Saturday, February 18, 2012

Gen. Muhammad Buhari Zai Dawo Kaduna Da Zama Daga Abuja Saboda Ba Zai Iya Biyan Miliyan 20 Kudin Haya

General Muhammad Buhari, tsohon janar din soja, tsohon gwamnan jihar Arewa maso gabas, tsohon ministan man fetur, tsohon shugaban tarayyar Nigeria, tsohon shugaban hukumar tattara rarar man fetur (PTF), dan takarar shugabancin kasa karo uku, zai tattara iyalansa daga birnin tarayya Abuja daga gidan da yake haya zuwa gidansa na jihar Kaduna.

Hakan ya biyo baya sakamakon iya biyan kudin hayar gidan da yake zaune a birnin tarayyar. General Buhari na zaune a gidan na tsawon shekara guda wanda wani abokinsa General Danjuma ya biya masa kudin hayar gidan Naira miliyan sha biyar N15,000,000 a shekarar da ta gabata saboda Buharin ya samu sakin zirga - zirgar da yake yawan yi tsakanin Kaduna da Abuja, a lokacin yakin neman zabensa.

'Yan kwanaki kadan ya rage lokacin hayar gidan ya cika, masu gidan suka aiko da takardar sabunta kudin hayar, inda suka sanar da cewa sakamakon tashin gwauron zabi da farashin kayayyaki ya samu kudin hayar gida ya karu da kaso daya bisa uku na kudin hayar gidan a bara, wato kudin hayar gidan yanzu ya kama naira miliyan ashirin N20,000,000.

General Buhari, bai yi kasa a gwiwa ba ya nuna ba zai iya biyan wannan kudi ba, kuma ba zai je wurin wani don neman taimakon a biya masa kudin hayar gidan ba, saboda haka ya tabbatar da komawa gidansa na Jihar Kaduna.

Gaskiya wannan ba karamin al'ajabi ba ne, a ce mutum kamar Buhari da ya rike irin wadannan mukamai amma bai mallaki unguwanni, kamfanunuwa, filaye a kowace jiha a kasar nan ba, sanin kowane ba wani mutum da ya taba rike mukami daya daga cikin mukaman da Buhari ya rike amma bai mallaki gidaje a birnin na tarayya ba, kai wasu ma har kasashen waje suke zuwa suna mallakar manya - manyan gidaje.

Hakan ya kara tabbatar min da dalilin da talakawan Nigeria suka dage sai ya sake dawowa sun zabe shi a matsayin shugaban kasa. Mafi yawa daga talakawan Nigeria sun baya Buhari kuri'arsu din din din, wato idan zai fito sun dubu ba tare da yayi nasara ba ko nace ba tare da an bashi ba, to za su zabe shi sau dubu, wasu daga cikin talakawan ma alkawari suka dauka idan ba Buhari ba to ko rijistar zabe ba zasu yi ba balle ma sau zabi wani. Kuma hakan ya kara tabbatar min da dalilin da yasa talakawan suke kiran Buhari da sunan Mai Gaskiya.

1 comment:

  1. Wannan gaskiya me,dan kuwa ko ni nan da ka ganni ina da irin wannan ra'ayin. Allah Ya taimaki mai gaskiya,Aameen

    ReplyDelete