Wednesday, March 14, 2012

Jama'a Ga Jaridar RARIYA Matatar Gaskiya, Domin Samar Da Labaran Gaskiya


Aminci a gare ku! Ya ku al'ummar kasar Nijeriya, musamman Hausawa da kuma masu amfani da harshen. Cike da farin ciki da annashuwa nake gabatar muku da sabuwar jarida mai suna RARIYA wadda ake yi wa lakabi da MATATAR GASKIYA.

Wannan jarida sabuwar fitowa ce da aka samar domin al'umma, kuma zahiri jaridar ta zo a daidai lokacin da al'umma ke bukatarta, ba don komai ba sai don yadda al'amura a kullum suke kara cabewa gami da dagulewa musamman a harkokin yada labarai, sanin kowa ne mafi yawa daga cikin jaridun wannan zamani ba kawo sahihin labarai ne ya dame su ba, abin da suka fi mai da hankali shi ne wane labarai zasu kawowa makaranta ya samu karbuwa su samu riba mai yawa, ko da kuwa ba su da tabbacin sahihancin gaskiyar labarin.

RARIYA ta zo da salo ne na daban da ya sabawa irin na wadannan jaridu na zamani, wannan dalili ya sa ta samu lakabin MATATAR GASKIYA, kafin ta kawowa masu karatu labari sai ta bi diddiginsa sannan ta tato gaskiyarsa ta bayyanawa al'umma. Samuwar RARIYA zai zame wa masu karatu wata wukar gindi, sannan RARIYA ta yi alwashin kawo labaran da zasu inganta rayuwar al'umma, cikin hanya mafi dacewa da yanayin rayuwar zamani. Tabbas RARIYA ta samu ne bisa kishin kasarmu da al'ummarmu a matsayin wata jagora da zata nuna mana mafi ingancin rayuwa tagari abar alfahari.

Jaridar RARIYA na kunshe da bangari daban - daban masu Ilimintarwa, Fadakarwa, Wa'azantarwa, har ma da nishadantarwa. Kadan daga cikin wadannan bangarori sun hada da:

NIJERIYARMU A YAU - wannan bangare ne da yake dauke da muhimman labarai da suka shafi kasar nan baki daya.

MU KEWAYA JIHOHI - daga jin sunan bangaren ba bukatar dogon bayani, bangaren na lekawa jihohin kasar nan 36 da birnin tarayya Abuja, domin zakulowa masu karatu sahihan labarai masu inganci.

DUNIYA LABARI - A wannan bangaren kuma labarai ne kala - kala daga sassan duniya daban - daban, domin sanin wainar da ake toyawa.

BABBAN BAKO - A wannan bangare RARIYA na kurdawa cikin kasar nan ta lalubo wani babban bako masani, domin yin fashin baki akan wasu al'amura da zasu amfani masu karatu da sauran al'ummar kasa baki daya.

KULIYA MANTA SABO - Nan kuma bangare ne daya shafi harkokin shari'ah, domin kawowa masu karatu ingantattun labarai daga bangaren na Shari'ah.

SHAFA LABARI SHUNI - Shafin na kawo labarai na nishadantarwa da fadakarwa, wanda masu karatu ke aikowa da kansu, domin daukar wani darasi.

TASKAR FIM - Bangare ne a cikin jaridar dake kawowa makaranta irin wainar da ake toyawa a masana'antar fina-finan Hausa har ma da takwarorinsu na kudanci kasar nan (Nollywood) dama na sauran kasashen duniya irin su Amurka da India.

YABON GWANI - Bangaren na kawowa masu karatu tarihin wani kwazo, haziki kuma gwani a wani bangare na rayuwa, da irin gudunmawar da ya bawa al'umma.

SIYASA ROMON BAKA - Wannan bangaren kuma dandali ne na 'yan siyasa da magoya bayansu, shafin ya kunshi duk wani batutuwa da suka danganci siyasa.

LIKITA BOKAN TURAI - Nan kuma bangare ne da aka ware domin kiwon lafiya, da bada shawarwari ga makaranta ta yadda zasu kare kawunansu daga cututtuka.

TABA KA LASHE - Bangare ne da Amina Galadanci ke tsakurowa masu karatu dadaden labari daga litattafan Hausa kala - kala na da dana zamani.

WASANNI - Bangare ne domin matasan zamani, bangaren na kawo labarai ne game da wasanni kala - kala musamman a fannin kwallon kafa a ciki da wajen kasar nan.

To wannan kadan kenan daga cikin bangarorin da wannan jarida ta RARIYA ta kunsa, amma fa kamar yadda na fada ba duk bangarorin na bayyana ba, kadan daga ciki na bayyana, akwai bangarori da dama da ban bayyana ba irin su: Ra'ayin Rariya, Kowa Ya Debo Da Zafi, Allah Daya Gari Bambam, Jiya Ba Yau Ba, Tafarki Madaidaici, Tallata Hajarka, Adon Gari, 'Yar Kwalisa, Ma'aunin Hankali, Ciki Da Gaskiya, Daga Majalisar Tarayya, Hangen Nesa, Cinikayya, Asan Mutum, Girkinki Sirrinki, Sakonnin Masu Karatu da kuma GYARAN GANGAR AZBINAWA wanda babban edita da kansa wato Ashafa M. Barkiya yake gabatar da bangaren, inda yake yin tsokaci game da al'amuran da suka shafi siyasar kasar nan dama duniya baki daya.

Kai amma da yawan mantuwa nake, tunda na fara wannan rubutu nake son yin bayani akan wani bangare saya fi kowane daukar hankali na kuma na san ku ma shafin zai dauki hankalinku kuma ya burge ku, amma ban tuna ba sai da ruwan alkalamin da nake wannan rubutu yazo daf da karewa, hakan tasa idan na fara bayanin bangaren ba zan kai karshe ba ragowar ruwan rubutun zai karasa, kuma nasan ba za ku ji dadin hakan ba, saboda haka bari na bada satar amsar shafin, shafin yana kusa da shafin tsakiya, kuma shafin yana daya daga cikin shafukan da aka fi kawatawa, kai bari dai na dakata anan, domin ganewa idonka abin da shafin ke kunshe da shi yi saurin mallakar taka kwafin jaridar RARIYA, hakan zai baka damar fahimtar sauran abubuwa sama yadda zan yi muku bayani, har ma ku ma ku samu damar bawa wasu labari.

A karshe kamfanin RARIYA MEDIA SERVICES LTD. Shi ne yake daukar nauyin tsarawa da buga wannan jarida a kowane sati biyu a karkashin jagorancin Alhaji Dr. Aliyu Modibbo Ph.D, domin karin bayani za'a iya tuntubar hukumar gudanarwar kamfanin dake lamba 7, titin Thaba - Tseka, kusa da British Village, Wuse II, Abuja ko lambobin waya: 09-8701707, 09-8701708, 08034269830 email: rariyajarida@yahoo.com

No comments:

Post a Comment