"Shin anya za'a yi wa Major Hamza Al - Mustapha adalci kuwa?" Wannan tambayar ita nayi ta maimaitawa a cikin zuciya tun jiya, bayan da naji dan uwan Al - Mustapha, mai suna Haruna Al - Mustapha ya bayyanawa gidan radio Wazobia FM dake Kano, halin da suke ciki tun bayan yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya da wata kotu da yanke masa a jihar Lagos. Amma abin mamaki har yanzu ban samu amsar tambayar da nake tayi wa kannawa ba, duk da daman ban yi tsammanin samun amsar tambayar cikin sauki ba, ko ma nace bazan taba samun amsar tambayar tawa ba, kawai dai zuciyata ce take son yaudara ta, da wahalar da ni akan tunanin nemo amsar tambayar da ba mai iya amsa ta sai 'yan tsurarun mutanen da zuciyata ke yin tambayar akansu.
Dalilin daya sa nayi wa kan nawa wannan tambaya shi ne halin da naji iyalen Al - Mustaphan sun bayyana suna ciki, ta bakin Haruna Al - Mustapha, kamar yadda na bayyana tun da farko. A jiya da misalin 8:30 na dare, ina sauraren wani shiri mai suna KASUWAR BUKATA wanda Muhammad Suleiman Gama ke gabatarwa a gidan radio Wazobia FM, a cikin shirin dan uwan na Al - Mustapha ya bayyana cewa suna cikin halin tsoro da damuwa tun bayan hukuncin kisa da kotu a jihar Lagos, karkashin Jagorancin mai shari'a Justice Dada ta yankewa dan uwan nasa.
Haruna Al - Mustapha ya bayyana cewa, tun bayan yanke hukuncin da aka yi suke ta kokarin daukaka kara a kotun gaba, amma har yanzu abin ya ci tura, ba don komai ba sai don rashin samun takarda a rubuce ta shaidar hukuncin da aka yankewa Al - Mustaphan, daga kotun da ta yanke hukuncin. Wanda kuma daukaka kara ba zai taba yiwuwa ba har sai da kwafin takardar shaidar yanke hukunci daga kotun baya.
Dan uwan na Al - Mustapha ya kara da cewa a kundin tsarin mulkin Nijeriya, sati daya ne mafi nisa ga duk wanda kotu ta yankewa wani hukunci kowane iri ne ta bashi a rubuce, amma sai gashi wata daya da yanke hukuncin, suna ta fafutukar samun rubutacciyar shaidar amma basu samu ba. Sannan yace a kundin tsarin mulkin na kasar nan, duk wanda aka yankewa hukunci bai daukaka kara ba tsawon wata biyu, to lailai ya gamsu da hukuncin da aka yanke masa kenan, hakan yana nufin idan bamu samu wannan rubutacciyar takarda ba har wata biyu ta cika za'a rataye mana dan uwa, ba tare da aikata laifin da ake zarginsa da shi ba.
Sanin kowane bayan yanke wannan hukunci daya daga cikin manya - manyan shaidun da suka bada shaidar cewa Al - Mustapha ne ya sa su, suka kashe Hajiya Kudirat Abiola, mai suna Abdul Katako ya fito ya bayyanawa duniya cewa shaidar karya aka tursashi yayi a gaban kotu, domin za'a bashi wasu makudan kudade da gidan zama duk inda yake son zama a fadin kasar nan.
A karshe Haruna Al - Mustapha ya bayyana cewa a tsakanin yau da gobe zasu dauki matakin shari'a, za su kai karar kotun da ta yanke wannan hukunci, a gaban hukumar shari'a ta kasa, saboda rashin basu takardar shaidar hukuncin da aka yankewa Major Hamza Al - Mustapha akan lokaci.
Ya Allah ga bawanka, Ka fitar da shi daga wannan hali da yake ciki, Ya Allah kar kabawa azzalumai damar yin zalunci akan wannan bawa naka.
No comments:
Post a Comment