Monday, July 20, 2015

MASU GUDU SU GUDU: Gwamnatin Buhari Ta Shirya Bincikar Jonathan Da Ministocinsa

Yayin da sabuwar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke kara matsa kaimi wajen kato dukiyar jama'ar kasar nan da tsofaffin shugabannin baya suka yi sama da fadi da ita, a yanzu haka gwamnatin ta bayyana shirinta na bincikar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da Tawagar ministocinsa domin tattaro kudaden da suka sace a lokacin da suke jagorantar kasar nan.

Cikin wani rubutu da yayi a shafin Jaridar Washington Post ta Amurka a jiya, Shugaba Buhari wanda yake kan ziyara a kasar ta Amurka a yanzu, ya ce yana neman goyon bayan Shugaba Barack Obama da gwamnatinsa wajen bada gudunmawa a yunkurin Nijeriya na kwato dukiyar da tsofaffin shugabannin suka sace.

Tuni Obama ya bayyana cikakken goyon bayansa kan wannan roko na Buhari, inda ya umarci hukumar tsaro na FBI ta binciki duk bankunan da suke Amurka idan aka samu kwandala da aka sato daga Nijeriya aka ajiye a bankunan a maida su.

Haka jam'iyyar adawa ta PDP ma ta nuna goyon bayanta kan sabon salon dawo da satattun kudaden da Buharin zai fara yin amfani da shi.

...Lalle wannan shi MASU GUDU SU GUDU, ko kuna goyon bayan wannan sabon salo da gwamnatin Buhari ta fito da shi?

No comments:

Post a Comment