijeriya - Nasir El-Rufai


Tsohon ministan birnin tarayya Abuja, kuma daya daga cikin manya a jam'iyyar CPC Malam Nasir El Rufai ya bayyana cewa abinda ya faru a kasar Mali zai iya faru a kasar idan shugabanni suka ci gaba da shimfida mulki zalunci ga talakawan da suka zabe su.

El Rufai ya bayyana hakan ne a turakarsa dake shafin bayyana ra'ayi na Twitter, inda wani daga cikin mabiyansa (followers) yayi masa tambayar "Shin yana tunanin abinda ya faru a kasar Mali zai iya faruwa a kasar nan idan shugabanni basu kula da bukatun talakawan da suka zabe su ba?" nan take Malam Nasir El Rufai ya maida masa da amsar cewa yana tunanin hakan zai iya faruwa.

Idan ba'a manta ba a ranar Laraba da ta gabata ne sojoji suka yi juyin mulki a kasar ta Mali, kasar da aka shafe tsawon lokaci ana yakin basasa.

A karshe ya kamata hukumomin Nijeriya su yi duba ga irin halin da talakawan da suka zabe su, suke ciki domin kaucewa hasashen na Malam Nasir El Rufai.

Malam Nasir El Rufai a kullum yana ware lokaci domin tattaunawa da jama'a akan matsalolin da suke fuskantar kasar nan a turakarsa ta Twitter. Za ka iya biyo shi akan @elrufai domin samun damar bayyana ra'ayinka tare da shi.

No comments:

Post a Comment