Wednesday, February 29, 2012

Shin Za a Bukaci Kafafen Yada Labarai Anan Gaba?


Babu shakka shafukan sada zumunta kamar
Facebook, Twitter da You Tube sun sauya
yadda muke samun labarai.

Shafukan sada zumunta sun yi matukar
sauya yadda kafafen yada labarai na
duniya ke gudanar da ayyukansu.

A lokacin wani taro da BBC ta shirya bara
kan shafukan sada zumunta, manajan
editan jaridar Washington Post ya yi wani
jawabi mai daukar hankali inda ya ce "Mai
zai sa na dauki dan jaridar da bashi da
adreshin Facebook ko Twitter?"

Tuni aka fara tattaunawa kan ko nan gaba
za a bukaci kafafen yada labarai kamar
rediyo da talabijin.

Amsar ita ce kamata ya yi a koma a duba
tarihin yadda fasaha ke habbaka.

ALAKAR LAMARIN DA TARIHI

Idan muka duba tarihin gidajen buga
takardu a shekarun 1400, amfani da allunan
buga takardu a 1700, da tarho a 1800, da
kuma rediyo a 1800 zuwa farkon 1900, sun
ci karo da mulkin mallaka da kuma yakin
duniya.

Lokacin da aka kirkiro kowanne daga cikin
wadannan, mutane sun yi hasashen cewa
mafi sabunta daga cikin zai maye gurbin
sauran.

Lokacin da aka fara amfani da tauraran
dan'adam a 1980, an nuna damuwa kan
cewa zai kawo karshen jaridu.

Duk da cewa tauraron dan'adam ya sauya
yadda jaridu suke aiki, amma har yanzu
suna aiki duk da cewa suna fuskantar wani
yanayi mai tsauri.

AL'UMMA A DUNIYAR GIZO MAI CIBIYA A KAN NA'URA MAI KWAKWALWA

Idan aka yi la'akari da shafukan sada
zumunta kamar Twitter da Facebook, wani
sauyi ne aka samu ta fannin fasaha wanda
kamar rediyo da talabijin sun karo da wasu
abubuwan na zamani.

Mafi muhimmanci shi ne boren kasashen
Larabawa wanda ya kai ga kifar da
gwamnatocin kasashen Tunisia da Masar da
kuma Libya. Ya kuma yi tasiri a Wall Street a
Amurka da Turai da ma Afrika.

Wannan tasiri ya kuma sauya fagen siyasan
duniya inda jama'ar da ke amfani da
facebook suka suka ninka adadin yawan
jama'ar Amurka.

Wannan shi ne abinda zan kira kasashen da
suka yi nisa wurin amfani da kafofin
sadarwa na zamani.

Suna cike da matasa wadanda koda yaushe
suna tare da na'urorin kwamfiyuta da kuma
wayoyin na salula masu komai-da-ruwanka.

Sun riga sun saba da amfani da irin
wadannan kayayyakin fasaha na zamani;
don haka kalubalen da ke gaban kafafen
yada labarai na zamani shi ne su shiga a
dama da su a wannan fagen.

Nan da shekaru masu zuwa, wadannan
matasan ne za su zamo masu fada aji, haka
kuma masu shiryawa da kuma sauraran
labarai.

Ban amince da batun da ake na cewa
shafukan sada zumunta ko kuma internet,
za su maye gurbin talabijin da rediyo
kwata-kwata ba. Abinda zai faru shi ne za
su sauya yadda ake gudanar da harkokin
watsa labarai.

Tuni mun fara ganin gidajen talabijin a
Amurka kamar PJTV duk da kayan aikin da
suke da su irin na zamani, amma suna
watsa shirye-shiryen na su kawai a internet.

Nan gaba za a samu karin kafafen yada labarai da za su bi sahun PJTV, amma ba
ruwansu da kalubalen da ainahin gidajen
yada labarai za su fuskanta ba.

KARFAFA DANGANTA

Sai dai akwai abubuwa masu kayatarwa da
talabijin ke samarwa musamman a tsakanin
masu matsakaicin hali. Tana kyautata
dangantaka tsakanin iyalai, kuma wannan
shi ne abinda shafukan sada zumunta ba sa
samarwa cikin sauki.

An fi amfani da su ta wayoyin salula domin
debe kewa a gida ko makarantu ko kuma
wuraren aiki.

Sai dai a wuraren jama'a da dama a kasashe
masu tasowa, rediyo na gudanar da
makamancin wannan a yankunan karkara.

Za a dauki tsawon lokaci kafin shafukan
sada zumunta su maye gurbin tasirin rediyo
musamman a inda rediyon ta kasance
hanya daya tilo ta samun bayanai.

Wani abu da ya fito fili shi ne lokacin da
manyan kafafen yada labarai ke da iko a
kan labarai ta wuce, amma hanyar gudanar
da cikakken tsarin aikin jarida na nan har
gobe.

Kuma wannan shi ne muhimmin abu da ya
rage ga 'yan jarida, kuma wata rana masu
amfani da hanyoyin sadarwa na zamani za
su so su shiga wannan fagen.

Koma dai yaya ta kaya, a yanzu muna
karnin shafukan sada zumunta!

Muhammad Jameel Yusha'u
Malami ne a jami'ar Nothurmbria a
Burtaniya
.

Daga shafi BBCHausa.com

No comments:

Post a Comment