Monday, March 19, 2012

Shin Idan Kai Ne Shugaban Nijeriya Taya Za Ka Tafiyar Da Mulkin Kasar Yadda Zaiyi Daidai Da Bukatun Talakawa?


Nijeriya na daya daga cikin kasashen wannan duniya, wadda Allah ya bawa matsuguni a yankin yammacin nahiyar Afrika, kasar na da al'umma mai tarun yawa sama da 160 miliyan. Allah ya horewa kasar yalwar arziki kala - kala, ciki har da man fetur mai matukar daraja.

Kamar sauran kasashe Nijeriya tayi shugabanni daban - daban wasu daga cikin su turawa ne, a lokacin mulkin mallaka daga kasar Burtaniya, wasu sojoji ne da suka kwaci mulkin da karfin bindiga, wasu kuma fararen hula ne da talakawa suka zabe su ta hanyar kada kuri'a.

Duk yawan shugabannin da kasar Nijeriya tayi amma har yanzu talakawan kasar basu yi sa'ar samun wanda ya fitar dasu daga cikin kangin wahalhalun rayuwar da mafiya yawa daga cikinsu ke fuskanta ba. Duk lokacin da aka samu canjin shugaba a kasar, sai kaga talakawa na ta murna da yiwa juna barka, sai dai kash! Tun kafin tafiya tayi nisa sai kaga ana fadin ai kwara na jiya dana yau, kuma kullum haka abin yake babu canji, ko mai ya kawo hakan? Amsa ita ce OHO!

To TAMBAYA anan ita ce "Shin idan kai ne shugaban na Nijeriya ya zaka bullowa al'amarin, ya zaka tafiyar da mulkin kasar yadda zai yi daidai da bukatun talakawan kasar?"

Bukatun talakawan Nijeriya, ba abubuwa ne boyayyu ba, a fili suke wanda duk shugaban da yazo da kokon bararsa kafin talakawa su zabe shi, da su yake jan hankalinsu da tabbatar da cewa da zarar an zabe shi ya dare karagar mulkin kasar, ta kansu zai fara. Amma da zarar talakawan sun zabe shi sai ya kasa tabbatar da koda alkawari daya daga cikin wanda ya dauka, yayi fatali da bukatun talakawan har sai maganar tazarce ta taso.

Bukatun talakawan Nijeriya sune: Samarwa 'yan kasa aikin yi, samar da wutar lantarki, kyautata harkar noma, kawo gyara a bangaren ilmi, samar da hanyoyin sufuri masu inganci, samar da wadatattun magani a bangaren lafiya, samar da tsaro a kowane bangare, samar da wadataccen man fetur a farashi mai rahusa, samar da ruwan sha mai tsafta birni da karkara, saukake harkokin rayuwa ga talakawa, dawo da TALLAFIN MAN FETUR.

Bana tunanin akwai wasu abubuwa da talakawan Nijeriya ke bukata a wuraren jagororin kasar sama da wadannan, amma shekaru aru - aru, an kasa samun shugaba guda daya da zai bugi kirji ya samarwa talakawan Nijeriya koda daya daga cikin bukatun nasu.

Ya Allah ka kawo mana shugaban da zai dubi wadannan bukatu namu kuma ya yi mana maganinsu.

Domin bada amsa ziyarci shafin wannan Dandali a Facebook. facebook.com/dandalinbashirahmad

No comments:

Post a Comment